Abin da ya sa Benuwai ke da muhimmaci ga makiyaya – Sakataren Miyatti Allah
A makon da ya gabata ne Gwamnan jihar Benuwai Mista Samuel Ortum ya zargi kungiyar fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, karkashij jagorancin Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, da shirin ta da zaune tsaye a jihar a yayin da ake shirin fara aiwatar da dokar hana kiwo daga a ranar 1 ga watan Nuwamba, inda ya […]

A makon da ya gabata ne Gwamnan jihar Benuwai Mista Samuel Ortum ya zargi kungiyar fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, karkashij jagorancin Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, da shirin ta da zaune tsaye a jihar a yayin da ake shirin fara aiwatar da dokar hana kiwo daga a ranar 1 ga watan Nuwamba, inda ya bukaci jami’an tsaro su kama shugabanninta. Aminiya ta zanta da babban sakataren kungiyar Injiniya Saleh Alhassan, inda ya mai da martani a kan zargin tare da dalilin da ya sa suke ganin dokar ba za ta yi aiki ba.
Aminiya: Gwamnan jihar Benuwa ya zargi kungiyarku da shirin kaddamar da tarzoma a jihar da zarar dokarsa ta hana kiwo ta fara a watan Nuwamba, me za ka ce?
Injiniya Saleh : Wannan ba gaskiya ba ne. kungiyarmu ta Miyetti Allah Kautal Hore na nan a kan tafarkinta da aka santa da shi na bin doka da oda tare da neman hakkin da a a danne mata ta hanyar kotu, kuma a dallin hakan ne ma muka shigar da kara a babban kotun tarayya da ke Abuja na neman a bi mana kadi a kan dokar wadda aka tsara fara aiwatarwa daga watan Nuwamba. Kuma za a yi hakan ne saboda kiyayya da ake da ita a kan al’ummar makiyaya da kuma halasta yin satar shanu da aka jima ana yi masu a jhar, wadda ita ce musabbabin wasu daga cikin rigingimu da jihar ke fama da su. Kuma muna zargin cewa ya yi kurarin ne don shriritar da shari’ar da ke gudana a tsakaninmu da gwamnatinsa da muka shigar a kotu. Ya kafa wuraren tsare dabbobi 6 a jihar a karkaashin kulawar wani kwamiti da ya kirkiro don aiwatar da shirin hana yin kiwo a wuraren da suka ratsa ta yankunan makwancin ruwu na gabar kogin Benuwai, ta hanyar tsare shanu na kwana 7, sannan daga nan sai a gwanjatar da su. Wannan wata sabuwar dabara ce ta halasta satar shanu a fakaice.
Mun kalubalanci Gwamnan da ya fito da takardun bayanan tsaro na sirri da yake ikararin ya samu a kan wai makiyaya na shirin auka wa jihar, sannan idan har yana da bayanai na tsaro irin wannan mai zai hana ya mika su ga hukumomin tsaro don daukar mataki a kan lamarin tun gabanin ya auku? Bayanansa ba komai ba ne illa farfagandar batanci da yake son ya fake da shi don kawar da jama’armu daga yankunan makwancin ruwa na kogin Benuwai, wanda kadara ce da suke tinkaho da ita tun kaka da kakanni, kuma da ita ce suke tafiyar da rayuwarsu. Sannan mun kalubalanci Gwamnan da ya fito da wani mai taimaka masa (S.A) da ake kira Gana, wanda ya jima yana jagorantar ayyukan ta’addanci na kashe al’umma a jihar. Kuma muna kira ga mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umarci hukumomin tsaro su sa ido a kan take-taken gwamnan, saboda muna da yakinin cewa yana da wata aniya ta ta da zaune-tsaye, sannan muna neman al’ummarmu da ke jhar da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda a game da jajircewar gwamnan na sai ya aiwatar da dokarsa daga watan Nuwamba, duk da kasancewar maganan na kotu
Aminiya: Ba jihar Benuwai ba ce kadai ta kafa dokar hana yin kiwo, me ya sa sai a kan nata ne kawai kuke takaddama?
Maganarka haka take: Na yarda akwai irin wannan doka a jhar Ekiti, sai da abin da ya kamata a yi la’akari da shi shi ne, jhar Ekiti na bangaren kudancin Najeriya ne, ita ko jihar Benuwai a arewacin Najerya take, wadda ke da dokar damar yin kiwo a duk yankin. Wannan doka ce da aka kafa tun a 1965 da kuma 1968. Sannan sun kasance a yankunan makwancin ruwa na gabar kogin Benuwai, tun gabanin kasar nan ma ta samun ‘yancin kai. Ka ga ba za ka hada shi da na jihar Ekiti ba, wanda makiyaya sun fara zuwa yankin ne bayan fara samun matsalar sauyawar yanayi a arewacin Najeriya. Sannan irin abin da ke faruwa a Ekiti ya bambanta da na Benuwai, saboda ita Benuwai mahada ce ta makiyaya, da zara an shiga watan Nuwamba har zuwa watan Fabarairu. Ba yadda za a hana wanan abu a lokaci guda haka nan, sai dai idan fitina ce da tarzoma kake neman kawowa. Sannan idan ka duba tsarin dokar, ta nuna cewa za a ba da damar kafa gidan gona na kiwo, ba tare da sun gudanar da wasu ayyuka gabanin hakan ba.
Na farko ya kamata a tantance adadin makiyaya da ke cikin jihar, sai ka tanada filayen kafa gidajen gona, ba kawai haka nan ba ka ce makiyaya su fito su nemi izinin damar kafa gidajen gona ba, yin hakan abu ne da ba zai yiwu ba, saboda sai makiyayi ya sayi fili, ya tanada abubuwan da ake bukata a wurin , alhali a yanzu ba masu iya tafiyar da irin gidajen gonan nan idan ba tsofaffin manyan ma’aikatan gwamnati ne ba ko kuma manyan tsoffin janar na soja ba.Wannan ba abu ne mai yiwu ba, domin tamkar hana kananan manoma ne yin kiwo har sai sun mallaki motocin tarakta da sauran abubuwan da ake amfani da su a noman zamani. Mu dai muna ganin hayayyafar al’ummar Tibi ce wanda ke faruwa a sakamakon haihuwa babu tsari da ya haifar da rigimar neman karin fili ke neman dawowa a kanmu, bayan sun jima suna yi da sauran kabilun jihar.
Aminiya: Me za ka ce kan zargi da ake yi wa makiyaya na sake kunno wutar rikici a jhar Filato bayan an samu zaman lafiya a baya?
Tarzomar da ke faruwa a yankin Bassa da ke jhar a tsakaniin al’ummar Iregwe da kuma makiyaya, zan so in fadada bayaninsa watakila za a fi ganewa, a maimakon takaita shi da yawanci a ke yi. Al’umman Iregwe na fada da al’ummomi wajen 5, da suka hada da ta Rukuba da ta Birom da Anakuta, da sauran sauran kabilu da ke kewaye da su. Tarzoma na baya-bayan nan ya auku ne a sakamakon abin da wasu matasan kabilar suka yi. Abu na farko da suka yi shi ne kashe wani makiyayi. Jami’an tsaro sun kama wasu a dalilin hakan, an yi zama sasanta lamarin. Bayan nan sai suka samu wata matsalar da al’ummar Birom a kan fili, inda aka kashe wasu.
To sai kuma wasu matasan Fulani 6 da aka kashe, an binne su bayan gano gawarsu, a gaban kwamnadan sojoji da kuma D.P.O na Miyangu, to wannan shi ya kai ga hare-haren ramakon gayya da ya faru daga baya-bayan nan. Sai dai abin mamaki idan kafofin yada labarai sun tashi ba da labarinsu sai su takaita bayanin a kan abin da ya faru na baya-bayan nan, ba tare da daukar lamarin daga masominsa ba, wanda zai nuna maka cewa Iregwe kabila ce masu fada da kowa a yankin, ba makiyaya kadai ba, da ake danganta duk wani al’amarin kisa da su a yanzu.
Aminiya: Ina a ka kwana a lamarin Mambila da ke jihar Taraba?
Al’amarin jihar Taraba ya bambata da na Benuwai, kasancewar makiyayan wajen zaune suke a wuri guda, gidajen gona ne suke gudanarwa ba masu yawo ba ne, wanda hakan ya ba su damar yin karatu fiye da makiyayan ko’ina a kasar nan. Suna da manyan mutane, mutum 3 da wannan gwamnatin ta bai wa mukamai daga jihar sun fito ne daga yankin.