Abin da ya kamata ’yan mata masu son shiga fim su yi —Amaryar TikTok

Jarumar ta bayyana kalubalen da ’yan mata masu shirin shiga harkar fim za su iya fuskanta.

Abin da ya kamata ’yan mata masu son shiga fim su yi —Amaryar TikTok

Hafsat Isma’il Tuge wadda aka fi sani da ‘Amaryar TikTok’ta fede biri har wutsiya kan halin da ta shiga lokacin da tsohon mijinta ya ce da aurensa ta fara harkar fim.

A tattauanwarta da Aminiya, jarumar ta yi tankade da rairaya kan abin da ya kamata ’yan mata masu shirin shiga  masana’antar Kannywood su yi.