Abin da ya kamata a sani game da sabuwar dokar haraji

Za a riƙa karɓar harajin kashi 5 cikin 100 kan kuɗaɗen shiga na caca da cinikin caca ko kasuwancinta.

Abin da ya kamata a sani game da sabuwar dokar haraji

A kwanakin baya ne Kwamitin Shugaban ƙasa Kan Sake Fasalin Kasafin Kuɗi da Haraji, ƙarƙashin jagorancin Mista Taiwo Oyedele ya gabatar da ƙudirin doka ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya, wanda daga bisani aka amince tare da miƙa ta ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin amincewa.

Kwamitin wanda ke da alhakin daidaita yawan haraji a dukkan matakai na gwamnati, yana da alhakin haɗe ayyukan tattara kuɗaɗen shiga tare da sabunta tsarin haraji da sauƙaƙa tsarisa, gami da amfani da fasaha don tara kuɗaɗen shiga.

An ɗora wa kwamitin ne alhakin sauya hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga don samun ci-gaba mai ɗorewa, da nufin cim ma aƙalla kashi 18 cikin 100 na harajin a cikin shekaru uku masu zuwa, wato nan da 2026.

Daga baya, a farkon watan Oktoba 2024, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa Ƙudirin Sabuwar Dokar haraji ta ƙasa ta 2024 ga Majalisar Dokoki ta ƙasa.

Ana sa ran ƙudirin zai sake fasalin tsarin kasafin kuɗin Nijeriya tare da kafa cikakken tsarin doka da zai tafiyar da harajin da kuɗaɗen shiga da hada-hadar kasuwanci da kayan aiki.

Ƙudirin yana da taken, Dokar Soke Wasu Ayyuka Kan Haraji da Daidaita Tsare-tsaren Dokoki da Shari’a da Suka Shafi Haraji da kuma Kafa Dokar Harajin Nijeriya Don Samar da Kuɗaɗen Shiga, Mu’amala da Kayayyakin Aiki da kuma Wasu Batutuwa Masu Alaƙa.

Har ila yau, ƙudurin ya jawo mayar da martani daga ɓangarori daban-daban da suka haɗa da gwamnoni da sarakunan gargajiya na jihohin Arewa, waɗanda a ranar Litinin suka yanke shawarar ƙin amincewa da shi.

A cewar gwamnonin Arewa, abin da ke cikin ƙudirin dokar harajin bai dace da muradun Arewacin Nijeriya da sauran ƙananan hukumomin ba. Haka kuma, a ranar Alhamis, Majalisar Tattalin Arzikin ƙasa ta ba da shawarar janye ƙudirin.

Muhimman bayanai na dokar

Ƙara harajin da ake biya kan kayayyaki da kasuwanci wato VAT Sashi na 146 na ƙudirin ya nemi a ƙara harajin na (ƁAT) daga kashi 7.5 zuwa kashi 10 nan da 2025, tare da ƙara shi zuwa kashi 12.5 daga 2026 zuwa 2029 da kuma sake ƙara kashi 15 daga 2030 zuwa gaba.

A wannan yanayi, darajar abin da za a karɓi haraji a kansa ya haɗa da jimillar la’akarin da aka y da kuma harajin ƁAT na kasuwancin da ya shafi kuɗi ko kuma darajar kasuwancin da ba na kuɗi ba a kasuwa. Sai dai, a yanayin da ya kasance cikin yana cikin babban tsari, za a biya harajin wani ɓangare ne kawai.

Haka kuma, a kan ma’amaloli tsakanin ɓangarorin da ke da alaƙa ko waɗanda suka haɗa da mu’amalar da ba ta kuɗi ba, ƙimar harajin za a ƙayyade ta daidai da ƙimar kasuwa.

Hakazalika, ƁAT da mai karɓar haraji ya karɓa, za a kira shi VAT kuma cikinsa ne za a fitar. Hukumomin gwamnati (na tarayya, jiha da ƙananan hukumomi), ma’aikatunsu, hukumominsu da sauran wakilan da aka zaɓa ana buƙatar su karɓa ko riƙe harajin na ƁAT su miƙa wa hukumar haraji kamar yadda aka tsara.

Kayayyakin da ba za a karɓi ƁAT ba

Har ila yau, a cikin lissafin akwai wasu kayayyaki da za a keɓance su daga tsarin biyan harajin ƁAT da aka tsara.

Waɗannan kayayyaki sun haɗa da: man fetur da iskar gas da za a fitar zuwa ƙasashen waje, ɗanyen mai. Sauran abubuwan da aka keɓe su ne: kayan da aka saya don ayyukan jin-ƙai (inda mai ba da gudunmawa zai biya ƁAT a gaba), kayan jarirai, kayayyakin tsaftar gida, kayan aikin soja da makamai da kuma harsasai da aka kai wa hukumomin tsaro.

Har ila yau, dokar ta cire harajin a kan wutar lantarki da kamfanonin samar da wutar lantarki (GENCOs) ke samarwa zuwa ga babbar tashar wutar lantarki ta ƙasa ko kuma ga Kamfanin Kasuwancin Wutar Lantarki na Nijeriya (NBET) da wutar lantarkin da Kamfanin Samar da Wutar Lantarki ya samr zuwa ga na rabbata wutar lantarki.

Kamfanoni za su biya 27.5% a kan harajin ribar da suka samu

Sashi na 56 na ƙudirin ya zayyana adadin harajin da za a ɗora a kan jimillar ribar da kamfanoni ke samu, tare daina sanya wa ƙananan kamfanoni haraji. Duk sauran kamfanoni za su biya harajin kashi 27.5 cikin 100 a 2025, wanda zai ragu zuwa kashi 25 cikin 100 daga 2026. Idan ingancin harajin kamfani bai kai kashi 15 cikin 100 a kowace shekara ba, dole ne ya sake yin lissafin kuma ya biya ƙarin haraji don kai shi zuwa kashi 15 cikin ɗari.

Wannan tanadin ya shafi kamfanoni a cikin ƙungiyoyin kasuwanci na ƙasa da ƙasa da duk wani kamfani da ke da jimlar kuɗin da ya haura Naira biliyan 20 a cikin shekarar da ta gabata.

Kashi 4% na harajin raya ƙasa da aka ɗora wa kamfanoni

Sashi na 59 ya tanadi harajin ci-gaba a kan ribar da ake iya tantancewa ta kamfanoni, ban da ƙananan kamfanoni masu zaman kansu.

Harajin zai zama kashi huɗu cikin 100 A 2025 da 2026, kashi uku daga 2027 zuwa 2029, sannan kashi biyu daga 2030 zuwa gaba. Daga harajin ne za a ba wa Asusun Lamuni na da zai bai wa ɗalibai rance.

Za a raba kuɗaɗen shiga ga Asusun Tallafawa Manyan Makarantu, wanda zai samu kashi 50 cikin 100 a 2025 da 2026, kashi 66 cikin 100 daga 2027 zuwa 2029, sai kuma kashi sifili daga 2030 zuwa gaba.

Asusun Lamuni na Ɗalibi zai karɓi kashi 25 cikin ɗari a cikin 2025 da 2026, kashi 33 cikin ɗari daga 2027 zuwa 2029 da kashi 100 daga 2030 gaba.

Haka kuma, Asusun Tallafa wa Fasahar Sadarwa na ƙasa zai samu kashi 20 cikin 100 a 2025 da 2026, inda daga nan zai daina samu.

Hukumar Samar da Kayyayakin More Rayuwa da Ƙere-ƙere a ƙasa za ta samu kashi 5 cikin 100 a 2025 da 2026, wanda daga nan zai daina samu.

Kashi 5% na harajin a kan caca

Sashi na 62 na jadawali na 10 na dokar sun ba da shawarar karɓar harajin kashi 5 cikin 100 kan kuɗaɗen shiga na caca da cinikin caca ko kasuwancinta.

Sashen ya bayyana wasanni a zaman caca, kamar wasannin irin su Wagering, poker na bidiyo, roulette, craps, bingo, ramin ko injin wasan caca, zane ko wasu wasanni da ake gudanarwa.

Har ila yau, ya bayyana ‘Lottery’ ko ‘Lotteries’ a matsayin duk wani wasa, tsari, kala, iri ko gasar talla ko amfani da na’ura don rarraba kyaututtuka ta hanyar canki-canki ko jefa ƙuri’a ko dama ko kuma sakamakon wata ƙwarewa da dama ko sakamakon wasanni na gaske ko na kama-da-wane ko kowane wasa na gasa ko amfani da na’ura.

Kashi 5% harajin sadarwa

Hakazalika, ƙudurin dokar ya gabatar da ƙarin harajin kashi biyar cikin 100 na ayyukan sadarwa da suka haɗa da biyan kuɗaɗen da aka biya kafin lokaci da kuma wanda Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta tsara.

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur 

Na kusa zama ɗan ƙwaya a baya — Obasanjo