Abin da ya kamata ku sani kan wasan Manchester United da Tottenham
Za a buga wasan ne a filin Old Trafford da ke Manchester da misalin karfe 8:15 na dare.
A yau Laraba za a buga wasu daga cikin wasannin mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila.
Sai dai daga ciki, wasa mafi zafi da kuma daukar hankali shi ne wanda za a fafata a tsakanin Manchester United da kuma Kungiyar Tottenham.
- Klopp ya amince da ba shi jan kati
- DAGA LARABA: Yadda aka zalunce mu a bainar jama’a, amma kowa ya kau da kai
Za a buga wasan ne a filin Old Trafford da ke Manchester da misalin karfe 8:15 na dare, agogon Najeriya.
Ga jerin sunayen ’yan wasa zabin farko da ake hasashen kowacce kungiyar za ta fara da su:
Manchester United
De Gea, Dalot, Varane, Martinez, Shaw; Casemiro, McTominay, Antony, Fernandes, Sancho, Rashford.
Tottenham
Hugo Lloris, Cristian Romero, Eric Dier, Clement Lenglet, Matt Doherty, Pierre Emile-Hojbjerg, Yves Bissouma , Rodrigo Bentancur, Ryan Sessegnon, Harry Kane, Son Heung-min.