Abin da ya sa ban taba yin bara ba – Malam Yusuf

Malam Yusuf Musa wani wada ne mutumin garin Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda yake kasuwanci a Abuja da kuma yadda bai taba yin bara ba a rayuwansadan kasuwan wanda a bana yake da shekara 42 da haihuwa , ya ce bayan ya kammala karatun […]

Abin da ya sa ban taba yin bara ba – Malam Yusuf
Abin da ya sa ban taba yin bara ba – Malam Yusuf

Malam Yusuf Musa wani wada ne mutumin garin Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso a Jihar Kano. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda yake kasuwanci a Abuja da kuma yadda bai taba yin bara ba a rayuwansa
dan kasuwan wanda a bana yake da shekara 42 da haihuwa , ya ce bayan ya kammala karatun Islamiyya, sai ya yi nazari don tunanin wace irin sana’a ce zai yi don ya taimaki kansa da kansa domin ya tsani yin bara. Ya ce ya ga bai dace ba ya jira sai an ba shi, “duk wuya gara ni na bayar,” inji shi.
Ana cikin haka ne wasu jama’a sukai ta cewa ya kamata ya fara yin bara.
Amma ganin an ce ba maraya sai raggo, sai Malam Yusuf ya fara sayar  da kayan kwalliyar mata da suka hada da dan kunne da sarka da jan baki da hoda da jagira da dai sauransu.  Yana yawon talla a kan keken guragu a Kano.
Ya ce ’yar ribar da ya samu sai ya kara zubawa a cikin jarin da yake riritawa. Yana cikin haka sai wani kwara wanda suka hadu a Kano, ya ce masa don me yake kasuwanci, amma baya bara, sai Malam Yusuf ya ce “bana son bara don da kaskanci ce.” Sai ya ce haka ne, sai ya ba shi Naira dubu 10 ya ce ya ja jari. Ganin haka sai Malam Yusuf ya sauya sana’a, ya koma sayar da kayan masarufi a kofar gidansu da ke Unguwar Sheka da ke Birnin Kano. Daga nan ne sai ya daina yawon talla.
Ana cikin haka ne sai ya dawo birnin Tarayya Abuja a shekarar 1999.  Daga nan sai dan kasuwan ya kwashe shekaru bakwai yana sayar da woyoyin salula sabbi da katin waya da kuma takalman yara ’yan makaranta a kusa da ofishin Hukumar Ilimi a Matakin Farko (UBEC) a unguwar Area II da ke Garki.
A karshe ya ce yana da iyali (mata daya da yara hudu).