Abin da ya sa ba za a yi nasarar yaki da cin-hanci a Najeriya ba – Ribadu

Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu, ya ce yaki da cin hanci da rashawa abu ne mai wahalar gaske a Najeriya. Ya ce a yanzu haka akwai shari’u daban-daban kan rashawa fiye da dubu 3 da 800 da ke jibge a kotunan kasar nan, yana mai cewa […]

Abin da ya sa ba za a yi nasarar yaki da cin-hanci a Najeriya ba – Ribadu

Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu, ya ce yaki da cin hanci da rashawa abu ne mai wahalar gaske a Najeriya. Ya ce a yanzu haka akwai shari’u daban-daban kan rashawa fiye da dubu 3 da 800 da ke jibge a kotunan kasar nan, yana mai cewa wannan adadi shi ne mafi yawa a tarihin rashawa a duniya baki daya.

Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, a yayin taron da Gidauniyar MacArthur Foundation ta shirya a Abuja. Ya kara da cewa, “Mun dauki lokaci mai tsawo muna bayyana irin hanyoyin da ya kamata a bi wajen gaggauta shari’un a duk inda muka samu dama, amma duk da haka lamarin ya faskara, baya ga makudan kudi da ake narkarwa kan lamarin.”

A cewarsa, Najeriyar ba ta yin adalci a sha’anin yaki da rashawar, duk kuwa da cewa ita ce kasa daya tilo a duniya da ta samu nasarar kwato kudaden da ’ya’yanta suka sace daga kasashen waje. Sai kuma ya bayyana shugabanni da cibiyoyi da daidaikun jama’a a matsayin kashin bayan cimma nasarar yaki da rashawa a kowace kasa. “Muddin abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata, to dole ne a ci gaba da samun tangarda a cikin tsarin,” inji shi.

Haka zalika tsohon Shugaban na EFCC, ya bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci Mai Zaman Kanta ta kasa (ICPC) da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta kasa (NOA) su kara zage damtse wajen dakushe matsalolin rashawa. Sannan ya nemi da ’yan Najeriya su zama masu gaskiya a yayin da Hukumar EFCC ke ci gaba da gurfanar da barayin gwamnati a gaban kotu.

Shi ma yayin da yake jawabi a wurin taron, Babban Sakataren Hukumar NEITI, Waziri Adio, ya ce al’ummar kasar nan ba su dauki rashawa a bakin komai ba, inda suke daukar matsalar da sauki, alhali laifi ne mai girma da kan take hakkin bil-adama. Ya ce rashawa laifin da ke kassara jin dadin al’ummar kasa, don haka wajibi ne a rika hukunta mai hannu cikinta ta yadda al’umma za su rika ganin girman laifin.

Shugaban Sashen Aikin Jarida na Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Umaru Pate ya bayyana cewa hatta satar amsa da dalibai ke yi a makarantu ana daukarsa a matsayin rashawa, kuma wani abu ne da iyaye ke dora ’ya’yansu a kai tunda farko, lamarin da yake fantsama ga sauran ma’aikatu da hukumomin kasar nan.

Wata daga cikin masu jawabi a taron, Rosemary Otohwo ta nanata cewa gidajen jaridu na taka muhimmiyar rawa kan wannan batu na yaki da rashawa a kasar nan. Sai kuma ta bukaci karin kokari daga jaridun da tabbatar da bin doka da ma dukan hanyoyin fadakawa na kasar nan wajen isar da sakon lungu da sako.

Sakataren Janar na kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Isiaka Abiola Olagunju, ya yi nuni da cewa bangaren shari’a na kasar nan na yin iyaacin kokarinsa kan shari’un cin hanci da rashawa a kasar nan, inda ya dora zargin kan akawu-akawun kotunan.