“Abin Da Ya Sa Ba Zan Iya Daina Sa Hijabi Ba”

Tattauna da mata da suka yi fice a ilimin zamani kuma suna sanya hijabi.

“Abin Da Ya Sa Ba Zan Iya Daina Sa Hijabi Ba”

Hijabi

Zamani ya zo da waɗansu ke yi wa mace mai saka hijabi kallon wacce ba ta cika ba, ko kuma wacce ba ta waye ba.

Shin ko har yanzu akwai matan da suka ji suka gani kan sanya hijabi?

Albarkacin Ranar Hijabi Ta Duniya ta 2024, shirin na yau ya tattauna da waɗansu fitattun mata da suka yi fice a ilimin zamani amma kuma suna saka hijabi.

Mun tattauna kan dalilansu, mun kuma ji ta bakin malamai kan yadda hijabi yake a addinin Musulunci.

Ku biyo mu sannu a hankali.

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan