Abin da ya kamata ku sani a kan ciwon hanta
Ranar Talatar 28 ga watan Yuli ce ranar da hukumomin lafiya na duniya suka ware domin yaki da ciwon hanta. Akan ware irin wannan rana ce a duk shekara domin wayar da kan jama’a domin kare kansu daga kamuwa da cutar a fadin duniya. Ciwon hanta mai saurin yaduwa, wasu kwayoyin cuta na virus ne ke […]
Ranar Talatar 28 ga watan Yuli ce ranar da hukumomin lafiya na duniya suka ware domin yaki da ciwon hanta.
Akan ware irin wannan rana ce a duk shekara domin wayar da kan jama’a domin kare kansu daga kamuwa da cutar a fadin duniya.
Ciwon hanta mai saurin yaduwa, wasu kwayoyin cuta na virus ne ke jawo shi, idan suka shiga cikin hanta ta hanyar jini.
Nau’ukan cutar hanta
Akwai nau’insu har kusan kala shida. Akwai A akwai B, akwai C da D da E da kuma F.
Amma an fi ganin nau’uka uku na farko wato A, B, da C.
A cikin wadannan ukun ma an fi ganin nau’in ajin B, wanda kuma shi ne ya fi yi wa hanta illa.
Ya kamata a san ban da wadannan rukunin kwayoyin cututtuka akwai sauran kwayoyi da ba na virus ba, da sauran abubuwa ma da suke kashe hanta.
Abubuwan sun hada da barasa da burkutu da shan miyagun kwayoyi da shan wasu guba kamar gubar dalma da sauransu.
Nau’ukan ciwon hanta da za mu yi magana a kai su ne wadanda kwayoyin cutar rukunin B ke kawowa, domin ita ta fi saurin yaduwa a al’umarmu, ita kuma ta fi hadari.
Hanyoyin daukarta daya ne da na Aids
Hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa hanyoyin da ake daukar wadannan kwayoyin cuta masu nakasa hanta kusan daya ne da ake daukar cutar Aids
Hanyoyin su ne jima’i da karin jini da amfani da kayan kaifi da allurai kamar yadda wasu ’yan kwaya suke yi.
A yanzu haka an fi samun mace-mace daga cututtukan hanta na hepatitis rukunin B fiye da mace-macen cutar Aids.
Dalili shi ne rashin samun magungunan ciwon hantar kamar yadda aka samar da na kanjamau.
Haka nan kuma saboda fadakarwa da ake ta yi a kan ciwon na Aids din ana mantawa da na hanta mai yaduwa.
Masu fama da cutar hanta
Yanzu mutane fiye da miliyan 1.5 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hantar.
Amma masu Aids wajen miliyan 1 ne ke mutuwa a duk shekara.
Haka kuma kusan kowa ya san cutar Aids amma da yawan mutane ba su san ciwon kumburin hanta mai yaduwa ba.
Shi ya sa da yawa mutane idan za su yi aure sai dai a yi gwajin Aids kawai, amma ba a hadawa da na ciwon hanta.
Yawanci a wurin gwajin ba da jini kawai akan gano mutum yana dauke da cutar, tunda sai ta yi shekara da shekaru mutum bai ma san yana dauke da kwayar cutar ba, domin da fari ba alamu take nunawa ba.
Hanyoyin daukar cutar:
Hanyoyin da ake daukar kwayoyin su ne yayin jima’i daga mai dauke da kwayar zuwa wanda bai dauke da ita.
Sai kuma ta hanyar karin jini idan ba a yi gwajin tantance kwayar cutar ba.
Ana kuma daukar cutar ta hanyar amfani da kayan kaifin da ba su da tsafta, kamar askar wanzamin da ba a gasa ba, ko almakashin mai yankan farce da ba ya sa wuta.
Daga cikin hanyoyin akwai amfani da rezar da mai ciwon ya yi amfani da ita, kamar lokacin yankan cibi idan an zo haihuwa.
Ko kuma amfani da allurar da aka yi wa wani, maimakon a yi amfani da sabuwa.
Wata hanyar kuma ta daukar ciwon a jarirai ita ce ta wurin uwa mai dauke da kwayar cutar, yayin haihuwa ko yayin shayarwa.
Alamomin cutar hanta:
Da yake kwayoyin cutar shiga cikin hanta suke su yi barcinsu, da yawa masu dauke da ita ba sa jin wasu alamu tsawon shekaru sai ranar da suka farka suka fara cin hantar sa’annan alamu za su bayyana.
Wannan na faruwa ne kawai a kashi daya cikin hudu na wadanda ke dauke da kwayar.
Sauran kashi ukun ba za su taba nuna wata alama ba duk tsawon rayuwarsu, shi ya sa aka fi cewa masu dauke da kwayar su kwantar da hankalinsu domin zai wahala su nuna alamunta.
Amma a wannan tsakanin ne masu ciwon ke yada ta musamman ga abokan zama na aure da kuma ’ya’yansu.
Alamun ciwon, idan har sun bayyana, su ne yawan zazzabi, yawan ciwon ciki bangaren dama, yawan tashin zuciya da rashin son abinci, yawan samun shawara, wato kadawar ido zuwa ruwan dorawa da rama da sauran alamu da mutum zai ji dai cewa ba lafiya ba.
Daukar mataki kan cutar hanta:
A daidai wannan lokaci ne dole a dauki matakin rage kwayoyin cutar domin kada su nakasar da hantar gaba daya.
Babban abin da kwayoyin cutar suke kawowa shi ne motsewar hanta ko ma ciwon daji na hanta.
Magunguna da alluran da ake amfani da su a ci karfin kwayoyin cutar kafin su kai ga illa suna da matukar tsada sosai, shi ya sa mukan ce riga-kafi ya fi magani.
Hanyoyin Kariya:
- Kamewa har sai an yi aure, masu auren ma su rike matansu kawai.
- Tabbatar da an yi gwajin cutar ga wadanda suke shirin aure.
Su je tare kuma a nuna musu sakamakon tare kafin a daura auren.
- Tabbatarwa cewa jinin da za a kara wa mutum an gwada shi a asibiti an tabbatar ba ya dauke da kwayoyin cutar.
- A wurin awon mata masu juna biyu ana auna wannan ciwon.
Idan an samu mace mai kwayar cutar ana daukar duk matakan da suka kamata wajen kare abin da take dauke da shi don kada ya samu.
Don haka a wurin awo a ba wa ma’aikatan lafiya hadin kai.
- A yanzu akwai alluran riga-kafin kamuwa daga wadannan kwayoyin cuta na ciwon hanta kyauta wadanda aka sa a jadawalin alluran riga-kafi don yi wa yara da zarar an haife su.
Sa’annan a maimaita watanni na biyu da na uku, akasin kwayar HIV wadda har yanzu ba a gano allurar riga-kafinta ba.
- Ba yara kawai ba, har manya wadanda ke cikin hadarin kamuwa za a iya yi wa allurar riga-kafin.
Wadannan sun hada da ma’aikatan lafiya, musamman masu aiki a dakin gwajin jini da tiyata, mata masu zaman kansu, da mutanen da ke aiki cikin damara.
A ma’aurata wadanda aka samu daya ke da kwayar cutar amma daya ba shi da ita, shi wanda ba ya dauke da kwayar cutar sai ya samu a yi masa allurar riga-kafin.
Ana samun wadannan allurai a asibitoci da cibiyoyin riga-kafi.
- A tabbata an tafasa kayan kaifi kamar na wanzamai ko na mai yankan farce ko na aski.
A kona su da wutar lighter ko a wanke su da sinadarin bleach kafin a yi wa mutum amfani da su.
Sai dai idan abin kaifin sabo ne daga ledarsa aka bare a gaban mutum to ba sai an gasa da wuta ba.
Haka ma sirinji da reza, a rika tabbatarwa sababbi fil aka bare kafin amfani da su.