Abin da ya sa aka kasa tsige Al-Makura

Ga dukkan alamu Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta kasa tsige Gwamna Tanko Al-Makura ne saboda wadansu dalilai masu yawa.Na farko dai mutanen jihar sun nuna rashin goyon bayansu ga wannan matakin, wanda ya sanya har suka kona motar wani dan majali, a sakamakon barazanar da ake yi wa rayuwarsu ta sanya dole ‘yan majalisan suka […]

Abin da ya sa aka kasa tsige Al-Makura
Abin da ya sa aka kasa tsige Al-Makura

Ga dukkan alamu Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta kasa tsige Gwamna Tanko Al-Makura ne saboda wadansu dalilai masu yawa.
Na farko dai mutanen jihar sun nuna rashin goyon bayansu ga wannan matakin, wanda ya sanya har suka kona motar wani dan majali, a sakamakon barazanar da ake yi wa rayuwarsu ta sanya dole ‘yan majalisan suka kaurace wa garin Lafiya suka koma Karu da zaman majalisar.
Haka kuma nuna adawa da Janar Buhari ya yi ga yunkurin tsige gwamna daya tilo da tsohuwar jam’iyyarsa ta CPC ta samu ya kara wa yunkurin ‘yan majalisar bakin jini, Sannan akwai zargin da ake yi wa ‘yan majalisar cewa an ba su makudan kudi a Abuja domin su tsigen gwamnan, zargin da ‘yan majalisan suka karyata.
Haka kuma kafewar da ‘yan majalisan suka yi sai sun cire gwamnan, duk da sanya bakin da sarakuna iyayen kasa suka yi domin sasanta su, ya sanya mutane da dama sun dawo rakiyarsu, domin suna ganin domin biyan bukatar wadansu suke son cire gwamnan, ba don amfanin jihar Nasarawa ba.
Rashin samun cikakken hadin kai daga babban jojin jihar Nasarawa ya jawo wa ‘yan majalisan matsala, domin mutanen da ya nada a kwamitin da suka ce ya kafa ba su gamsar da su ba.
Idan za a iya tunawa dai Kwamitin Binciken Gwamna Umaru Tanko Al-Makura da Majalisar Jihar ta umarci Babba Jojin Jihar Nasarawa Mai shari’a Suleiman Umaru Dikko ya kafa don duba zarge-zargen da majalisar ke yi masa a yunkurinsu na neman ke tsige shi ya yi watsi da zarge-zarge 16 da wakilan majalisar suka yi masa kan almundahana da dukiyar jama’ar jihar.
Shugaban Kwamitin Malam Yusuf Shehu Usman ne ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata a lokacin zaman kwamitin na karshe da aka gudanar a dakin taro na Ma’akatar kananan Hukumomi da Harkokin Masarautun Gargajiya ta Jihar da ke Lafiya.
Ya ce ’yan majalisar sun kasa bayar da ingantacciyar shaida a kan zargen-zarge16 da suke yi wa Gwamnan don haka a cewarsa ya zame wa kwamitin wajibi ya yi wasi da koke-koken.
An yi ta samun takun-saka kan halaccin hanyar da majalisar ta bi wajen aika wa Gwamnan sammaci, kuma bayan da Babban Jojin ya kafa kwamitin, sai majalisar ta nemi ya rushe shi ya sake kafa wani saboda ba ta yarda da wasu wakilan kwamitin ba, wannan ya jawo muhawara a tsakanin lauyoyi inda wasu suka ce ba aikin majalisar ba ne ta ce masa ga mutanen da ya kamata ya nada. Wannan ya sa ’yan majalisar wadanda galibinsu ’yan jam’iyyar adawa ta PDP ne suka ce ba za su halarci zaman kwamitin ba, sai dai daga baya sun tura lauyoyinsu.
Jagoran lauyoyin ’yan majalisar Olcha Ufendode ya nuna rashin amincewa da mambobin kwamitin inda ya ce tsarin mulki ya nuna cewa bai dace a zabi dan siyasa ko ma’aikacin gwamnati ya zama wakilin kwamitin ba, saboda haka ya bukaci Babban Jojin ya rushe kwamitin ya kafa wani saboda mutum uku daga cikinsu a cewarasa ’yan siyara ne. Daga nan sai ya sanar wa kwamitin cewa ba za su ci gaba da halartar zaman ba kuma ba za su gabatar da shaida ba game da zarge-zargen sai an kafa wani kwamitin daban.
Babban lauyan Gwamna Al-Makura, Mista Udochuku O. Udochuku ya bukaci kwamitin ne ya yi watsi da zargin lauyoyin ’yan majalisar saboda kasa bayar da shaidar da za ta tabbatar da zargezargen nasu.
Shugaban kwamitin ya amince da wannan bukata inda bayan dawowa daga hutun minti 30 ya sanar da yin watsi da zarge-zargen.  
Gwamna Umaru Al-Makura ya ce matakin da kwamitin ya dauka na watsi da zarge-zargen da majalisar ke yi masa nasara ce ga dimokuradiyya da kuma al’ummar jihar.  Gwamnan ya bayyana haka ne a gidan gwamnati da ke Lafiya jim kadan da kwamitin ya yi watsi da zarge-zargen.
Ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata al’ummar jihar baki daya musamman ’yan majalisar su zo su hada hannu don ci gaba da gina jihar maimakon zargi na ba gara ba dalili da a ccewarsa ba zai yi wa jihar da su kansu alheri ba.
Tun lokacin da majalisar ta fara yunkurin tsige Gwamna Al-Makura aka rika gudanar da zanga-zangar adawa da yunkurin a sassan jihar lamarin da ya tilasta ’yan majalisar kaurace wa zaman majalisar a Lafiya suka koma Karu a kusa da Abuja.
Sarakunan gargajiya a nasu bangaren sun yi kokarin hana ’yan majalisar daukar wannan mataki, amma wasu majiyoyi suka ce uwar Jam’iyyar PDP da fadar Shugaban kasa sun tsaya kai da fata sai an tsige Gwamna Al-Makura.
’Yan majalisar sun yi watsi da hukuncin kwamitin a ranar Talatar a wani taron manema labarai da shugaban kwamitin labarai na majalisar Mohammed Baba Ibaku ya kira a Abuja. Ya ce tun farko majalisar ta ki amincewa da zubin wakilan kwamitin kuma ba za ta amince da shawarar da kwamitin ya zartar ba.
“A wurinmu ba a wanke Gwamnan daga zarge-zargen da ake yi masa ba; ba za mu je kotu ba, saboda lamarin na tsarin mulki ne da ba wata kotu da za ta warware shi. Za mu dauki matakin da ya dace kan lamarin nan gaba kuma za mu bi tsarin mulki; ba za mu yi abin da ya saba wa tsarin mulki ba, amma ina tabbatar muku za mu ci gaba da batun tsigewar,” inji Ibaku.
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Nasarawa ta goyi bayan ’yan majalisar kan matakin da suka dauka. Wata takardar bayan taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar dauke da sanya hannun mutum 84 ne ta bayyana haka a ranar Talata. PDP ta bukaci jami’an tsaro su ba da kariya ga ’yan majalisar don gudanar da aikinsu, kuma ta nemi al’ummar jihar su kasance masu bin doka da oda, kuma ta ce za ta jajirce wa duk wani yunkuri na Jam’iyyar APC na kawo cikas ga dimokuradiyya a jihar.