Abin da ya sa ba zan bar sukar Jonathan ba – Obasanjo
Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce ba zai daina sukar Shugaba Goodluck Jonathan ba duk da halartar auren ’yarsa, domin batutuwan da yake sukansa a kansu sun shafi ci gaban Najeriya ne. Cif Obasanjo ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da jaridar Premium Times ta tarho a ranar Litinin, inda ya ce, “Babu […]
Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce ba zai daina sukar Shugaba Goodluck Jonathan ba duk da halartar auren ’yarsa, domin batutuwan da yake sukansa a kansu sun shafi ci gaban Najeriya ne.
Cif Obasanjo ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da jaridar Premium Times ta tarho a ranar Litinin, inda ya ce, “Babu wata kullalliya a tsakanina da shi. Ya gayyace ni aure ’yarsa, ina da lokaci na kuma je. Don haka babu batun sulhuntawa ko rashin sulhuntawa. Ku mutane ba ku da fahimta. Aure biki ne na al’ada. (Jonathan) ya gaza kuma na fadi haka balo-balo. Ba zan sassauta a kan duk wani abu da ya shafi ci gaban Najeriya ba. Idan ina da biki zan gayyace shi, idan yana da lokaci yana iya halarta.”
Cif Obasanjo ya ce, “Ku mutane ba ku fahimtar wannan al’amari. Ba ni da wata kulalliya da shi, ba ina fada da shi ba ne, amma ba zan sassauta kan muhimman al’amuran da suka shafi Najeriya ba.”
A kwanakin baya lokacin da ya gana da shugabannin matan Yarbawa, Cif Obasanjo ya caccaki Shugaba Jonathan inda ya zarge shi da almubazzarantar da kudin rarar man fetur Dala biliyan 35 da gwamnatinsa da ta Shugaba ’Yar’aduwa suka bari. Kuma ya shaida musu cewa ya bar Dala biliyan 40 a asusun ajiyar waje, sannan ’Yar’aduwa ya kara zuwa Dala biliyan 60, amma gwamnatin Jonathan ta dawo da kudin Dala biliyan 40.
“Ba na da kulli da Jonathan kuma ina jin shi ma bai kulle da ni. Ba na fada da Jonathan, abin da na sani kawai shi ne duk abin da zai kasance alheri ga Najeriya a shirye nake in mutu a kansa.”
Obasanjo dai ya sha zargin Shugaba Jonathan kan yadda yake daurewa da karfafa cin hanci da rshawa, daya daga ciki shi ne a wajen kaddamar da wani littafi don karrama tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), Mustapha Akanbi a watan Nuwamban bara, inda ya ceJonathan bai ‘taka rawar gani ba.’ Kuma ya ce a wurin taron tattalin arzikin kasar nan “na tsaka mai wuya in ma bai koma da baya ba.”
A cikin wani sabon littafinsa mai suna “My Watch” da ya sake a watan jiya Obasanjo ya yi kaca-kaca da Shugaba Jonathan inda ya bayyana shi da wanda bai damu da kasar nan ba, kuma yake gwawajewa da masu cin hanci da rashawa da miyagu.
Cif Obasanjo ya kuma ragargaji Jonathan a wata wasika mai shafi 18 da ya rubuta masa a Disamban shekarar 2013, inda a ciki ya soki salin mulkinsa da gaza cika alkawurran da ya yi wa jama’a da gaza hada kan kasa da hana cin hanci da rashawa da kuma karya alkawarinsa na yin mulki na zango daya kamar yadda ya yi alkawari, sai kuma ya zarge shi da horar da wasu makasa na musamman don fuskantar zaben bana.