‘Abin da ya kamata gwamnati ta yi kan noman alkama’
Alhaji Musa Shehu Sheka, Mukaddashin Shugaban Kungiyar Manoman Alkama ta Kasa reshen Jihar Kano, a zantawarsa da wakilinmu ya ba da wasu shawarwarin da suka kamata gwamnati ta bi don farfado da noman alkama a Najeriya: Bari mu fara da jin ra’ayinka kan harkar noman alkama a Najeriya, shin kana jin kasar nan tana samun […]
Alhaji Musa Shehu Sheka, Mukaddashin Shugaban Kungiyar Manoman Alkama ta Kasa reshen Jihar Kano, a zantawarsa da wakilinmu ya ba da wasu shawarwarin da suka kamata gwamnati ta bi don farfado da noman alkama a Najeriya:
Bari mu fara da jin ra’ayinka kan harkar noman alkama a Najeriya, shin kana jin kasar nan tana samun riba kan harkar noman alkama kuwa?
Ina son ka san cewa ita alkama iri ne da kasashen duniya masu karfin mulki suke sarrafawa fiye da shekara 20 da suka gabata, kuma fiye da kashi 70 cikin 100 na alkamarsu Najeriya ake shigowa da ita ake cinye ta. Saboda haka tsawon wadannan shekaru Najeriya tana kashe kudade masu yawa wajen bada tallafi kan alkama. A ’yan kwanakin nan ne wannan gwamnati ta nuna sha’awarta wajen bada karfi kan noman alkama, saboda haka a ganina yanzu ne gwamnati za ta amfana da noman alkama wajen jajircewa ta ga an farfado da nomanta ta hanyar hada karfi da karfe da Babban Bankin Najeriya (CBN), ta bai wa manoman bashi wato Anchor Borrower Programme.
Mece ce matsalar da ta shafi noman alkama a Jihar Kano?
Akwai matsaloli da yawa da suka shafi harkar noman alkama a Jihar Kano; kadan daga cikinsu su ne (1) Rashin iri mai inganci a hannun manoma ya shafi manoma sosai (2) Rashin samun kayan noma na zamani da kuma (3) Rashin samun horo kan harkar noma na zamani da kayayyakin aiki.
Yaya za ka bayyana tallafin da gwamnati ke bayarwa wajen noman alkama?
Gaskiya yadda Gwamnatin Jihar Kano ke bai wa manoman tallafin abin a yaba ne. Ta hannun kungiya, mun samu tallafi da kula daga gwamnati a bangarori daban-daban. Misali gwamnatin ta ba mu bashi marar ruwa na Naira miliyan 100 a lokacin shirin noman na shekarar 2015/2016 na shirin sayen irin alkama a raba wa manoma a wannan shekarar. Sa’annan kuma ta sake ba mu wani rancen Naira miliyan 100 ya zama miliyan 200.
Wannan girbi da muka yi a tsakanin wadannan shekaru gwamnati ce ta saya ta bai wa kungiyar manoma don sama musu sauki a fadin jihar. Sa’annan kuma gwamnatin jihar ta tsaya mana a matsayin garanto don kungiyar ta samu rancen Naira miliyan 18 na sayan injin zazzabar alkamar ga manoma .
Bugu da kari an ba mu wani waje kyauta da muke yin zazzabar duk yana daga cikin irin tallafin da gwamnatin take bai wa manoman alkama a jihar don bunkasa noman alkama a daukacin Jihar Kano.
Adadin manoma nawa ne kake jin ake da su a Jihar Kano?
Akalla za su kai dubu 150 da suke noma alkama a Jihar Kano.
Yaya adadin alkamar da ake nomawa yanzu a Kano?
Yanzu haka muna da filin noma kadada dubu 250 zuwa dubu 300 a Kano; inda a kadada dubu 250 din nan za mu iya noma tan uku zuwa tan hudu a kowace kadada.
Ka gamsu da yadda alkama take yanzu a kasuwa?
Mun sanya hannun kan takardar yarjejeniya (MOU) da masu nika ta wajen ganin ta yi daraja, inda yanzu haka daga mako biyun da suka gabata, buhun akan sayar da shi tsakanin Naira 18,500 zuwa Naira dubu 20 ya danganta da wacce iri ce.
Wane bangare ne kake jin ya kamata gwamnati ta shigo a dukkan matakai don taimaka wa noman alkama?
Muna bukatar tallafin gwamnati a bangarori da dama don bai wa manazarta kwarin gwiwar samar da cibiya kan bincike ko nazarin irin alkama. Gwamnati ta bayar da dama ana shigo da alkamar daga kasashen da muke makwabtaka da su, sa’annan ta dauki mataki na daidaita farashi a tsakanin manoma da ’yan kasuwa da kuma karfafa tsakanin Babban Bankin Najeriya (CBN) da shirin bada rance na Anchor Borrowers. Mun tabbata idan aka magance wadannan matsaloli za a cimma buri da habaka noman alkama ba a Kano kadai ba a kasa baki daya.