Abin da ya sa faxakarwa da ilimantarwa ke da muhimmaci wajen kare hakkin abokan hulxa – NCC

Hukumar Kula Da Al’amuran Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bayyana cewa ilimantarwa da faxakarwa ga abokan hulxa suna karfafa gwiwa ga masu tu’ammali da tsare-tsaren kamfanonin sadarwa. Darakta mai kula da al’amuran abokan hulxa a Hukumar NCC, Alhaji Abdullahi Maikano ne ya bayyana hala a yayin gudanar da taron masu ruwa da tsaki a zauren […]

Abin da ya sa faxakarwa da ilimantarwa ke da muhimmaci wajen kare hakkin abokan hulxa – NCC

Hukumar Kula Da Al’amuran Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bayyana cewa ilimantarwa da faxakarwa ga abokan hulxa suna karfafa gwiwa ga masu tu’ammali da tsare-tsaren kamfanonin sadarwa.

Darakta mai kula da al’amuran abokan hulxa a Hukumar NCC, Alhaji Abdullahi Maikano ne ya bayyana hala a yayin gudanar da taron masu ruwa da tsaki a zauren taro na karamar hukumar Udenu, a ranar Alhamis ta makon jiya.

Alhaji Maikano, wanda Mukaddashin Darakta Mista Ismail Adediba ya wakilta ya bayyana cewa ilimantarwa da faxakarwa suna da matukar muhimmanci wajen bayar da kariya ga abokan hulxa. Ya kara da cewa abokin hulxa shi ne mutum mafi muhimmanci a harkar kasuwancin sadarwa, domin kuwa shi ne ke tallatawa da kuma sayen  hajar kamfanonin sadarwa, don haka ya zama wajibi a kula da bukatunsa da kyautatawa.

Ya ce zauren yana kokari ne wajen faxakarwa da ilimantar da abokan hulxa ta yadda za su ci gajiyar ayyukan kamfanonin sadarwa yadda ya kamata. Ya kara da cewa, hukumar ta zavi maudu’in da aka tattauna ne a zauren, saboda a ta yi la’akari da muhimmin abin da abokan hulxa ke bukata, domin ba su kariya, kada kamfanonin sadarwa su ha’ince su. Ta haka ne za su iya yin zavi mafi dacewa, a yayin da za su yi hulxa da kowane kamfanin sadarwa suka bukata.

Ya ce: “Hukumar NCC a matsayinta na mai kula da harkokin sadarwa ta fito da tsare-tsare domin karfafa abokan hulxa. Xaya daga cikin ririn waxannan tsare-tsare shi ne taron masu ruwa da tsaki, taron da ke haxa kamfanonin sadarwa da abokan hulxarsu, domin magance matsalolin da ke faruwa a tsakaninsu, yayin hulxa da juna.

“Hukumar ta fito da wani ingantaccen tsari wanda ke ba abokan hulxa masu tu’ammali da kayayyakin sadarwa kariya, musamman kamar sashin faxakarwa, inda abokin hulxa zai samu shawarwari ta hanyar buga waya kyauta, ta lambar 622, ko kuma ya bayyana kokarfinsa dangane da wani al’amari da ya same shi a yayin amfani da wata kafar sadarwa. Haka kuma akwai tsarin da hukumar ta samar, inda abokin hulxa zai bukaci a daina aika masa sakon tes wanda bai nema da kashin kansa ba, ta hanyar aika sako ga 2442.”

Da yake zayyana wasu tsare-tsaren da hukumar tasa ta samar ga abokan hulxa, domin su kasance suna samun ingantaccen aiki daga kamfanonin sadarwa, Alhaji Maikano ya ce hukumar ta fito da tsarin ganawa da abokan hulxa kai tsaye a duk inda suke ta hanyar kafafen sadarwa na zumunta kamar twitter da Facebook.

Haka kuma ya zayyana wasu shirye-shirye waxanda za su taimaki abokin hulxa, yadda zai fahimci dukkan harkokin kamfanin sadarwar da yake mu’amala da shi, yadda zai fahimci duk wani sabon tsari da kamfanin sadarwa ya fito da shi, tare da sanin yadda tsarin zai amfane shi..

Ya ce abu ne mai muhimmanci ga abokin hulxa a ce yana samun gamsassun bayanai dangane da abin da zai amfane shi a yayin hulxa da kamfanin sadarwa a kowane yare da yake fahimta.

A dai yayin wannan taro, Daraktan Kula Da Al’amuran Al’umma na hukumar ta NCC, Tony Ojobo ya ce an shirya taron ne da nufin tabbatar da cewa abokin hulxa ya samu gamsarwa ga abin da ya sanya na kxi wajen sayen data daga kamfanin sadarwa.

Kamar yadda Ojobo, wanda Shugaban Vangaren Hulxa da Jama’a na hukumar NCC, Reuben Mouka ya wakilta, ya ce taron zai kasance ne wata kafa ta samar da sahihiyar gudanarwar ayyukan sadarwa don biyan bukatun abokan hulxa da su hukumar sadarwa da kuma su kansu kamfanonin na sadarwa.

Taron dai ya samu halartar Jakadiyar Abokan Hulxar Kamfanonin Sadarwa, Hel Paul da Shugaban karamar Hukumar Udenu da Sarakunan Gargajiya da kamfanonin sadarwa da kungiyoyin sa-kai da kuma al’ummar garin Obollafor.