Abin da ya sa aka kasa magance garkuwa da mutane a Jihar Bauchi – danladi Gamji

Alhaji danladi Gamji shi ne shugaban kungiyar ’Yan Sintiri ta Jihar Bauchi, a tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana dalilan da suka sa har yanzu aka gagara magance matsalar masu garkuwa da mutane a kananan hukumomi biyar da matsalar ta zamo ruwan darea jihar: Me za ka ce kan matsalar satar mutane a jiharka?Kamar yadda kowa […]

Abin da ya sa aka kasa magance garkuwa da mutane a Jihar Bauchi – danladi Gamji

Alhaji danladi Gamji shi ne shugaban kungiyar ’Yan Sintiri ta Jihar Bauchi, a tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana dalilan da suka sa har yanzu aka gagara magance matsalar masu garkuwa da mutane a kananan hukumomi biyar da matsalar ta zamo ruwan darea jihar:

Me za ka ce kan matsalar satar mutane a jiharka?
Kamar yadda kowa ya sani ne jihohin kasar nan da dama suna fama da matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa wadansu bayan sun karbi kudin sai su yi lalata da matan da suka kama wasu lokuta ma har da kisan gilla. Wannan matsala tana neman zamowa ruwan dare a Najeriya kuma sama da kashi 85 cikin 100 na wadanda ake kamawa Fulani neda aka tabbbatar suna da dukiya.
Amma abin da zan fada wa gwamnoni shi ne ya kamata su tashi tsaye domin ba da gudunmawa ga kungiyoyin ’yan sintiri saboda muna da hanyoyin samun bayanai fiye da sauran hukumomin tsaro. ’Yan sanda da sojoji kadai ba za su iya magance matsalar garkuwa da mutane ba, dole al’umma da kungiyoyi irin namu sun ba da gudunmawa kafin kwalliya ta biya kudin sabulu.
A matsayina na shugaban wannan kungiya kullum sai na dauki kudina na sa mai a motocinmu domin kai samame a wasu sassan Jihar Bauchi. Na kan tura sama da mutum 50 cikin daji domin farauto masu garkuwa da mutane kuma na sha kama barayin shanu ina mika su ga Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi. Yarana da dama sun rasa rayukansu a sanadiyyar wannan aiki na yaki da masu garkuwa da mutane a baya ba mu da matsalar man fetur a motocinmu kowane lokaci aiki ya taso za mu je ba tare da bata lokaci ba.
Amma yanzu ga aiki amma babu alawus-alawus kuma muna fama da karancin motocin aiki. Don haka ina kira ga Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar ya taimaka wa wannan kungiya da take yaki da masu aikata miyagun laifuffuka a sassan jihar .
Wadanne kananan hukumomi suka fi fama da masu sace mutane?
kananan hukumomi shida ne suka fi fama da matsalar masu garkuwa da mutane, wato Ningi da Ganjuwa da Alkaleri da Bauchin da Toro da Darazo. Amma karamar Hukumar Toro ce kan gaba. Yanzu dubban mutane ba sa iya kwana a cikin gidajensu wadansu kuma sun kaurace wa yankin sun dawo cikin garin Bauchi da zama. Akwai wani mummunan daji ne a yankin Toro wanda ya hade da dajin Falgore wanda ya yi iyaka da jihohin Filato da Kaduna da Kano, kuma akwai duwatsu a dajin muna iya bakin kokarinmu tare da jami’an tsaro domin magance matsalar. Mutanen yankin Tulu da Rauta da ’Yuga suka fi fuskantar matsalar a yankin Toro kuma har yanzu mutanen yankin suna cikin mawuyacin hali wadansu sun yi noma amma suna tsoron zuwa gonakinsu saboda yadda masu garkuwa da mutane suka addabi yankin. Mun shiga dajin da ’yan sanda da sojoji kuma an samu gagarumin nasara, yanzu haka na tura mambobina sama da mutum 80 da suke aiki da sojoji da ’yan sanda.
Mene ne sakonka ga mutanen yankin Toro?
Babban sakona ga daukacin mutanen yankin Toro da sauran al’ummar Jihar Bauchi shi ne ya kamata su rika ba mu bayanan sarri duk wanda suka gani bakon fuska ne don Allah a sanar da mu domin daukar matakin gaggawa. Rashin ba da goyon baya da bayanan sirri na daya daga cikin abubuwan da suka sa aka gagara magance matsalar masu garkuwa da mutane a yankin Toro da jihar. Wasu daga cikin masu garkuwar sai mutum ya sa a kama mahaifinsa ko dan uwansa sai an kawo kudi kafin su sake shi. Muna fatar Allah Ya kawo mana karshen wannan matsala.