Abin da ya kamata ka yi a matsayinka na Sarkin Zazzau – El-Rufai
El-Rufai ya ce a yanzu dai takarar neman gadon sarauta ta kare kuma an nada sabon Sarkin Zazzau.
Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, ya kira yi sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, da ya mayar da hankali wajen hada kan al’ummar masauratarsa tare da tabbatar da yi wa dukkan bangarori adalci.
Kiran Gwamnan na zuwa ne a yayin da Sabon Sarkin ya jagoranci wata tawaga da ta kai masa ziyarar mika godiya har fadar Gwamnatinsa da ke birnin Kaduna a ranar Laraba.
- Sarkin Zazzau ya kai wa El-Rufai ziyara
- Iyan Zazzau ya nemi kotu ta soke nadin Bamalli
- Tirka-tirkar da aka yi kan nada Sarkin Zazzau
El-Rufa’i ya ce tun da a yanzu takarar neman gadon sarauta ta kare kuma har an yi nadin sabon Sarki, akwai bukatar a yi wa dukkan bangarori adalci walau wadanda suka goyi baya da sabanin haka.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, yana alfahari da masarautar Zazzau kasancewarta tushen da ya fito wanda hakan zai sai gwamnatinsa ta kara kaimi wajen goyon bayanta.
Ya kuma hadin kai shi ne sirrin da zai tabbatar da kai masarautar zuwa ga mataki na gaci da kuma samar ci gaba mai dorewa.
Gwamnan ya kara da cewa, babu shakka burin kowane yarima shi ne wata ranar ya zama Sarki kuma a yanzu Mai Kaddara wa da sanadin Gwamnatin Jihar ya zabi Ahmed Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.