Abin da ya sa dan sanda ya bindige kansa da mutum biyar

An bayyana cewa rashin jituwa ce da ta ki ci, ta ki cinyewa a tsakanin wani dan sanda da matarsa ya sanya shi ya fusata ya dauki bindiga ya harbe matarsa da wadansu mutane biyar, sannan kuma ya harbe kansa.An samu rashin jituwar ne a tsakanin dan sandan mai suna Sunkanmi Ogunbiyi, mai igiya 2 […]

Abin da ya sa dan sanda ya bindige kansa da mutum biyar

An bayyana cewa rashin jituwa ce da ta ki ci, ta ki cinyewa a tsakanin wani dan sanda da matarsa ya sanya shi ya fusata ya dauki bindiga ya harbe matarsa da wadansu mutane biyar, sannan kuma ya harbe kansa.
An samu rashin jituwar ne a tsakanin dan sandan mai suna Sunkanmi Ogunbiyi, mai igiya 2 da matarsa mai suna Oluwatosin Faremi, ita ma ’yar sanda ce mai igiya 2, wacce ta yi yaji ta bar ainihin gidan da suke zaune tare da mijin  nata a garin Abeokuta ta koma gidan uwar dakinta da zama, shi kuma sai ya bi sawunta rike da bindiga  har cikin gidan ya kashe ta, ya kashe uwar dakin nata mai suna Mama Basirat da ’ya’yanta kananan yara 3, daga bisani ya harbe kansa.
 A lokacin da ya yi wannan danyen aikin akwai ’ya’yansa su biyu da suka haifa da matar tasa da suke zaune tare da sauran yara a cikin gidan, amma sun tsira daga harbin nasa, saboda bai taba su ba. Wannan al’amari ya auku ne a ranar Alhamis ta makon jiya a garin Abeokuta hedkwatar Jihar Ogun.
 Mista Saheed Afoka, wanda shi ne babban da ga Mama Basirat, ya ce ya dade yana ba mahaifiyarsa shawarar ta daina tsoma baki a kan rikicin da ke tsakanin ’yan sandan biyu, miji da mata. Ya ce, “Kamar na san abun da zai faru, na sha jan kunnen mahaifiyata ta daina tsoma baki a kan rashin jituwar da ke tsakaninsu tunda sun rabu da juna, amma ta ki yin aiki da shawarata,  wanda hakan ne ya sanya mu cikin halin bakin cikin da muke ciki a yanzu. Kafin rasuwarta, Oluwatosin Faremi, ta sha dauko ’ya’yan mijin nata tana kawo su gidan mahaifiyata, wanda mijin nata ba ya son hakan.”
Saheed Afoka, yana wannan bayanin ga ’yan jarida ne yana zubar da hawaye, a lokacin da yake zaune kusa da gadon da dansa ke kwance a asibitin da ake yi wa yaron tiyatar cire harsashi daga kafadarsa  bayan da ya tsallake rijiya da baya daga harbe-harben da dan sandan ya yi a wannan ranar.
Wani amini ga dan sandan, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce a kwanakin baya, kafin aukuwar wannan al’amari, akwai rashin jituwa a tsakanin miji da matar,  wanda ya sanya mijin rika furta cewa sai ya yi mata jina-jina. “Kuma a cikin makon jiya da suka yi rikici cewa ya yi sai ya kashe ta a duk lokacin da ya sake komawa gare ta, amma ba mu taba zaton da gaske yake yi ba. Wannan abun bakin ciki ne kwarai.” Inji shi.
Tabbatattun bayanan da wakilinmu ya jiyo sun nuna cewa, kafin wannan ranar, dan sanda Sunkanmi Ogunbiyi ya sha gargadin Mama Basirat da ta daina boye matarsa a cikin gidanta amma hakan bai yiwuwu ba, saboda kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin uwar dakin da ’yarta. Hakan ne ya yi sanadin fusatar da Sunkanmi, ya dauki bindiga ya nufi wannan gida mai lamba 67, a kan titin Akingbala a unguwar Obantoko, a garin Abeokuta, ya daidaici lokacin da matarsa za ta fito daga cikin gidan zuwa wurin aiki ya yi mata kwanton bauna ya harbe ta har lahira, ya wuce cikin gidan ya fara harbe uwar dakin matarsa Mama Basirat, sannan ya yi kan mai uwa da wabi ga kananan yaran da ke shirin zuwa makaranta a lokacin, amma bai yi irin wannan harbin ga ’ya’ya biyu da suka haifa da matar tasa ba, wadanda su ma suke shirin tafiya makaranta, sai  ya wuce ya kyale su. Sai dai an tabbatar da mutuwar wani dan okada (Achaba) da tsautsayi ya rutsa da shi.
Daga bisani bayan ya tabbatar da mutuwar matar tasa da mutane 5, sai ya sake dana bindigar ya harbe kansa, a nan take ya fadi kasa hakora na dumtsar kasa.
 Jin wannan danyen labari ke da wuya, sai Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Ogun, Mista Ikemefuna Okoye, ya gayyaci manyan jami’ansa suka rufa masa baya zuwa gidan domin gani da ido tare da jajanta wa dukkan iyalan wadanda suka rasa rayukan nasu.
Da yake tabbatar da aukuwar al’amarin, a cikin wata takardar sanarwa da Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, DSP Muyiwa Adejobi ya sanya wa hannu, Kwamishinan ’yan sandan ya ce, “A ranar Alhamis 27 ga watan Maris da misalin karfe 7 da minti 58 na safe ne Kofur na ’yan sanda Sunkanmi Ogunbiyi da ke aiki a karkashin rundunar ’yan sanda ta Jihar Ogun, ya yi amfani da bindigar da ke hannunsa wajen kashe mutane 6 har da matarsa mai suna Kofur Oluwatosin Faremi da matar da ta mallaki gidan da wata yarinya mai shekaru biyu da wadansu  yara maza biyu da kuma wadansu mutane 3 da suka samu raunukan harbin bindiga da aka yi musu magani a cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Idi Aba a Abeokuta. Bayan kashe mutane 6, Kofur Sunkanmi ya kashe kansa da wannan bindiga.”
Kwamishina Ikemefuna Okoye, ya ce rundunar ta fara yin bincike a kan wannan al’amari tare da tabbatar da yin adalci a binciken nata. Ya kuma nemi jama’a da su kalli wannan al’amari a matsayin abu mai bakanta rai da tausayi. Ya ce bai kamata jama’a su jingina wannan matsala ga ’yan sanda ba, domin a tsaye suke a kowane lokaci wajen gudanar da ayyukan tsaron lafiya da dukiyar jama’a.