Abin da ya sa aka cire wa shugaban Guatemala rigar kariya

A shekaranjiya Laraba ne ’Yan Majalisun Dokokin kasar Guatemala suka kada kuri’ar amince wa da cire wa Shugaban kasar Otto Perez Molina rigar kariya daga fuskantar tuhumarsa bisa zargin cin hanci da rashawa.dimbin masu zanga-zanga ne suka zagaye harabar Majalisar don ba da kariya ga ‘yan Majalisun dokokin yayin da suka fara hallara zauren majalisar […]

Abin da ya sa aka cire wa shugaban Guatemala rigar kariya
Abin da ya sa aka cire wa shugaban Guatemala rigar kariya

A shekaranjiya Laraba ne ’Yan Majalisun Dokokin kasar Guatemala suka kada kuri’ar amince wa da cire wa Shugaban kasar Otto Perez Molina rigar kariya daga fuskantar tuhumarsa bisa zargin cin hanci da rashawa.
dimbin masu zanga-zanga ne suka zagaye harabar Majalisar don ba da kariya ga ‘yan Majalisun dokokin yayin da suka fara hallara zauren majalisar don kada kuri’ar. kasar dai tana nahiyar Arewacin Amurka ne.
Shugaba Perez Molina ya tsallake irin wannan kuri’a a watan daya gabata, sai dai masu gabatar da kara sun zarge shi da hannu dumu-dumu a badakalar cin hancin miliyoyin daloli a hukumar hana fasakwauri ta kasar, sai dai ya sha musanta zarge zargen da ake yi masa. Kuma ana ganin wannan ne dalilin da ya sa majalisar cire masa rigar kariya.
A ranar Lahadi ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasar, kuma wannan kuri’ar da ‘yan majalisun suka kada matakin farko ne, yayin da shugaba Perez Molino ke dab da fuskantar shari’a kamar kowane dan kasar Guatemala.