Abin da ya sa Atiku ba zai hakura da takara ba – Usman Tama

A Kwanan baya ne aka kaddamar da kungiyar Magoya bayan Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar na jihohin Arewa maso Gabas.  Alhaji Usman Tama (Wazirin Tama), wanda gogaggen dan siyasa ne da ya yi jami’in mulki na jihohin Bauchi da Gombe a tsohuwar Jamiyyar NPN a lokacin jamhuriyya ta biyu, kuma ya rike mukamai daban […]

Abin da ya sa Atiku ba zai hakura da takara ba – Usman Tama

A Kwanan baya ne aka kaddamar da kungiyar Magoya bayan Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar na jihohin Arewa maso Gabas.  Alhaji Usman Tama (Wazirin Tama), wanda gogaggen dan siyasa ne da ya yi jami’in mulki na jihohin Bauchi da Gombe a tsohuwar Jamiyyar NPN a lokacin jamhuriyya ta biyu, kuma ya rike mukamai daban daban na siyasa a Jihar Bauchi, shi ne aka kaddamar a matsayin shugaban kungiyar ta Magoya Bayan Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar. A zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan an kaddamar da su ya bayyana dalilan kafa kungiyar.  Ga kadan daga cikin yadda hirar ta kasance:

 

Aminiya: Ko mece ce manufar kafa wannan kungiya ta goyon bayan Atiku?

Manufar kafa wannan kungiya ita ce domin mu fito fili wajen kara hada kanmu mu nuna kyakykyawar goyon bayanmu domin cimma burin da muke da shi na ganin Allah madaukakin sarki Ya amsa addu’armu na jawo hankalin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya karbi kirayen kirayen da alu’mmar Najeriya ke yi masa ya fito ya sake tsayawa takara a shekarar 2019. In Allah Ya kaimu. kuma kamar yadda na fada maka wannan yunkuri na mu shi ya jawo muka kara himma don mu hada kai mu dunkule wuri guda mu kara fuskantar al’ummar Najeriya da ma al’ummar wannan shiyya na Arewa maso Gabas wanda a shiyyar ne Atiku Abubakar ya fito. Mu kuma mu kara nema masa goyon bayan al’ummar wannan shiyya da ma Najeriya baki daya tun da hannu daya baya daukar jinka. Sannan idan muka hada kai za mu samu karfin kara shiga lungu da sakon ko ina cikin kasar nan domin mu sama masa karin goyon baya da nufin Allah Ya ba mu nasara.

Aminiya: Hidimar Siyasa abu ne mai wahala. A matsayinka na gogaggen dan siyasa wace hanya kake gani za agyara?

Wannan Gaskiyane, duk mutumin da Allah zai bashi wani mukami na siyasa ko takara ko wani abu, tilas sai ya hada da hakuri saboda mutane daban daban kuma halayen da Allah Ya musu daban. Wadansu ‘yan ta fadi gasassane, su ne suka fi sa’ar siyasa ba su sha wahala ba. Idan Allah Ya tsaga rabonsu  sai ka ga an jawo su ana ci da su kuma sun fi wadanda suka sha wahalar iko da cin moriyar tafiyar, Wasu da suka sha wahalar ma har a gama mulkin ba za su lashi komAi ba, wadansu kuma na da gaggawa ne, musamman a mulki irin na yau, dole mai mulki sai ya yi hakuri kuma sai ya yi zurfin tunani ya sa kishi da kokarin tafiya da kowa da kowa. Kuma ya bude zuciyarsa da kunnuwansa, ya sa ido sosai, idan ya yi haka zai rage matsalolin, kuma komai zai wuce, Sannan wajen takara wajibine a yarda da Allah shi ke bada mulki ga wanda ya so a lokacin da yaso, idan an hada da hakuri anyi ayyuka na gari sai ka ga an cimma nasara.

Aminiya: Ranka ya dade mutane na ganin Atiku ya yi ta neman wannan mukami bai samu ba, Me ya sa ba za ku hakura haka ba?

Dariya…. Ka san ita siyasa yadda al’amarin yake kowane dan siyasa yana da dan takarar da yake kallo kuma yake kyautata masa zaton alheri tattare da shi, kuma shi siyasa da goyon bayan dan takara abu ne da ke cikin jinin masoyi. Don haka a duk lokacin da aka kada gangar siyasa, sai ka ga idan dan takaran da kake goyon baya bai fito anyi da shi ba, sai ka ji duk baka jin dadi, domin kai da kake goyon bayan dan takaran ka kana da kishin jama’arka kuma kana da abubuwan alherin da kake gani a tare da dan takaran da yasa kake gani idan har ya yi nasara to ga irin alherin da zai jawowa al’umma ga kuma irin taimakon da kake gani kuma kake kyautata zaton cewa shi kadai ne kawai zai yi. 

Saboda haka sai ka rika kwadayin wannan alheri, kana kuma kwadaitar da shi dan takarar. Kuma masu zabe kuna kara wayar musu da kai, da haka har Allah Ya baku sa’a, saboda haka batun cewa Atiku ya yi ta takara bai yi nasara ba, haka ne komai da lokaci mafi alheri da Allah Ya zaba wa jama’a. haka shi ma Atikun da mu da muke goyon bayansa muna kokarine domin mu dace da lokaci mafi alheri da Allah zai cika mana burinmu mu ganshi ya zama Shugaban kasar Najeriya, saboda haka ne ba zamu gaji ba, shi ma ba zamu barshi ya huta ba, za mu yi ta kokari har Allah Ya sa mu dace. Musamman da muke gani yanzu kamar Allah Ya kawo mana lokaci.

Aminiya: Tun ba a fara siyasa ba kun matsa da kira ga Atiku ya fito, ko me yasa?

Atiku ya wuce wani ya masa kira sai dai mu kara bashi goyon baya tunda shi jama’a na sonsa kuma ya karbi kiran jama’a tun tuni, shi ma yana so ya bada gudummawar da yake ganin ya dace wajen gina kasar nan, yana so Allah Ya bashi mulkin da zai yi wa A’lummar Najeriya kyakykyawar jagoranci cikin alheri. Ka ga yanzu jama’a da kungiyoyin siyasa da dama ke ta tururuwa suna zuwa gareshi kuma yana tsaya musu yana kuma yi musu taimako gwargwadon yadda ya dace don haka Atiku tsayayyaye ne.

Aminiya: Mece ce cancantar Atiku?

Gaskiya Atiku mutuum ne daya dade yana siyasa. kankararren dan siyasa ne, ko kafin ya zama Mataimakin shugaban kasa ya ci zabensa ya zama Gwamnan Adamawa, tun lokacin da ya fara takara kowa ya san ya cancanta saboda halayensa na kirki. Mutumne ne mai taimako mai sauraron jama’a, kuma mai burin ganin Najeriya ta ci gaba ta fita daga kangin talauchi da fatara, kuma a samu yalwar arziki da zama lafiya mai dorewa. Kamar yadda na fadi da farko, Atiku mutuum ne da zai yi shugabanci abin misali.

Aminiya: ‘Yan Arewa maso Gabas na gani Atiku ya sami dama amma ba abin da ya musu.

A’a wannan yarfe ne kawai na siyasa.Ai mutum irin Atiku ayyukan alherin da ya yi a Arewa Maso Gabas suna da yawa, hakan ne ma ya mayar da shi babban gwarzo kuma jagora a siyasar Najeriya. Ai Atiku bai da bangare ko gefe, ba Arewa maso Gabas ba, dukan Najeriya babu bangaren da alherinsa bai kai ba, ka duba miliyoyin magoya bayan da yake da su a duk fadin kasar nan. Wasu ya samar musu da ayyuka suna taimakon kansu da iyalansu da jihohinsu. Wadansu ya samar musu da ayyuka daga Gwamnatin Tarayya. Kai ko a Adamawa ya kakkafa kamfanoni da makarantu har ma da gidan rediyo da ‘ya’yan jihar ke aiki a karkashi suna samun abinci, Atiku ya yi komai daidai gwargwado wa ‘yan kasar nan. Kuma ka san ba a san maci tuwo, sai miya ta kare, yanzu dai dukan harkar da ya taso a kasar nan fagen ilimi, kasuwanci da walwalar Jamaa ko a inane, Atiku na zuwa ya taimaka, idan ana so a kara ganin kwazonsa a ba shi dama ya shugabanci kasar nan a gani, sai a ga kwazonsa. Amma yanzu duk wanda ya ce bai yi ba, bai masa adalci ba.

Aminiya: Wace shawara za ka bai wa al’umma?

Shawarar da za mu bayar ita ce mu al’ummar Najeriya mu fahimci matsalolin kasar nan ta mu, musanmman matsalolin yunwa, fatara, talauchi, da rashin aikin yi, da rashin kyakykyawar rayuwa. Mu duba ya ya za a iya warware wadannan matsaloli. Kuma wane shugaba ne zai iya zuwa ya kawar mana da wadannan matsaloli, ko kuma ya sama mana sauki a kansu? idan mun samo amsar to wannan shi ne zai taimakemu wajen zabo shugabanni nagari a 2019.