Abin da ya sa Babana bai son gaba a siyasa – Hauwa Waziri Ibrahim

Hauwa Waziri Ibrahim ’yar marigayi Shugaban Rusasshiyar Jam’iyyar GNPP, Alhaji Waziri Ibrahim ne, ta fadi dililan da suka sa mahaifinta ba ya son gaba a siyasa:Ko kin taba tambayar me mahaifinki yake nufi da siyasa ba da gaba ba?Eh, ya ce abin da yake nufi shi ne kodai ka kafa jam’iyyar siyasa, ko kuma ka […]

Abin da ya sa Babana bai son gaba a siyasa – Hauwa Waziri Ibrahim
Abin da ya sa Babana bai son gaba a siyasa – Hauwa Waziri Ibrahim

Hauwa Waziri Ibrahim ’yar marigayi Shugaban Rusasshiyar Jam’iyyar GNPP, Alhaji Waziri Ibrahim ne, ta fadi dililan da suka sa mahaifinta ba ya son gaba a siyasa:
Ko kin taba tambayar me mahaifinki yake nufi da siyasa ba da gaba ba?
Eh, ya ce abin da yake nufi shi ne kodai ka kafa jam’iyyar siyasa, ko kuma ka shiga wacce ra’ayinku ya zo daya. Sannan ka yi kamfe don neman cin zabe. Kuma ka kuduri aniyar cewa in ka ci daidai, in kuma ka fadi to kada ka dauki gaba. Sannan in ka hadu da wanda ya yi nasara ka yi murna ka gaisa da shi. Ya ce kada ka taba daukar wanda ya kayar da kai a matsayin abokin gaba, sai dai a matsayin wanda yake da sa’a. Ya kuma hori ’yan siyasa su shiga siyasa don gina kasa ba kansu ba.
 Ko ya taba gaya miki dalilin da ya sa ya nemi zama Shugaban kasa?
 Ya ce ya yi don tallafa wa kasa ta ci gaba. Domin makarantu ba kwararrun malamai ba wadatattun kujeru da tebura da ajujuwa da sauransu. Ya ce kasa na komawa baya a lokacin.
 Mene ne sharawarki ga ’yan Najeriya ganin zabe ya yi kusa?
 Mu yi addu’a don neman a yi lafiya a gama lafiya kalau, domin in mutum ya yi da kyau kansa don akwai Allah da zai yi mana hisabi. Don mulkin kasa kamar Najeriya na da wuya, saboda duk duniya ma ta shiga rudani. Amma a sani cewa mutum mugu ne don in ya wayigari lafiya, ya ci burodi ya koshi ya kori yunwa, sai ya nemi makwabcinsa da rigima. Yawancin mutane ba sa neman ci gaban jama’arsu, sai dai na kansu. Jama’a su san cewa akwai mutane na kwarai, kuma ya kamata su nemi ganin an kambama kasa don a gudu-tare-a-tsira-tare ta hanyar zamani da samar da kamfanoni da sama wa jama’a aiki. Kuma ya kamata a ce muna da kasar da kana zaune a dakinka za ka yi odar abin da kake so, amma ba kasa da ake rashin tsaro ba.
 Me za ki ce game da kamfen din bacin juna?
Ban son yin magana kan siyasa, amma ina son ’yan siyasa su yi wa jama’a aiki ba a yi ta ka-ce-na-ce-ba. Ni Musulma ce don ba na kyamar wasu addinai. Amma ba zan yi siyasa a irin wannan yanayi ba.
 Me za ki ce game da yadda duniya ke rububin zuwa kasar Dubai don ta ci gaba, amma Najeriya na rarrafe?
Da an inganta wasu hanyoyin samun kudi ta hanyar aikin gona da hako ma’adinai da mun ci gaba, amma duk an dogara ga man fetur. Kuma matatun manmu ba sa aikin da ya kamata. Me zai hana a a kai matasa waje don su koyi aiki su zo su gina kasa? Ya kamata a ce muna fitar da danyen mai da tataccen mai waje a yanzu.
 Ina mafita?
Mafita ita ce a tabbatar kullum ana gyara ba barnata kasa ba, domin na baya su ji dadi. Muna da masu ilimi kuma ya kamata a ce ’yan kasa ne ke da kamfanonin da ke gine-gine da kuma yin tituna. Amma mun zama sai baki sun zo sun yi mana duk da muna da kwalta da sauransu. Kada fa a manta in ba ka yi shiri tunda rani ba, to in damina ta fadi za ka sha wuya.
Yawancin sa’anninki da suka yi karatu a Ingila sun ki dawowa gida, me ya sa ke kika dawo?
Na dawo da dadewa don ni ’yar kasa ce. Ina son ganin na taimaka wajen gina kasata ta fi wasu da suka yi mata zarra. Amma kana toshe wannan kafa, wata na hujewa, burina shi ne Najeriya ta daukaka.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya