Abin da ya sa ba mu halarci taron yaki da ta’addanci na Abuja ba – Sheikh Jingir

na Izala, gaskiya muke fada babu ruwanmu da farfaganda ko kuma fadin abin da ba shi ne ba. Bayan haka kuma sai muka ji an sake fadin cewa Izala ta kafa gidan talabijin mai suna Sunnah Tb alhalin ba na Izala ba ne, na wani mutumin Jamhuriyyar Benin ne. Muka ce yaya kuke fadar magana […]

Abin da ya sa ba mu halarci taron yaki da ta’addanci na Abuja ba – Sheikh Jingir
Abin da ya sa ba mu halarci taron yaki da ta’addanci na Abuja ba – Sheikh Jingir

na Izala, gaskiya muke fada babu ruwanmu da farfaganda ko kuma fadin abin da ba shi ne ba. Bayan haka kuma sai muka ji an sake fadin cewa Izala ta kafa gidan talabijin mai suna Sunnah Tb alhalin ba na Izala ba ne, na wani mutumin Jamhuriyyar Benin ne. Muka ce yaya kuke fadar magana wadda babu ita? Mai wa’azi ba ya karya, ba ya yaudara duk abin da za mu yi ya zamo gaskiya ne.
Daga  nan sai suka daina zuwa taro suka daina zuwa wa’azi. Suka yi ta yin maganganu marasa dadi suka rika cewa ai asalin kungiyar Izala ba marigayi Isma’ila Idris ne ya kafa ta ba. Haka aka ci gaba da tafiya idan muka sanya wani aiki su ma sai su je su sanya wani irinsa a wani waje daban. karshe har aka zo muka shiga wasu abubuwa na damuwa a Najeriya aka rika amfani da sunan addini ana kawo cikas a kasa. Muna cewa an dame mu da zalunci a Najeriya muna da tuhuma kan maganar Boko Haram, muna zargin cewa gwamnatin baya a lokacin tana da hannu kan maganar Boko Haram. Su kuma sai suna cewa yaya za a yi a zabi mutumin da Shugaban Jam’iyyarsa ba Musulmi ba, Mataimakinsa ba Musulmi ba? Saboda haka yana tsakanin wadanda ba Musulmi ba mutum biyu. Mu kuma muna cewa ai wanda ke jagorancin shugabanci da shi ake la’akari muka kwana da su a wannan.
Sai ga shi kuma ana cewa akwai sunayen wasu kamfanoni da aka gano suna cikin badakalar cin kudaden sayo makaman yaki da Boko Haram da ake tuhumar tsohon mai bai wa tsohon Shugaban kasa Shawara kan Harkokin Tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, ana zargin akwai hannayensu a cikin wadanda suka karbi kudaden. Kan wannan al’amari sai kowa yana kokarin fitar da kansa ko yaya zai yi ya binne laifinsa, ta hanyar wata siyasa ko wata farfaganda.
Mu da muka ce ku zo mu tafi suka zama sun ki zuwa, mun yi duk yadda za a yi amma sunki zuwa. Shi ke nan sai muka ji bayan mun yi taron kaddamar da Gidauniyar Raya Ilimi da Ilimantarwa a Abuja a kwanakin baya wanda ya samu halartar manyan malamai daga ko’ina a kasar nan, sai suka ware Sheikh Alhassan Sa’eed  Adam Jos da Sheikh Yakubu Musa Katsina suna jan su kan hanyar da ba ta dace ba, don suna ganinsu yara ne. Suka zo suka ce za su yi wani taro wanda za a zauna da ’yan darikun Tijjaniya da kadiriyya. To mu da muka taho addinin Musulunci muke koyarwa tsatsa, Musulunci ya nuna addinin Yahudanci daban addinin Musulunci daban haka kuma ya nuna addinin Kiristanci daban addinin Musulunci daban. Ya nuna tauhidi ya nuna littafin Alkur’ani zance Allah ne. Idan aka zo aka samu wani ya ce ga darikarsa ya kwatanta Alkur’ani da zancen wani taliki to Izala daban shi daban.
Muna cikin wannan hali sai aka zo aka ba da sanarwa cewa Rabidatul Alamil za ta shirya wani taro tare da su wato sun biyo ta karkashinsu saboda wala’alla, idan hukumomin Najeriya suka ga da su aka shirya wannan taro, wancan bincike da ake yi kan badakalar kudaden sayo makamai su samu sassauci.
To, ka ga ni na kira ka na ce zo mu yi abu kaza, ka ki zuwa kai kuma ka kama abinka babu inda muka yi wani zama da kai ka ce ka shirya taro ba ka gan ni ba. Ka ga wannan magana ko kama ba ta yi ba. Domin mu muna wa’azi ne na tauhidi muna karantar da ’ya dariku muna karantar da ’yan Shi’a muna karantar da wadanda ba Musulmi ba. A kan tsari na zaman lafiya da kwanciyar hankali ba zagi, ba duka, ba tare wa kowa hanya, ba kulla wa wani shirri don bambancin addini ko bambancin akida. Don haka idan ka ga ba ka ganmu a wajen wannan taro ba, mu babu wata gayyata da za a ce damu aka shirya wannan taro. A wannan ranar mun tafi garin Gumi ne gudanar da karatun wa’azi na kasa. Kuma ko a karin magana ana cewa bikin magaji ba ya hana na magajiya.

Aminiya: A baya-bayan nan wata kungiyar ’yan Shi’a da ke kasar Ingila ta kai karar wadansu mutane cewa suna da hannu a kisan da aka yi wa ‘yan Shi’a a Zariya. Abin mamaki sai aka ga sunanka da sunan mataimakinka da wasu sarakuna har da su Sheikh Bala Lau, shin kafin wannan kungiya ta kai wannan kara ko ta tuntube ku don jin naku bahasin?
Sheikh Jingir: A gaskiya babu wata tuntuba da na samu kan wannan al’amari kuma ba na tunanin cewa zan samu wata tuntuba kansa. Domin babu wani abu da ya hada ni da ’yan Shi’a da har muka yi wata arangama a ko’ina cikin duniya. Kuma a iya masaniyata ban san wani daga cikin mutanen da suka kai wa ’yan Shi’a hari ba. Iyaka dai na san ’yan Shi’a sun yi tashen abubuwa marasa dadi a Najeriya. Domin suna tare manyan hanyoyi suna tafiya a kafa kuma na ji an ce har sun tare Babban Hafsan Sojan Najeriya Janar Tukur Buratai a kan hanya sun kai masa hari. Kuma ba na jin a wannan al’amari da ya faru akwai wasu sarakuna ko wasu malaman addinin Musulunci.

Aminiya: Ba ka ganin ko don irin wa’azin da kuke yi na sukar akidarsu ne ya sanya suka sanya ku a cikin wadannan mutane da suka kai kara?
Sheikh Jingir: Watakila ba zai rasa nasaba da hakan ba. Amma ai ka ga ni lokacin da aka kewayemu a Masallacin Idi aka yi ta harbinmu, ban san wani da ya kawo mini wannan hari ba, sai Kiristocin da na gane wa idanuna a lokacin. Don haka da na tashi rubuta bayani su ne na aika da sunayensu har Majalisar dinkin Duniya. Duk da na san ’yan dariku suna zaginmu na san ’yan Shi’a suna zaginmu na san Kiristoci suna zaginmu, amma wannan bai hana kowa ya yi wa’azinsa ya fadi manufarsa tunda akwai ’yancin bayyana ra’ayi.

Aminiya: karshe wane sako ne kake da shi zuwa ga ’ya’yan wannan kungiya?
Sheikh Jingir: Sakon shi ne wanda muka saba fada, jama’ar Musulmi mu riki karatu duk abin da za mu yi mu yi shi da ilimi. Abu na gaba duk wanda yake son ya ci ribar duniya da Lahira ya rike gaskiya da amana da cika alkawari. Na uku mu zamanto masu da’a ga shugabanninmu da dukkan na gaba da mu kan ka’idar shari’a kuma mu tausaya wa na baya da mu. Kuma ina kira ga jama’ar kasar nan baki daya mu rika yi wa kasarmu addu’ar alheri.