Abin da ya kawo faduwar farashin kayan amfanin gona – Farfesa Dadari

Farfesa Salihu Adamu Dadari, malami ne a Sashen Bincike da Nazarin Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a tattaunawar da ya yi da wakilinmu kan harkokin noma a daminar bana, ya yi bayanin cewa Allah ne Ya kawo faduwar farashin kayan amfanin gona a bana.  Ya kuma tabo abubuwa da dama kan […]

Abin da ya kawo faduwar farashin kayan amfanin gona – Farfesa Dadari

Farfesa Salihu Adamu Dadari

Farfesa Salihu Adamu Dadari, malami ne a Sashen Bincike da Nazarin Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a tattaunawar da ya yi da wakilinmu kan harkokin noma a daminar bana, ya yi bayanin cewa Allah ne Ya kawo faduwar farashin kayan amfanin gona a bana.  Ya kuma tabo abubuwa da dama kan harkokin noma:

A matsayinka na masanin harkokin noma yaya ka ga yanayin yadda aikin  noma, ke tafiya a daminar bana?

Gaskiya aikin noma a daminar bana, sai dai mu yi wa Allah godiya. Domin na ga har inda ba a taba  nomawa ba a bara, a bana ana noma shi. Yanzu kowanne dan Najeriya ya koma noma da likita da injiniya da malami da dan siyasa, kowa ya koma noma.

Amma wadansu na cewa a bana, saboda karyewar farashin kayan amfanin gona, manoma sun yi baya kan aikin noma.?

A gaskiya a bana manoma sun yi noma. Sai dai saboda rashin fahimtar kasuwar duniya, wadansu manoman  sun canja abin da suke nomawa. Misali manomin da yake noma masara ya koma noma waken soya. To duk ba haka bane, domin amfanin gonar da ka saki sai ka ga Allah Ya daga shi. Domin wannan abin na Allah ne, ba na wayonmu ba ne. Wannan abu ya wuce hankali a ce wai ilimin zamani ne, ko wani tunaninka ne. A kullum ya kamata mutum ya yarda da ikon Allah, idan ka yarda da ikon Allah, abin da kake nomawa sai ka ci gaba da yi.

Yanzu misali wadanda suke noma barkono a da ba ya kudi, amma a bana sai ga shi ya zo ya fi kowanne kayan amfanin gona kudi. Sai kuma manoma su ce bari a bana, su noma barkona saboda ya yi kudi? Tana iya yiwuwa a badi ba zai yi kudi ba.

Mutane suna da mantuwa kullum yanayin kasuwar duniya yana canjawa. Don haka idan yanayin  kasuwar duniya ya canja ba a bin mamaki ba ne, yanayin kasuwa ya canja a Najeriya.  Kuma dole mutane su yi la’akari cewa yau da gobe sai Allah.  Ya kamata mu fahimci cewa tattalin arzikin Najeriya zai gyaru ne idan aka bunkasa noma.

Kuma a kullum ina kawo  misali da kasar Malawi lokacin tsohon Shugaban Kasar Dokta Kamuzu Banda yana Ministan Gona, kafin ya zama shugaban kasar.

A lokacin kowane kasafin kudin kasar idan za a yi, yana ba da fatawar farashin kayayyakin amfanin gonar da ake nomawa a kasar idan kaka ta yi. Wato ga farashin kudin kowane kayan amfanin gona  da za a saya, idan kaka ta yi. Don kowane manomi ya zabi kayan amfanin gonar da zai noma a damina mai zuwa.

Kuma idan gwamnati ta bayar da wannan farashin kayayyakin amfanin gona doka ce, babu wanda ya isa ya karya. Gwamnati za ta je kasuwanni da masayanta suna jira idan kowa ya gama sayen amfanin gonar, sai ta saye sauran rarar da aka rage.

Gwamnati ba za ta yarda kowane manomi ya koma gida da sauran amfanin gonar da ya kawo kasuwa ba. Takan saye ta je ta ajiye a rumbunan da ta tadana,  saboda haka manoma ba za su jigata ba. Kuma lokacin da farashi ya hau sai gwamnati ta fito da wadannan kayayyakin amfanin gona da ta adana, ta sayar kan farashi mai rahusa.

To me kake ganin ya sanya amfanin gona a bana farashinsa ya fadi kasa?

Ikon Allah ne Ya kawo karyewar farashin kayayyakin amfanin gona a bana. Idan aka fadi ikon Allah ai magana ta kare.  Mu dai muna kira ga gwamnati ta tsaya kada ta rika yarda ana shigo da kayan abinci da muke nomawa a Najeriya. Kamar shinkafa da masara da wake da  sauransu.

Domin idan ka shigo da kayayyakin abinci daga wata kasa ka kara wa wancan kasa karfin jari, kuma ka kara wa manoman kasar gonakin da suke nomawa, ka kara ba su damar da za su samar wa jama’arsu ayyukan yi. Sannan ka rushe manoman Najeriya tare rage tattalin arzikin kasar nan.

Kuma muna kara kira ga gwamnatin Najeriya da gwamnatocin jihohi su ba da muhimmanci ga noma, kuma su kirkiro yadda za su tallafa wa manoma.

Kuma al’ummar Najeriya mu tashi mu rungumi noma, domin muna da kasa da dausayi mai kyau. Manoman Najeriya  kada mu karaya yau da gobe sai Allah. Abin da manomi yake nomawa ya kara nomawa,  in da hali  ya kara noma wani kayan amfanin gonar, kada ya zauna kan noma abu guda daya kawai.

Yaya kake kallon dambarwar da ke faruwa kan Fulani makiyaya a Najeriya?

Wato al’amarin Fulani makiyaya a Najeriya, na farko ya kamata mu gane cewa su ma  ’yan Najeriya ne, don haka suna da ’yanci kamar kowane dan Najeriya. Kuma a kundin tsarin mulkin Najeriya ya nuna cewa kowane dan Najeriya yana da ’yancin ya zauna a duk inda ya ga dama, a Najeriya.

Saboda haka duk wannan hayaniya da ake yi a Najeriya kan Fulani makiyaya soki burutsu ne. Mutane ne kawai da suke son su sanya siyasa wadda ba za ta ba amfane  mu ba.

Don haka su ma Fulani makiyaya a ba su hakkinsu ta hanyar dawo musu da burtalolinsu da aka kwace a kowane yanki na Najeriya.  Kuma gwamnati ta gina musu madatsun ruwan da za su rika shan ruwa da  gina musu makarantu.

Bai kamata a rika nuna wa Fulani makiyaya kiyayya ba. Domin dabbobin da suke kiwo muna amfani da su wajen noma muna cin namansu. Don haka ya kamata a yawaita shanun nan a Najeriya.