‘Abin da ya sa ba mu nada kwamishinoni ba
’Rashin kudi ne ya hana nada kwamishinoni a Bauchi – Yakubu Muhammed A Jihar Bauchi wadda daya ce daga cikin jihohin da suka gaza nada kwamishinonin, AlhajI Yakubu Ibn Muhammed Babban Mai tallafa wa Gwamnan Jihar, Barista Mohammed Abubakar kan Harkokin Watsa Labarai da Sadarwa, ya ce rashin kudi ne ya hana nada kwamishinonin. “Abin […]

’Rashin kudi ne ya hana nada kwamishinoni a Bauchi – Yakubu Muhammed
A Jihar Bauchi wadda daya ce daga cikin jihohin da suka gaza nada kwamishinonin, AlhajI Yakubu Ibn Muhammed Babban Mai tallafa wa Gwamnan Jihar, Barista Mohammed Abubakar kan Harkokin Watsa Labarai da Sadarwa, ya ce rashin kudi ne ya hana nada kwamishinonin. “Abin da ya sa Mai girma Gwamna bai nada kwamishinoni ba tun zuwansa karagar mulki a ranar 29 ga Mayun, 2015 shi ne ya samu aljihun gwamnatin jihar babu ko sisin kwabo sakamakon yadda tsohuwar gwamnatin jihar ta yi kaca-kaca da dukiyar al’umma. Kuma lokacin da Gwamna ya karbi mulki ya gaji bashin albashi na wata hudu, jihar na fama da rashin ruwan famfo da dimbin matsaloli. Gwamna Abubakar ya fi kowa sanin muhimmancin kwamishinoni domin ya yi kwamishina sau biyu a jihar ban da sauran mukaman da ya rike.”
Ya ce: “Gwamna ya fadi a lokuta da dama cewa ba ya son nada kwamishinan jeka-na -yi-ka, mutanen kirki yake son nadawa masu gaskiya da rikon amana wadanda za su yi aiki sosai domin ciyar da jihar gaba,” inji shi. Ya ce, In Allah Ya yarda nan da sabuwar shekara ko kafin ta za a bayyana sunayen sababbin kwaminonin kuma suna fata wadanda za a nada za su dage sosai wajen yi wa jama’a aiki, domin duk wanda yake tunanin za a ba shi kwamishina ne domin tara abin duniya to yana yaudarar kansa ne.
Yakubu Ibn Mohammed ya ce tunda ake gwamnati a Jihar Bauchi ba a taba samun gwamnatin da ta samu dimbin matsaloli kamar gwamnatin Barista Abubakar ba, kusan komai ya lalace. Don haka ya toshe dukkan hanyoyin da ake cuwa-cuwa da kudin jama’a domin ta haka ne zai samu kudin da zai shimfida ayyukan alheri ga talakawan da suka zabe shi. Kuma toshen hanyoyin ya sa gwamnati ta fara samun kudin da take gudanar da wasu manyan ayyukan raya kasa, yanzu haka a cikin gari an yi ban kwana da matsalar ruwan famfo kullum sai an kawo ruwa. Ya ce tsohuwar gwamnati ta rika ba wadansu mutane kudi haka kawai ba sa aikin komai, kuma gwamnatin Barista Abubakar ba za ta rika daukar kudi haka kawai tana raba wa ga wasu mutane ’yan tsiraru ba.
Da wakilinmu ya tuntubi Alhaji Sunusi Baban Takko, Barayan Bauchi, kuma jigo a Jam’iyyar PDP mai adawa a jihar, ya ce duk da gwamnatin APC ta gaji wasu matsaloli, amma yana ganin ya kamata a nada kwamishinoni a jihar domin suna da matukar amfani a siyasance. Ya ce jami’an gwamnatin jihar ya kamata su ba da amsa me ya sa har yanzu ba su nada kwamishinoni ba tun zuwan gwamnatin kusan wata shida.
Barayan na Bauchi ya ce a yanzu sun ba gwamnatin jihar zuwa sabuwar shekarar 2016 ne watakila abubuwa su sauya. “Amma bayan shekara biyu babu abin da gwamnatin APC za ta fada mana mu yarda sai mun gani a kasa da gaske ne za a yi gyare-gyare kamar yadda suke fada a kafafen watsa labarai, ko a’a,” inji shi.
Ya bukaci Gwamna Abubakar idan zai nada kwamishinoni ya nada wadanda ake ganin za su ba da gudunmawa da ’yan siyasa koda ba daga APC suka fito ba, kuma ya kamata ya fahimci cewa ba ’yan APC ne kawai suka zabe shi Gwamna ba don haka ya kamata ya dama da kowa.