Abin da ya sa beli kyauta ke zama ‘maganar ’yan sanda’
Jama’a na zargin hannun manyan jami’an ’yan sanda a karbar kudin beli.
Jama’a na zargin hannun manyan jami’an ’yan sanda a karbar kudin beli amma hukumomin ’yan sanda na jaddada cewa beli kyauta ne.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa har yanzu ’yan sanda suna ci gaba da karbar kudi daga hannun jama’a da sunan beli a duk lokacin da suka je neman belin ’yan uwansu.
Amma Rundunar ’Yan sandan Najeriya tana yawan nanata cewa beli kyauta ne a kokarinta na magance cin hanci da rashawa a tsakanin jami’anta.
Binciken da muka gudanar ya nuna cewa dabi’ar karbar kudin beli ta yi kamari a ofisoshin ’yan sanda.
A birnin Kano, babu inda lamarin ya fi kamari irin ofishin rundunar da ke Dala. Akwai rahotannin da ke cewa jami’an ’yan sanda a wannan ofishi na Dala suna karbar kudi masu yawa daga dangi da ’yan uwan wadanda ake kamawa.
Aminiya ta samu labarin cewa matsalar ba ta tsaya kan kananan ’yan sandan ofishin ba hatta manyansu ma suna nuna ba sani-ba-sabo wajen tsuga wa mutane kudin belin na rashin imani.
Wadansu daga cikin mutanen da Aminiya ta tattauna da su da suka fuskanci irin wannan hali a wurin jami’an ’yan sandan, sun ce wani lokaci ma kamar jami’an da ke ofishin za su bugi mutum.
Malam Abubakar Kabir ya bayyana wa Aminiya cewa lokacin da ’yan sandan ofishin suka kama dansa bisa zargin yin fada da dukan wani abokinsa sai da ya biya kudi kafin ya samu belinsa.
“Fada aka yi tsakanin dana da wani yaro abokinsa. To shi dan nawa ya yi masa duka, lamarin da har ya samu raunuka, ’ya sanda suka kama shi.
“Da muka je don yin belinsa sai suka ce ba za su ba mu shi ba sai mun biya kudi. A takaice sai da na biya Naira dubu biyar kafin suka sake shi,” inji shi.
Malam Abubakar ya kara da cewa “Ina zargin ba wai kananan ’yan sanda ke karbar wannan kudi suna durawa a aljihunsu ba, ina zargin har da DPO a ciki.
“Domin lokacin da suka ce sai na biya kudin, na nemi in gana da DPO ko DCO, amma abin ya ki yiwuwa saboda sun fada min cewa wai a lokacin suna ganawa ce. Ni kuma ganin za a bata min lokaci sai na biya.”
Wata mahaifiya da ta nemi a boye sunanta ta ce an taba matsa mata sai da ta biya kudin beli a ofishin na Dala.
“Ba zan manta ba ’yata suka yi fada da wata makwabciyarmu, sai ta kai kara da aka rufe ta sai da na biya kudi kafin a sake ta,” inji ta.
Beli kyauta ne —’Yan sanda
Da Aminiya ta tuntubi Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano kan matsayin beli a dokar aikin dan sanda, sai Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya nanata cewa beli kyauta ne.
Ya ce, “Mun sha fadin wannan cewa beli kyauta ne. Kuma muna da shirye-shirye da yawa a kafafen sadarwa na jihar da muke wayar wa al’umma kai cewa belin kyauta ne.
“A yanzu har lambar waya muka bayar cewa duk wanda ya je ofishin ’yan sanda aka nemi ya biya kudin beli, to ya kira mu ya sanar da mu don daukar matakin da ya dace.
“Kuma mutane su sani cewa ko namji ko mace ana iya ba kowa belin dan uwansa matukar an san cewa idan har an nemi mutum zai dawo da shi.”
DSP Kiyawa ya kara da cewa “Laifuffuka sun kasu kashi uku, akwai kanana da matsakaita wadanda ake ba da belinsu kuma kyauta ake bayarwa.
“Akwai manyan laifuffuka irin su kisa da fyade, wadanan ba a bayar da belinsu sai a kotu. Haka idan ana zargin mutum ana iya ba shi damar ya ga ’yan uwansa ko lauyansa sai dai hakan zai auku ne gaban dan sanda don sanin abin da suke tattaunawa a kai.”
Game da ko suna samun korafi a kan tilasta wa mutane su biya kudin beli da ’yan sanda ke yi, kafin a ba su beli, sai DSP Kiyawa ya ce ba su fiye samun wannan korafi ba.
Ya ce, “A gaskiya ba sosai ba saboda mutane sun fara wayewa a kan haka. Muna da sashi da ke karbar korafe-korafe a kan aikin ’yan sanda, ba wai sai kawai a kan beli ba.
“Idan aka samu dan sanda ya ci zarafin mutum to zai kai kara kuma idan aka bincika aka samu dan sandan da laifi, za a hukunta shi daidai da laifinsa.”
Har ila yau DSP Kiyawa ya yi bayani game da matakin da suke dauka a kan haka. Ya ce, “Muna da kotu ta musamman da ake hukunta ’yan sanda.
“Akwai dan sandan ma da ya yi harbi sai da aka hukunta shi. To irin haka suna nan da yawa. Na kuma tabbata idan har aka samu dan sanda da laifin karbar kudin beli, to, shi ma za a hukunta shi.”
A Jihar Gombe ma Aminiya ta ci karo da wadansu matasa da suka bukaci a sakaya sunansu wadanda suka taba fuskantar matsala a ofisoshin ’yan sanda inda aka tsare su aka kuma tilasta musu biyan kudin beli.
‘Saura kadan a tura ni gidan yari’
Daya daga cikin matasan ya ce, fada suka taba yi da wani saboda rashin gata aka dauko masa ’yan sanda suka kama shi.
Ya ce da ake je aka tambaye shi ya yi bayani aka ce masa laifinsa karami ne amma ya yi belin kansa Naira dubu biyar ko a tura shi kotu daga can a wuce da shi gidan yari.
Shi kuma ba ya dakudin amma ganin kada a bata masa suna ya kira ’yan uwansa haka suka nemo kudi suka biya suna Allah Ya isa.
Ya ce duk yadda mutum yake da gaskiya idan ya shiga hannun ’yan sanda sai sun karbi kudi a wajensa su ce wai kudin takarda. Ya ce “Wace takarda ce za a saya har Naira dubu biyar ko dubu uku?”
A cewarsa lokacin da aka kai shi ya ga wanda saboda ’yan uwansa ba su da kudi a kan belin Naira dubu uku aka kai shi gidan fursuna.
Haka shi ma wani mai suna Mubarak Dan’asabe da Aminiya ta hadu da shi a Unguwar Bagadaza, ya ce shi kafinta ne, kuma an taba yi masa sharrin sata, da aka tashi, saboda dan talaka ne, ba a kai shi ofishin shiyya ba sai aka kai shi hedkwata wajen CID aka ce laifinsa fashi da makami ne.
Ya ce an nemi a sasanta, sai ’yan sandan suka ce a je a nemo wani abu a kawo a kashe maganar, sai ’yan uwansa suka tambaya kamar me aka ce musu Naira dubu 50.
Ya ce da suka nuna ba su da shi aka ce musu to za a kai shi gidan fursuna. Ya ce da roko da kamun kafa sai da suka kashe Naira dubu 15.
‘Rashin kudin beli ya sa aka tura ni fursuna’
Shi ma wani matashi da yake harkar shaye-shaye ya ce, wadansu yara ya gani suna fada sai ya hana su ya kore su ya doki kansu saboda kada su sake.
Ashe dayan babansa mai kudi ne, da yake a unguwarsu ne sai ya je gida ya ce ya buge shi, sai baban ya sa aka dauko ’yan sanda, wanda a dalilin haka ’yan sanda suka tura shi gidan fursuna saboda ba ya da kudin belin kansa.
A bangaren ’yan sanda Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Jami’ar Hulda da Jama’a ta Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe, SP Mary Malum amma lamarin ya faskara.