Abin da ya sa ba na goyon bayan taron kasa – Sanata Gamawa

Sanata Babayo Garba Gamawa daga Bauchi ta Arewa na cikin sanatocin da ke bayyana ra’ayoyinsu kan lamuran kasa ba tare da shakka ba, wakilinmu ya tattauna da shi a garin Gamawa lokacin da ya karbi kayan tallafi da Hukumar NEMA ta kai don raba wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a bara. Ya yi bayani […]

Abin da ya sa ba na goyon bayan taron kasa – Sanata Gamawa

Sanata Babayo Garba Gamawa daga Bauchi ta Arewa na cikin sanatocin da ke bayyana ra’ayoyinsu kan lamuran kasa ba tare da shakka ba, wakilinmu ya tattauna da shi a garin Gamawa lokacin da ya karbi kayan tallafi da Hukumar NEMA ta kai don raba wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a bara. Ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi siyasa da zamantakewa da kuma taron kasa da ake shirin gudanarwa:

Aminiya: Yallabai, an fara shirin yadda za a tura wakilai zuwa taron kasa, mene ne ra’ayinka game da yadda ake samun rarrbuwa a Arewa kan taron?
Sanata Gamawa: Taron kasa na sha fada ba na goyon bayansa, saboda ni wakilin jama’a ne kuma kuri’arsu ta kawo ni kan wannan kujera, don haka ba na zaton wanda aka nada a kan tebur zai je wannan taron ya yi abin da ba mu yi ba. A zatona taron ba zai yi wani tasiri fiye da wanda majalisu za su yi ba. Don haka muna gudun rarrabuwa ko kawo cikas ga hadin kan kasa. Kullum addu’armu ita ce a yi abin da zai inganta rayuwar mutanen da suka zabe mu, ya zamanto an fita daga cikin halin rashin aiki da rashin tsaro da ake fama da shi a kasar nan. Haka muna rokon Allah a shiga harkar siyasa lafiya a gudanar da zabubbuka lafiya ba tare da samun wata matsala ba, musamman ganin yadda lokacin zabbubuka ke karatowa.
Aminiya:  Akwai masu kiran ka fito ka nemi kujerar Gwamnan Jihar Bauchi, ka amsa kiran?
Sanata Gamawa: Ban amsa ba tukuna, muna kan tattaunawa, saboda ita siyasa ’yar lissafi ce da la’akari da irin goyon bayan da mutum ke da shi tare da tuntubar mutanen da suka dace tun daga sama har kasa. Don haka ni a kullum ina rokon Allah Ya hada mu da abin da ya fi alheri don samun ci gaban jama’armu, kuma duk kujerar da za mu hau idan mutanenmu ba za su amfana ba ba ma fatar hawa, kullum fatata na ga mutane sun fita cikin wahala da rashin aikin da ake fama da shi.
Aminiya: Mene ne kiranka ga jama’a game da zaben 2015?
Sanata Gamawa: Kirana shi ne mutane su zamo masu ra’ayin zabar shugaba na kwarai ba jam’iyya ba, su zabi wanda zai yi musu abin arziki kada ra’ayinsu ya tsaya kan jam’iyyu ko abin da za su samu mai karewa. Su dubi wakilai masu kyan hali da kuma ingancin wakilcin da za su yi musu su kawo musu ci gaba da yalwar arziki. Bayan haka kuma mutane su kasance masu hakuri da junansu da kuma rayuwar da suka tsinci kansu a ciki, kada su zamanto masu cin zarafin juna a siyasa da zamantakewa, su sani duk abin da muka aikata a wannan duniya za mu yi bayani gobe kiyama. Don haka mu guje wa lalata rayuwarmu domin gyara duniyar wasu.
Aminiya: Me za ka ce game da matsalolin da mutanen wannan shiyya ke fuskanta a wannan lokaci?
Sanata Gamawa: A kowane lokaci ina tausaya wa mutanen wannan mazaba tawa saboda suna cikin yankin da ake fama da wahalar rayuwa saboda rashin aikin yi da bushewar kasa idan damina ta wuce. Don haka ne ko a bara da mutane suka fuskanci matsalar ambaliyar ruwa da ta lalata musu gonaki da rusa gidaje na rubuta wa Gwamnatin Tarayya na bi sawu, kuma alhamdu lillahi wannan mako aka kawo min wannan kaya na taimako na kafa kwamiti domin rabawa da nufin za a yi adalci ta yadda ba wanda zai koka game da yadda aka rabon. Na ji dadi saosai saboda a baya ana samun irin wannan matsala amma ba abin da ake samu sai a wannan lokaci na tashi tsaye domin ganin na samo wannan tallafi ga jama’ata, mutane kuma za su amfana da yardar Allah. Ba mu taba samun tallafin Gwamnatin Tarayya kamar na wannan lokaci ba, saboda haka na sanya mutane na kwarai da nake zaton su ma masu saye a aljihunsu ne su raba wa mutane don haka nake zaton za su raba kayan yadda ya kamata don mun yi gargadi ba kayan ’yan PDP ba ne na kowane mutum ne da ruwa ya yi masa ta’adi kuma muna wakiltar kowane mutum ne.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno