Abin da ya kamata El-Rufa’i ya yi game da malaman Firamare

Salam. Koran malaman Firamare a Jihar Kaduna kimanin guda dubu ashirin da biyu da kuma maye gurbinsu da guda dubu ashirun da biyar ba zai wadatar da illimi ba a jihar Kaduna da ake yi wa take da cibiyar illimi. A hakikanin gaskiya akwai matsaloli da yawa a cikin harkar illimi na Afirka, musamman Najeriya […]

Abin da ya kamata El-Rufa’i ya yi game da malaman Firamare

Salam. Koran malaman Firamare a Jihar Kaduna kimanin guda dubu ashirin da biyu da kuma maye gurbinsu da guda dubu ashirun da biyar ba zai wadatar da illimi ba a jihar Kaduna da ake yi wa take da cibiyar illimi. A hakikanin gaskiya akwai matsaloli da yawa a cikin harkar illimi na Afirka, musamman Najeriya saboda idan muka duba a gwamnatocin baya, basa bai wa illimi mahimmanci a aikace sai dai a baki kawai. 

Wannan ya jawo ci baya wajen tafiyar da harkar ilimi a kasar. Idan muka duba ko muka dawo baya, zamu ga cewa ba an bar mu a baya ba wajen lalacewar illimin Firamare. Na farko akwai bukatar malaman Firamare a rika biyansu albashi mai kyau. 

Saboda albashi da ake ba su ya yi karanci, wanda ya sa malaman ba sa mayar da hankali wajen koyarwa saboda kullum suna cikin neman wani aikin. Na biyu dole ne gwamnati ta samar da kayan da za ayi amfani da su wajen koyar da dalibai. Na uku shi ne dole ne gwamnati ta gyara makarantu. Babu yadda za ace ajin da ya kamata ya dauki dalibai 30 an zuba dalibai 60, sannan ya zama daliban suna fahimtar abin da ya kamata. Sannan saboda rashin guraren karatun za ka ga yara har karatun rana suke yi wanda kamata ya yi su rika karatun da safe kafin rana ta yi zafi. 

Ko an dauki sabbin mallamai, za a ci gaba da samun wadannan matsalolin idan ba a gyara ba. Na hudu shi ne akwai bukatar samar da jami’ain lura da yadda mallamai ke zuwa aiki da shiga aji. A karshe ina ba da shawaran da cewa mallamai na makaranta tun daga Firamare zuwa babban Sakandare akwai bukatan a rika biyansu albashi mai kyau. Saboda za ka ga cewa wadanna kananan mallaman sun fi wahala wajen koyar da yara. 

A karkashin wannan matakin na illimi ne idan ya gyaru, yara za su yi amfani a gaba. Idan ba a maida hankali gurin wannan ginshikin ba, tabbas yara za su samu matsala a karatunsa na gaba. Muna rokon Allah Ya ba mu ikon jajircewa wajen kawo gyara a harkar ilimin kasarmu, musamman ma jiharmu ta Kaduna mai tarin albarka. 

Daga Aliyu Khalid. 08038597907