Abin da ya sa aka zabe ni Gwamnan Bauchi – Bala Muhammad
Sanata Bala Muhammad shi ne zababben Gwamnan Jihar Bauchi, a zantawarsa da ’yan jarida a Bauchi ya bayyana dalilin da ya sa aka zzabe shi da yadda zai tafiyar da jihar: Me za ka ce game da wannan nasara da ka samu? Muna godiya ga Allah da Ya ba mu nasara a matsayinmu na mutane […]
Sanata Bala Muhammad shi ne zababben Gwamnan Jihar Bauchi, a zantawarsa da ’yan jarida a Bauchi ya bayyana dalilin da ya sa aka zzabe shi da yadda zai tafiyar da jihar:
Me za ka ce game da wannan nasara da ka samu?
Muna godiya ga Allah da Ya ba mu nasara a matsayinmu na mutane kuma ’yan Bauchi musamman ma Jam’iyyar PDP, wadda Allah cikin ikonSa da rahamarSa Ya sa yau ni ne zababben Gwamnan Jihar Bauchi. Kuma dan uwana mutumin kirki Sanata Baba Tela shi ne Mataimakin Gwamna. A gaskiya mutane da yawa sun ba da gudunmawa, musamman malamai da iyayenmu da sarakunanmu, da matasa mata da maza da ’yan jarida, duka muna godiya Allah Ya saka da alheri. Wannan mulki da muka samu abin a yi godiya ne amma akwai kalubale da yawa, saboda haka za mu yi iya kokari don kada mu ba wa al’umma kunya, za mu yi kokarin hada kan al’ummar Jihar Bauchi kuma za mu kawo wani shiri da zai fitar da mu daga cikin wahala da talauci da wahala wajen haihuwa da tabarbarewar ilimi da kiwon lafiya da harkokin noma insha Allahu. Kuma za mu fito da kwararru ’yan Jihar Bauchi wadanda aka san mu da su wadanda za su yi wadannan ayyuka saboda muna bukatar mu ga cewa mun cimma burinmu na kawo wa Bauchi ci gaban da za ta fi sauran jihohi kamar yadda muke yi a baya. Ina kuma kira ga ’yan uwanmu su san cewa wannan aiki ba mai sauki ba ne. Muna godiya ga duk wadanda suka ba mu wannan dama, mun san cewa ba mun fi kowa ba ne, da ni da mataimakina da kuma Jam’iyyar PDP. Sai dai lokaci ne da ya zo na neman canji. Muna fata za a rika ba mu shawara ana taka mana birki a inda aka ga cewa mun yi kuskure.
Gwamnan Bauchi ya taya ka murna cikin wata takardar sanarwa da muka samu ko ka samu wannan takarda ?
Har yanzu ban samu ba amma na ji labari cewa an tura ga kafafen labarai amma koma ba ta zo ba, kamar yadda muka ce kowane dan Jihar Bauchi an ba shi dama na ba da gudunmawarsa don ci gaban jihar nan, ko shi tsohon Gwamna ne, ko tsohon kwamishina ne ko babban sakatare, burinmu mu hada kan Jihar Bauchi mu nemo wadanda suka kware mu yi aiki don ceto jihar saboda komai ya tabarbare a jihar.
Ka ce za ka yi siyasa ba da gaba ba, shin za iya cewa gwamnatinka ba za ta binciki gwamnatin baya ba?
Ba haka ba ne, kamar yadda na yi lokacin ina Ministan Abuja, ni bincikena ina yi ne cikin hikima da ilimi cikin tsari babu kwaramniya babu gaba, amma abubuwa da yawa nakan dawo da su baitul malin gwamnati ba sai na yi hargowa ba kamar yadda na dawo wa Abuja da kudade da yawa. Duk inda na ga barna zan yi kokari in gyara in kuma an tafi da dukiya ko kadarar gwamnati zan yi kokari in karbo cikin hikima ba tare da na yi batanci ko bata suna ba. Sai dai wadanda suka yi taurin kai, ko suka nuna izgilanci da sauransu, shi ne dole sai mun bi ta hanyar hukuma.
Da me za ka fara wannan gwamnati, cikin kwanaki 100 na farko?
Ina so in kawo mutunci ga ’yan kwadago a Jihar Bauchi, saboda ba a biyan mutane albashi a kan lokaci, ba a biyan fansho da garatuti, kuma talauci ya addabi Jihar Bauchi. ’Yan kasuwa suna wayyo saboda ma’aikata ba sa samun yadda suke so kasancewar jihar ta ma’aikata ce, amma ba su iya zuwa kasuwa su sayi komai. Saboda haka zan dawo da mutunci da hakkin mutane wadanda suke aikin gwamnati a Jihar Bauchi,
Wace dabara za ka yi wajen gudanar da wadannan ayyuka ganin cewa ana bin jihar basussuka da yawa?
Gaskiya ne muna da matsalar nan, domin an ce ana bin bashin sama da Naira biliyan 26 na garatuti da fansho amma komai bai gagari Allah ba. Kuma ba zai gagare mu ba saboda na zauna a Birnin Tarayya na samu bashi da ake bin mu sama da Naira biliyan 50 na biya, zan bi hanyoyin biya cikin hikima da tsari ta yadda ake rarraba kudaden gwamnati da ake kira (Cash Flow) kuma zan yi kokari in ga cewa mun samu kudin shiga yadda zai kasance ba za mu ta’allaka a kan kudin da ake ba mu daga kason tarayya ba.