Abin da ya sa ba zan bar jam’iyyar APC ba – Tinubu

Babban jigo a jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya ce ba zai bar jam’iyyar ba duk da cewa kuwa akwai wasu kurakurai da ake tafkawa a jam’iyyar. Tsohon gwamnan jihar Legas wanda ya na daya daga cikin manyan wadanda suka goya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin fafutukar neman zaben 2015 ya fada […]

Abin da ya sa ba zan bar jam’iyyar APC ba – Tinubu

Babban jigo a jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya ce ba zai bar jam’iyyar ba duk da cewa kuwa akwai wasu kurakurai da ake tafkawa a jam’iyyar.

Tsohon gwamnan jihar Legas wanda ya na daya daga cikin manyan wadanda suka goya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin fafutukar neman zaben 2015 ya fada hakan ne a shafinsa na Twitter mai suna @AsiwajuTinubu cewa ya na nan a jam’iyyar APC wanda a cewarshi ya sha wahala wajen hada ta.
Wannan jawabin ya biyo bayan rade-radin da ake yadawa ne a kafafen yada labarai cewa Tinubu, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da wasu ‘yan jam’iyyar APC wadanda ba sa jin dadin yadda abubuwa ke gudana da kuma jam’iyyar PDP bangaren Makarfi na shirin hada wata babbar jam’iyar hadaka kafin watan maris na shekarar 2017, musamman ganin yadda zaben jihar Ondo ya gudana.
Jawaban Tinubu wadanda ya turo su a jere suna cewa: “a tafiyar mu na gyara kasa, a na shirye-shirye, sannan a gyara shirye-shiryen, sannan kuma a na kuskure sai a gyara kuskuren. Za a samu nasarori. Saboda haka, ni Asiwaju, zan ci gaba da zama mai gaskiya wajen tabbatabar da manufofin ci gaban kasa wanda shine manufar kirkiro jam’iyyar APC.
“Na sadaukar da rayuwar siyasa ta wajen cimma burina da aka samu yanzu, zuciyata tana tare da mutane sosai, sannan kuma tunani shine kafa wata tarihi mai amfani, ba wai tarwatsa wa ba.
“Wannan gwamnatin ta APC, ta jama’a ce kuma gina kasa ya na gaba da duk burin zuciyar wani mutum.
“Wannan jam’iyya ce da mu ka sha wahala tare da wasu jama’a domin a gina ta. Ba za mu bar ta ga wasu mutane ba. Miliyoyin mutane da suka yi zabe suna nan suna kallo kuma suna addu’a.”
Idan ba a manta ba, fadar shugaban kasa ta fitar da jawabi inda ta karyata rade-radin cewa akwai takun saka tsakanin shugaban kasa da Muhammadu Buhari da Tinubu a wata sanarwa da babban mataimakin shugaban kasar a harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar bayan zaben jihar Ondo.
A sanarwar “duk wata Magana a kan cewa ‘yan jam’iyyar APC da shugaban kasa na shirin watsar da Tinubu ba ta wani tushe na gaskiya. Shugaban kasa na murna da ganin yadda Tinubu ya dauki alkawarin cewa ba zai taimaka wa wata jam’iyyar ba a zaben Ondo kuma ya cika alkawarin shi.”
Wannan jawabin ya zo ne domin ya canja tunanin jama’a na cewa nasarar Rotimi Akeredolu wani babban rashi ne ga Tinubu wanda ake tunanin ya so dan takaran jam’iyyar AD Chief Olusola Oke ne ya lashe zaben.