Abin da ya kawo tabarbarewa a Katsina – Wayya
Harkokin kasuwancinai kara ja da baya a wannan lokaci a Jihar Katsina, inda mutum zai tarar da mafi yawan ’yan kasuwa suna zaune kodai a cikin shagunansu ko a tsakiyar kasuwa suna hira. Saboda harkokin kasuwanci ba sa tafiya yanda ya kamata. Alhaji Babangida Wayya Shinkafi, wanda aka fi sani da ‘Sauki Fish’ daya ne […]
Harkokin kasuwancinai kara ja da baya a wannan lokaci a Jihar Katsina, inda mutum zai tarar da mafi yawan ’yan kasuwa suna zaune kodai a cikin shagunansu ko a tsakiyar kasuwa suna hira. Saboda harkokin kasuwanci ba sa tafiya yanda ya kamata.
Alhaji Babangida Wayya Shinkafi, wanda aka fi sani da ‘Sauki Fish’ daya ne daga cikin matasan ’yan kasuwa a Jihar Katsina, ya bayyana wa Aminiya wasu daga cikin dalilan da suka kawo tabarbarewar harkokin kasuwancin a yanzu.
Dan kasuwar ya ce “A da ana ba ni kaya ba tare da na bayar da ko sisi ba, sai in na sayar in fitar da ribata in kai uwar kudin a sake ba ni wasu. Amma a yanzu hakan ba ta yiwuwa, wadannan dalilan ne jigon lalacewar kasuwanci. Abu na farko shi ne,karuwar al’umma, yawan al’umma ya sa harkokin suna ja baya, domin kowa ya taso shi ma zai ce kasuwanci yake so. Sannan ana iya samun mutum fiye da biyu ko uku a waje daya suna sayar da kaya iri daya.”
Ya ce “Wani abin shi ne, gasar da ta shigo a tsakanin ’yan kasuwar inda da zarar wani ya kyalla ido ya ga kana sayar da wani kaya kana samun ciniki shi ma sai ya fara sayar da irinsa. Sannan rade-radin da aka yi watannin baya na karin kudin man fetur ma ya taimaka wajen manyan ’yan kasuwa su janye bayar da kayansu daga kananan ’yan kasuwa.”
Ya ce wannan abu ya taimaka wajen koma bayan kasuwanci, domin hatta ’yan kasuwar kasashen waje a lokacin sun daina shigowa. Masu kaya a ciki suka fara janye kayansu saboda a lokacin suna ganin kamar Najeriyar ba za ta zauna lafiya ba.
Dan kasuwar ya ce hakan ya sa ’yan kasuwar da ake da su suka bar ba da kaya bashi ga kananan ’yan kasuwa.
“In za a ba ka kayan Naira dubu 50 to sai ka ajiye musu kudi a kasa koda Naira dubu 30 ne ko 20, kuma bayan kwana biyu su ce suna son sauran kudinsu,” inji shi.
Alhaji Babangida ya ce, matsalar ba ta yi karfi sosai ba sai daga shekarar 2014 zuwa yau, inda mai karamin karfi a harkar kasuwancin ba ya da inda zai sa kansa, bayan kuma shi ne tushe a harkar kasuwanci.
Babangida ya ci gaba da cewa, “Yanzu mai karamin karfi a kasuwanci ba ya samun bashi daga wajen manyan ’yan kasuwa ko manyan dillalai domin ya tafiyar da kasuwancinsa.
In ka ga an ba da bashin kaya a yanzu, to wanda aka ba an dauki dogon lokaci ana yi da shi kuma ba a taba samun matsala ba. Abin da ya sa kuma ba a bayar da bashi shi ne, saboda tsoron kada ka bayar da kayanka kudinka su ki fitowa,” inji shi.
Da yake bayani a kan tallafin gwamnati kuwa, Alhaji Babangida ya ce, tsarin da gwamnati ke bi wajen taimaka wa kananan ’yan kasuwa ba ya zuwa wajen da ya kamata ya je.
“Ana bayar da jagorancin bayar da tallafin ga wadanda ba su da adalci ko ba su da alaka da kasuwanci. Misali; za a bayar da tallafin kudin jari Naira dubu 10. Ga masu karamar sana’a, maimakon a ba su sai wanda aka dora wa nauyi, ya nemo kannensa ko dangin matarsa. Daga shekarar 2015 zuwa yau, an ba wani kudi ya kai sau goma ko sama da haka. An dauko siyasa an sanya a ciki. Saboda haka, kullum abin yana nan wuri daya ba a samun nasara daga bangaren Gwamnati,” inji shi.
Ya ce kamata ya yi duk wanda za a bai wa wakilci a tabbatar yana da alaka da kasuwanci ko wata sana’a ba wai dan siyasa ba.
Dan kasuwar ya ba da misali da kansa, ya ce mutanan da ya dauka aiki, a duk wata yana biyan sama da Naira milyan 2 ga ma’aikatansa baya ga kudin haraji da sauransu, amma har zuwa hirarsa da Aminiya babu wani daga gwamnati ko wani bangare da ya ce masa ya bayar da wata shawara ko tallafi don ci gaban kasuwanci.
Ya zargi hukumomin da ke kula da kwato wa ’yan kasuwa hakkinsu da ba su sauke nauyin da ke kansu ba.
Dan kasuwar ya ce, mafita ga wadannan matsaloli ita ce, a fitar da son zuciya. Gwamnati in za ta bayar da tallafi, ta tabbatar ta ba dan kasuwa wanda ya cancanta mai yin kasuwanci.
“Kuma a rika sanya sarakunan gargajiya duk lokacin da aka tashi bayar da irin wannan tallafi, domin koda sana’ar kulle-kulle mace ke yi a cikin gida mai unguwa ya san da ita, maimakon ’yan siyasa da ake ba kayan ’yan kasuwa. Kowa ya tsaya a matsayinsa ita ce mafita,” inji shi.
Ya ce akwai hanyoyi da yawa da za a tallafa wa harkokin kasuwanci, kuma masu bayar da wannan tallafi sun san kansu, “Mun kuma san in sun yi niyya za su yi,” inji shi.