Abin da ya sa ake cincirindon zuwa Amurka domin haihuwa
Da yawan mata ’yan asalin Afirka da Chaina yanzu sun mayar da zuwa Amurka haihuwa tamkar wani abu na bakin rai bakin fama. Wasu matan da wakilin Aminiya ya tattauna da su, cewa suka yi wannan wata dama ce na su dawo Amurka da mazajensu su ci gaba da zama. Wasu kuma suka ce ko […]

Da yawan mata ’yan asalin Afirka da Chaina yanzu sun mayar da zuwa Amurka haihuwa tamkar wani abu na bakin rai bakin fama.
Wasu matan da wakilin Aminiya ya tattauna da su, cewa suka yi wannan wata dama ce na su dawo Amurka da mazajensu su ci gaba da zama.
Wasu kuma suka ce ko ba komai suna da tabbacin samun tsaro kuma za su haihu a inda za a kula da lafiyarsu da abin da suka haifa, kana idan sun sauka lafiya har abin da za su ciyar da yaran ma suna iya samu.
Wasu daga cikin abubuwan da matar da ta haihu a Amurka za ta anfana da su su ne: dan da ta haifa shi ma ya zama dan Amurka, kuma duk wata dama da wani dan Amurka zai samu shi ma yana da wannan damar.
Misali ilmi kyauta ne, kiwon lafiya kyauta ne, kuma yana da damar yin takara daga mukamin kansila har zuwa na Shugaban kasa, sannan iyayen suna iya zama ‘yan kasa idan suna bukatar hakan.
Akwai takardar da ake bayarwa na kyautata rayuwar dan kasa wanda da turanci ake kira (SOCIAL SERURITY CARD). Wannan katin duk wanda zama ta kamashi a Amurka, dole ya mallake shi. Idan baka da wannan katin, tamkar baka cikin lissafin Amurka. Shi ma yaron da aka haifa shi ne abu na farko da ake bashi, da wannan katin ne za ka iya samun duk wata dama a Amurka.
Hajiya Hafsatu Adamu da ta jima a Amurka ta ce ta karbi bakuncin ‘yan Afirca da dama da suka baro gida domin zuwa Amurka su haihu kuma da yawansu suna biyanta ne kafin ta ba su matsugunni na tsawon lokacin da za su kasance a Amurka.
Amma wani bincike kuma ya tabbatar cewa wasu matan suna zuwa wajen wasu ‘yan uwansu ne ko kuma su kama hayan gida daga wata uku zuwa shekara, domin bincike ya nuna masu zama a Otel kalilan ne idan aka kwatanta da masu zama gidajen mutane. Idan ka cire Los Angeles.
Hukumar shige da fice ta Amurka ta ce a cikin shekarar 2015 kawai, ta bai wa mata ‘yan China takardan iznin shigowa Amurka (bisa) har miliyan 2.27 domin su zo haihuwa
Sai dai kuma hukumar ta fara samun damuwa da ‘yan kasar ta China. Jama’an da ke zaune a wurin da ake kira San Gabriel balley inda nan ne ake samun cincirindon ‘yan kasar China sai da suka kai kukansu ga jami’an tsaro cewa ‘yan China sun cika wurin har ma da wadanda suka shigo ta barauniyar hanya.
A shekarar 2013, sai da hukumar mulkin Los Angeles ta samar da wani kwamitin sha-yanzu magani-yanzu a kan masu shigowa garin domin haihuwa.
Wannan kwamitin ya gano wurare har 34 da yawancin mutanen da ke cikinsu masu zuwa haihuwa ne daga wata kasa.
Karin Wang, mataimakiyar ‘yan kungiyar ‘yan Asiya ta ce abin da ke damun ta shi ne yadda wannan dabi’ar zuwa a haihu a Amurka daga kasashen yankin Asiya ke haifar wa ‘yan yankin bakin jini da kyama a wajen ‘yan Amurka.
Ta ce babban abin takaicin ma shi ne yadda suke yaudaran jami’an shige da fice. Kuma idan sun haihun ba su wuce wa kasarsu, sai su jira har sun gudanar da al’adar nan ta China da ake kira ZUO YUEZI.
Kusan ana iya cewa Los Angeles ne matattaran ‘yan kasar China masu zuwa Amurka neman haihuwa.
Wakilin Aminiya ya yi kicibis da wata baiwar Allah ‘yar kasar China a Washington DC wadda ke dauke da juna biyu mai suna Zhu, inda ta ce ba ta da aure amma kuma daga Guangdong ta zo domin haihuwa, sannan ta ce ba ta yanke shawara ko za ta koma gida ba ko kuma ta ci gaba rayuwa a nan Amurka.
Ta ce daya daga cikin abin da ya sa ta zo nan Amurka shi ne domin ta guje wa tsarin kayyade iyalai wanda ya fi tsanani a kan masu cikin da ba su yi aure ba.