Abin da ya kawo cikas a sulhun ECOWAS da sojin Nijar — Yusuf Tuggar

Tuggar ya ce dole ne idan mutane suka yi ba daidai ba a tsawatar musu.

Abin da ya kawo cikas a sulhun ECOWAS da sojin Nijar — Yusuf Tuggar

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce sun yi tayin tattaunawa domin kawo ƙarshen tankiyar da ke tsakanin Ƙungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da sojojin da suka kifar da Shugaban Nijar Mohammed Bazoum, amma hakan bai yiwu ba, don kuwa shugabannin sojojin sun ƙi amincewa da yunƙurin.

Ambasada Tuggar ya faɗi hakan ne a wata hirarsa da BBC, yana mai cewa duk wata magana da ta shafi a saki Shugaba Bazoum, sojin ba su amince da ita ba.

“Sun ce kar ma a yi wannan maganar, kar ma a sa shi cikin sharuɗɗan yin sulhu,” in ji Yusuf Tuggar.

Ya bayyana cewa babu ta yadda za a iya samun sulhu a wannan yanayi.

“Za su ci gaba da rike shi kenan ya yi zaman dindindin a kulle?”

Ministan ya ce sojojin da suka yi juyin mulki ne suka janyo wa Nijar takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙaba mata, da kuma shiga halin da take ciki.

Ya ce abin da suke buƙata shi ne a saki Shugaba Bazoum.

“Muna son sojojin su saki Bazoum ya fita, a kai shi wata ƙasa daban. Ba maganar dawo da shi kan mulki ake yi ba,” in ji ministan.

Ya ƙara da cewa, duk wani yunƙuri da suka yi, sojojin sun ƙi ba da haɗin-kai ta kowanne yanayi, inda suka ce ba sa son a yi maganar ma kwata-kwata.

“Ta yaya za a yi sulhu a haka, mene ne sojojin za su yi saboda in ana son yin sulhu tsakanin mutane, gefe ɗaya zai ce ya haƙura da abu kaza, ɗaya gefen ma ya ce haka.

“To su kwata-kwata cewa suka yi, sai dai a yi musu abin da suke so,” in ji Tuggar.

Ya ce ECOWAS ba ta da matsala da ƴan Nijar kuma ba ta jin daɗin halin da suke ciki.

Ya ƙara da cewa matsalarsu ita ce sojojin da suka kama Shugaba Bazoum suka riƙe, duk da yake suna ganin akwai hanya mai sauƙi ta warware rikicin.

Ministan harkokin wajen Najeriyar ya ce dole ne idan mutane suka yi ba daidai ba a tsawatar musu.

A cewarsa, sojojin ma ba yadda suka iya da junansu don kuwa, kowa na ƙoƙarin samun ƙarfin iko a Nijar, inda a gefe guda suka bar ƴan ta’adda na can suna cin karensu babu babbaka.

Watanni huɗu bayan kakaba wa jamhuriyar Nijar takunkumi da ƙungiyar ECOWAS ta yi, sakamakon juyin mulkin sojoji, har yanzu ƴan ƙasar na ci gaba da ɗanɗana kuɗa da rayuwar ƙunci.

Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi, saboda rufe iyakar ƙasar da Najeriya ta yi, da kuma yanke hulɗar kasuwanci da ƙasashen ECOWAS suka yi da Nijar.

2025: ’Yan Najeriya suke bibiyar abin da shugabanni ke yi – Atiku

Abba ya sanya hannu kan kasafin kuɗin N719bn na 2025

Mutum 5 da aka fi ambato a 2024 a Afirka

Gwamnatin Borno ta horar da mata 162 sana’o’in dogaro da kai