…Abin da ya sa aka dauki wannan mataki
Sakataren Fadar Sarkin Abzin ya ce an dauki wadannan matakan ne saboda yadda koke-koke suka yi yawa daga al’umma kamar yadda BBC ta ruwaito. “Malamai daga unguwanni daban-daban suka jawo hankalinmu saboda yadda jama’a ke kai kuka wajensu domin ganin an dauki mataki. “Shi kansa Sarki ana yawan koka masa, shi ya sa aka ga […]

Sakataren Fadar Sarkin Abzin ya ce an dauki wadannan matakan ne saboda yadda koke-koke suka yi yawa daga al’umma kamar yadda BBC ta ruwaito.
“Malamai daga unguwanni daban-daban suka jawo hankalinmu saboda yadda jama’a ke kai kuka wajensu domin ganin an dauki mataki.
“Shi kansa Sarki ana yawan koka masa, shi ya sa aka ga ya dace a dauki wadannan matakan.”
A yanzu an sa ido don ganin ko wannan doka za ta dore ko kuwa ta dan lokaci ce za ta shude kamar yadda aka saba gani a sauran masarautu da suka dauki irin wannan doka a baya.