Abin da ya sa ba mu halarci taron yaki da ta’addanci na Abuja ba – Sheikh Jingir

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, wanda aka rika yada jita-jita a kafafen sadarwa na zamani cewa ya rasu a karshe da farkon wannan mako, ya samu tattaunawa da Aminiya game da wasu matsaloli da suka hada da gina cibiyar da kungiyar ke […]

Abin da ya sa ba mu halarci taron yaki da ta’addanci na Abuja ba – Sheikh Jingir
Abin da ya sa ba mu halarci taron yaki da ta’addanci na Abuja ba – Sheikh Jingir

Sheikh JingirSheikh Muhammad Sani Yahya Jingir Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, wanda aka rika yada jita-jita a kafafen sadarwa na zamani cewa ya rasu a karshe da farkon wannan mako, ya samu tattaunawa da Aminiya game da wasu matsaloli da suka hada da gina cibiyar da kungiyar ke yi a Abuja da kuma rashin halartarsa taro kan zaman lafiya da bangaren su Sheikh Abdullahi Bala Lau suka shirya a Abuja. Ga yadda tattaunawar ta gudana:

Aminiya: kungiyar Izala tana gina wata cibiyar Musulunci a Abuja, mene ne makasudin gina wannan cibiya?
Sheikh Jingir: Gaskiya kamar yadda kuka sani kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, kungiya ce ta wa’azin addinin musulunci da rayar da Sunnar Manzon Allah (SAW) da dogara hujjoji na Alkur’ani da Hadisi da fahimtar Malaman Sunnah, musamman a wannan nahiya da muke bin Mazahabar Malikiyya. A lokacin da aka kafa wannan kungiya babban aikinta shi ne yi wa jama’a wa’azi a birane da kauyuka. Hedkwatar wannan kungiya tana nan garin Jos ne babban birnin Jihar Filato. Wato wurin da wanda ya kafa kungiyar marigayi Sheikh Isma’ila Idris  yake da zama a lokacin da aka kafa ta. Ganin cewa a yanzu Abuja ce cibiyar kasar nan, inda fadar gwamnatin kasa da Shugaban kasa  da wakilan majalisun tarayya da manyan ma’aikatun gwamnati, muka ce ya zama wajibi mu zo birnin mu kafa cibiyar yada addinin Musulunci a bangaren ilimi. Saboda wadannan mutane su da matansu da ’ya’yansu su samu majuya ta samun tataccen ilimi wanda yake hade da aiki. Don haka muka yi kokarin samun filin da za mu gina cibiyar da makarantu tun daga kananan zuwa sakandare zuwa gaba da sakandare. Allah Ya ba mu iko muka samu wannan fili a lokacin tsohon Ministan Abuja Sanata Adamu Aleiro aka tabbatar mana muka yi ta cika ka’idojin abubuwan da muke son mu yi har gwamnati ta amince ta sanya mana hanu.
Bayan da aka amince mana sai muka kafa kwamitin da zai gudanar da wannan aiki a karkashin tsohon Ministan Abuja, Dokta Aliyu Moddibo. A cikin ’yan kwamiti har da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu da tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu da Mai bai wa
Shugaban kasa Shawara kan Majalisar Wakilai, Alhaji Abdurrrahman Kawu Sumaila da Mataimakina na farko Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun da Mataimakina na biyu Sheikh Sa’idu Hassan Jingir da Shugaban kungiya Sheikh Abdul-Nasir Abdul-Muhyi da Daraktan ’Yan Agaji na kasa Alhaji Isah Waziri Gombe da sauransu. Na hada su na ba su gudanar da wannan aiki. Muka dogara ga Allah muka fara wannan aiki, yanzu aiki ya fara kankama domin mun kashe kudi kusan Naira miliyan 160  ta hanyar gudunmawar da  talakawa da manyan masu dukiya suka bayar.

Aminiya: Mun san cewa wannan kungiya tana da makarantu tun daga na firamare zuwa na gaba da sakandare, shin a wannan wuri nr kungiyar take son gina jami’a ko za ku bude rassanta ne a ko’ina?
Sheikh Jingir: To, da farko dai muna da wurare  har guda uku da muke son mu kafa jami’a. Na farko mun sayi wani fili a nan Jos a hanyar Zariya a kusa da Yelwan Matabo, har mun gina dakunan gudanarwa. Na biyu tsohon Gwamnan Jihar Neja Alhaji Babangida Aliyu a lokacin da ya zo wajen kaddamar da gudunmawar raya ilimi da muka gudanar bara a Abuja ya ba mu wani babban  fili a Jihar Neja don mu gina jami’a. Tuni mun kafa kwamiti kan wannan al’amari mun gana da wasu jami’o’I da farfesoshi da daktoci a kan lamarin. Muna ci gaba da shirye-shirye kan lamarin idan muka kammala za mu yanke shawara shin a Jos ko Minna ko Abuja ne za mu kafa jami’ar.

Aminiya: Ganin irin muhimmancin da kafofin watsa labarai suke da  shi, ina aka kwana kan maganar bude gidan rediyo da talabijin da wannan kungiya take shirin yi?
Sheikh Jingir: A gaskiya an kwana a wani mataki mai faranta rai kan al’amarin. Kuma saboda lura da yadda mutane suka sanya siyasa da farfaganda a ciki, sai muka tuno wata karin magana ta Hausawa da ke cewa ba a yi ciki don tuwo ba kawai. Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce idan za ku nemi wasu abubuwa na alheri ku boye asirinku, sai kun kai wata gaba sai a ji ku. Amma ina shaida muku cewa za ku ji kyakkyawan labari kan wannan al’amari. Muna da shiri mai karfi kuma mun riga mun yi nisa.

Aminiya: Baya ga maganar bunkasa ilimi, wannan kungiya ta dauki harkokin kiwon lafiya da muhimmanci, shin wane hali ake ciki dangane da harkokin bunkasa kiwon lafiya a yanzu?
Sheikh Jingir: Babu shakka muna da sashin lura da harkokin kiwon lafiya a wannan kungiya. A wannan sashi muna da asibitoci da muka gina wadanda idan ka gan su sai ka dauka gwamnati ce ta gina su, ko kuma ta ba mu kudi muka gina. Amma da hadin kan nan namu muka tara kudade muka gina asibitocin. Idan ka bi diddigi babu inda za ka ga mun samu kudi daga wata kasar waje, mu ne da kanmu muka tara taro da sisi muka gina wadannan asibitoci. A nan Jos muna da babban asibiti mai Sunnah da muka gina. Wannan asibiti mun hada masa komai na kayan jinya tare da likitoci da sauran ma’aikata wadanda suke aiki dare da rana. Mun gina wani asibitin a garin Dengi a karamar hukumar Kanam da Barikin Ladi  a nan jihar Filato kuma mun gina wani asibitin a Gombe. Dukkan wadannan asibitoci suna nan suna aikin jinyar marasa lafiya dare da rana.

Aminiya: A makon jiya su Sheikh Abdullahi Bala Lau suka shirya wani taro a Abuja kuma sun ce sun gayyace ku ba ku je, shin idan sun gayyace ku, mene ne ya sa kuke ganin bai da ce ku je  wurin taron ba?
Sheikh Jingir: Wato su Sheikh Abdullahi Bala Lau mutanenmu ne kuma almajiran malaman wannan kungiya ce, wadanda aka horar da su a makarantunmu. Don lokacin da aka fara tafiyar wannan kungiya su suna yara ne. Mun samu ’yar matsala a wannan kungiya bayan ta shekara 13 da kafuwa, inda aka samu rabuwa har aka rika yi mana lakabi da ’yan Jos da ’yan Kaduna. Marigayi Sheikh Isma’ila Idris da ya kafa kungiyar da duk wadanda muke tare da shi, sai ana kiranmu ’yan Izalar Jos. Sheikh Yusuf Sambo da yake zaune a garin Kaduna  wanda yake shugabancin malaman da suka gabatar da shi a matsayin shugaba sai ana kiransu da ’yan Izalar Kaduna.
Bayan mun shekara 20 cikin wannan hali sai Allah Ya nufa a lokacin rasuwar marigayi Shugaban Gudanarwa na kungiyar Alhaji Musa Maigandu muka je ta’aziyar rasuwarsa a Bauchi, muka hadu da su Sheikh Yusuf Sambo da sauran malamai, sai na ce ya kamata mu duba gaba mu duba baya. Ina marigayi Sheikh Abubakar Gumi da marigayi Sheikh Isma’ila Idris da Gado da Masu suke? Dukkansu sun koma ga Allah, don haka ya kamata mutuwar nan ta zamanto mana wa’azi. Mu daina cece-ku-ce mu zo mu hada hannu mu hada kai mu yi wa addinin Allah aiki. Nan take Allah Ya yi wa wannan kira da na yi albrka sai muka ce daga ranar zuwa mako biyu mu taru a Kaduna. Mu kaddamar da sake hadewarmu tare da yarjejeniya. Allah da ikonSa kafin wannan rana da muka ajiye za mu kaddamar da sake hadewarmu sai ga shi mutanenmu daga ko’ina, duk sun hade an rage duk wata takaddama.  To kafin mu je taron na Kaduna tunda da ma su a tafiyarsu marigayi Alhaji Musa Maigandu ne Shugaban Gudanarwa sai suka yi taro a Katsina suka fitar da Sheikh Abdullahi Bala Lau a matsayin Shugaban Gudanarwa na bangarensu. Da muka zo taron sake hadewarmu sai aka ce ni na shugabanci Majalisar Malamai ta wannan kungiya Mataimakina na daya Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya sauka ya dawo Mataimakina na biyu shi kuma Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya zama Mataimakina na daya. Sannan muka ce marigayi Alhaji Na-Alhaji Azare ya zamo Shugaban Gudanarwa su ba da wanda zai zama mataimakinsa. Sai suka ce tunda mun karbi jagorancin Majalisar Malamai wajen shugabancin gudanarwa a ba su. Sai muka ce mun yarda  don haka  aka zabi Sheikh Abdullahi Bala Lau a matsayin Shugaban Gudanarwa, shi kuma marigayi Alhaji Na-Alhaji Azare aka zabe shi Mataimakinsa. A lokacin na jagoranci Sallar Azahar suka bi ni baki daya. Muka shirya wa’azi na kasa baki dayanmu a garin Bauchi.
Da muka fara tafiya sai suka ce su fa aikin nan da muke yi ya yi musu yawa, a ce a tashi daga wa’azi da daddare da safe a zo a yi taro daga nan a fita wajen wa’azi sannan kuma kowane mako biyu a je a yi wa’azi. Suka ce wannan ya yi musu yawa. Don haka suna son a koma da yin wa’azi wata-wata mu kuma mutanenmu sun saba zuwa wa’azi a duk mako biyu. Suka ce su a koma yin wa’azin ma duk mako tunda mutane sun karu. Sai na kawo shawarar a rika yin wa’azi a duk bayan makonni uku kada mu jira har wata guda kamar yadda suka ce, kuma kada mu ce za mu rika yi a duk mako kamar yadda mutanenmu suka ce. Mu nemi tsakiya mu rika yi bayan mako uku-uku, sai aka yarda da haka.
Bayan mun fara tafiya sai ga wani abu yana fitowa, ya kamata duk abin da za a yi a rika yin shawara kafin a fitar da shi. Sai muka gani a jarida ana cewa kungiyar Izala ta noma gona hekta dubu kuma za ta taimaka ne wa makarantun tsangaya ta almajirai aka buga a jarida. Da aka zo taro na ce wane ne ya fadi wannan magana kuma a ina aka yi ta kuma ina muke da wannan gona? Sai suka ce don Allah mu yi hakuri sun yi ne kamar farfaganda. Sai na ce mu a tsarin wa’azinmu