Abin da ya sa ba mu murkushe ’yan Biyafara ba – Ministan Tsaro
Ga shi kun zo taron Majalisar dinkin Duniya kuma Shugaba Buhari da kuka rufa wa baya ya yi jawabi yaya ka saurari jawabin? Alhamdulillah, kamar dai yadda rahotanni suke nunawa hatta Sakataren Majalisar dinkin Duniya ya yaba wa shugaban namu domin ya nuna cewa jawabinsa tamkar matsayin shugaban Afirka ne baki daya ba na […]
Ga shi kun zo taron Majalisar dinkin Duniya kuma Shugaba Buhari da kuka rufa wa baya ya yi jawabi yaya ka saurari jawabin?
Alhamdulillah, kamar dai yadda rahotanni suke nunawa hatta Sakataren Majalisar dinkin Duniya ya yaba wa shugaban namu domin ya nuna cewa jawabinsa tamkar matsayin shugaban Afirka ne baki daya ba na Najeriya ba, musamman a kan kalamansa kan rikicin Koriya ta Arewa da sauran rikice-rikicen kasashen duniya.
A ciki jawabinsa ya yi wa Amurka da Majalisar dinkin Duniya godiya kan taimakon da Najeriya ke samun ta fannin tsaro, wane taimako kuke samu daga gare su?
To ka san taimako iri-iri ne, ko ta fatar baki ma mutum ya nuna damuwarsa a kan abubuwa da suke damunka wannan ma taimako ne, domin zai kara maka kwarin gwiwa. Kuma kada ka manta kwanakin baya Kwamitin Sullhu na Majalisar dinkin Duniya ya zagaya kasashen yakin Tafkin Chadi wato Najeriya da Nijar da Chad da Kamaru, domin gane wa idonsa abin da ke faruwa da matsalolin ’yan gudun hijirar Boko Haram da sauran abubuwan da suke damun jama’ar yankin. Shi ma wannan wani abin godiya ne domin majalisar ta nuna ta damu da abin da yake faruwa a wannan gefe namu.
An ce kasar Jordan ta bai wa Najeriya gudunmawar makamai ciki har da jiragen yaki shin ina gaskiyar wannan batu?
kwarai gaskiya ne, kamar wata shida da suka wuce, Shugaban kasar Jordan ya yi wa kasarmu albishir cewa za su ba mu makaman da suke amfani da su da wadanda suka yi musu yawa kuma yanzu ba su amfani da su har ma da jiragen yaki duk ya ce za su gyara su, su ba mu. Ka san sun yi yaki a da to amma da yake an daina yakin kuma suna da su da yawa shi ya sa suka ce za su ba mu wasu daga cikinsu. Wannan ya nuna suna damuwa da abin da ke damun yankinmu na Tafkin Chadi, musamman fadan da muke yi da Boko Haram. Ba ya ga kasar Jordan akwai kasashe da dama da suka yi mana irin wannan alkawari, amma shi Allah Ya ba shi ikon cika nasa alkawarin, don haka muna gode masa da sauran wadanda suka yi alkawarin. Ba Jordan kadai ba, Saudiyya ma ta yi alkawarin za ta taimaka mana da makamai haka wasu kasashe, kuma muna fata nan ba da jimawa ba kasashen za su cika wadannan alkawurra.
Kafin ku taso zuwa nan kun baro batun kungiyar IPOB ta kabilar Ibo wadda aka ayyana ta da kungiyar ’yan ta’adda, shin me gwamnatin Najeriya ke yi domin dakile ayyukan ire-iren wadannan kungiyoyi?
To yanzu lokacin siyasa ana yawan samun ire-iren wadannan, ba ka hana ire-irensu, sai dai na su waddnnan masu kalaman nuna kiyayya ga jama’a, dama Mataimakin Shugaban kasa ya ce ire-irensu za a sanya su a jerin kungiyoyin ’yan ta’adda masu ta da kayar baya kamar Boko Haram. Shi ya sa su wadannan da aka ga sun ci gaba da ire-iren wadannan surutai, sai sojoji suka duba suka ce su ma sun fada cikin rukunin masu ta da kayar baya kamar Boko Haram. Wannan ya sa Ministan Shari’a ya tafi kotu da wannan batu, kuma kotu ta saurare shi, ta ce ba shakka wannan kungiya ta IPOB ta fada cikin na ’yan ta’adda.
Tunda ta tabbata ta ’yan ta’adda, me gwamnati za ta yi don dakile ta kada a zo a yi wata Boko Haram?
Kamar yadda na fada ne a baya, lokacin siyasa akwai abin da ake cewa da Ingilishi Rule of Law,wato ba za a gudanar da abubuwa kara-zube ba, tilas ne sai an bi abin da dokar kasa ta tanada, don haka muna a kai. Ka san an kai shugabansu kotu kuma an ba da belinsa don haka muna jiran belinsa ya kare, sai gwamnati ta san mataki na gaba game da shi, daga bisani a kai ga magoya bayansa. Amma kamar yadda na ce, lokaci ne na siyasa, wasu abubuwan ba dole ne a bi su yadda ya kamata ba, kowa yana da ’yancin ya yi magana, amma ’yancin kowa akwai inda ya tsaya. ’Yancinka zai tsaya ne a inda ba za ka takura wa wadansu ba. Don haka ire-iren wadannan abubuwa koyaushe ana duba su cikin fahimta da hikima kafin a dauki mataki.
A baya kun ce an kawo karshen Boko Haram, sai daidaikunsu ne suka rage, amma a iya cewa wannan batu ya wuce haka domin a ’yan kwanakin nan sun kai hari a Borno sun kashe mutum 15, me ake ciki ?
Abin da mutane ba su gane ba, shi ne wadannan mutanen a wani lokaci can baya suna kame da jihohi ne, har aka dawo suka koma kananan hukumomi, yau aka koma suna wani dan gefe kadan. Abu ne wanda ba za ka ce za a shawo karshensa a rana guda ba, kada ka manta wadannan mutanen akwai su a cikin jama’a, shi ya sa muke cewa kowane lokaci jama’a su rika ba da rahoton bakin fuska ko wani abu da suke tuhuma. Domin wannan ba kamar yakin gari da gari ba ne ko ga ni, ga ka, wannan ya kawo hari wancan ya kawo a yi a gama. Sam, wannan ba haka yake ba, don haka zai dan dauki lokaci. A yanzu ba su iya hada karfi da karfe kamar yadda suke yi a baya su yi jerin gwanon motoci 10 zuwa 20 su dumfari wani wuri su yi abin da suke so. Yanzu sai dai su yi kwanton bauna ko sari-ka-noke, wanda ba abu ne da za a yi maganinsa nan take ba. Kuma kana gani ko kwanan nan sojojin sama sun je sun yi ta banka musu wuta insha Allahu nan ba da dadewa ba da taimakon addo’in ’yan Najeriya za a kawo karshen abin gaba daya.
Akwai maganar Najeriya za ta sayi makamai daga Rasha, kuma Amurka ma ta ce za ta sayar muku da makamai akwai rashin jittuwa tsakanin Amurka da Rasha, wannan ba zai shafi dangantakarku da Amurka ba?
Duk yakin da aka yi a Najeriya, ba wuri guda muke sayen makamanmu ba, muna saye a Rasha muna saye a Amurka, kuma ba mu riga mun saya daga Amurka ba, amma Rasha har ta kawo mana wasu jiragen helikwafta, kuma mun sake cewa su kawo mana wasu jirage 10. Amma ita Amurka ta yi alkawari cewa za ta sayar mana ne amm ba mu riga mun saya ba.
Wadanne irin jirage ne?
Masu saukar ungulu, akwai masu farfela wadanda na yaki ne tsantsa.
Me za ka ce game da dangatakar Amurka da Najeriya ganin canjin shugabanci da aka samu a nan Amurka?
Alhamdulillahi, ba laifi kana gani Shugaban Amurka kullum yana yaba abubuwan da Najeriya ke yi, kuma ka ga a baya takunkumin hana sayar mana makamai yanzu an dage wannan haramci kuma kullum dangataka a tsakaninmu tana kara kyau.
Kana nufin ba abin da ya canja a tsakanin wannan gwamnati da wadda ta shude?
Akwai, domin ka ga lokacin zuwa Donald Trump, ya ce mu sayi duk makaman da muke so, amma shi Obama an sa mana takunkumi an hana mu sayen makamai, yanzu muna cikin shirin sayen makamai daga Amurka.
’Yan Najeriya na ta kiraye-kirayen Shugaba Buhari ya yi wa Majalisar Ministocinsa garanbawul, ina hankali ya karkata game da wadannan kiraye-kiraye?
To ai ka san ra’ayi ne na siyasa kullum kowa yana da ’yancin fadin albarkacin bakinsa, shi dai shi ake yi wa aiki kuma ya san wanda ya yi daidai, ya san wanda bai yi daidai ba. Wani ya ce ga abin da za a yi wannan ra’ayinsa ne kuma yana da ’yancin fadin albarkacin bakinsa, Shugabanmu mutun ne mai kamanta gaskiya.