Abin da ya kamata Tinubu ya yi kafin cire tallafin man fetur —Atiku
Tinubu ya yi azarbabin janye tallafin man fetur din baki daya.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya soki matakin shugaba Bola Tinubu na cire tallafin mai ba tare da samar da hanyoyin saukaka wa al’umma ba.
Wazirin Adamawa ya ce Shugaba Tinubu ya dauki matakin ba tare da yin zuzzurfan nazari ba musamman wajen rashin samar wa al’umma ababen rage radadin janye tallafin man fetur din baki daya.
- Bala Mohammed ya zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP
- Hatsarin jirgin kasa ya kashe kusan mutum 300 a Indiya
Atiku Abubakar wanda shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasar da ya gudana, ya yi wannan suka ne a wani taron PDP da aka shirya wa zababbun jami’ai a Jihar Bauchi.
A cewar Atiku, “tsakanin 1999 da 2007, gwamnatin PDP ta bullo da batun cire tallafin mai kuma ni na jagoranci kwamitin.
“Mun cimma kudirin ta hanyoyi biyu amma sai bayan samar da kayayyakin rage radadin matakin ga wadanda lamarin ya shafa.
“Mun dandana irin wannan a matsayin jam’iyya da ke mulki. Da abin da za mu yi ke nan ba wai kawai sanar da janye tallafi ba, ba tare da tattaunawa da bangarorin da abin ya shafa ba,” in ji Atiku Abubakar.
Bola Tinubu dai ya bayyana matakin janye tallafin man fetur din ne a lokacin da yake jawabinsa na farko ga al’ummar Najeriya bayan rantsar da shi a matsayin Shugaban Kasa.
Kuma tun lokacin ne al’ummar kasar suka shiga rudani kasancewar farashin mai ya tashi ga kuma hauhawar farashin kayayyaki.