Abin da ya sa fim din China ya fi na Hausa – Fati Macijiya
Fati Musa wadda aka fi sani da lakanin ‘Macijiya’ tana daya daga cikin jarumai masu haskawa kuma tana cikin sahun ’yan wasa mata masu dimbin masoya. A hirar da ta yi da Aminiya, ta bayyana yadda ta shiga harkar, nasarorin da ta samu da kuma kalubalen da ta fuskanta. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Tarihin […]
Fati Musa wadda aka fi sani da lakanin ‘Macijiya’ tana daya daga cikin jarumai masu haskawa kuma tana cikin sahun ’yan wasa mata masu dimbin masoya. A hirar da ta yi da Aminiya, ta bayyana yadda ta shiga harkar, nasarorin da ta samu da kuma kalubalen da ta fuskanta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Tarihin rayuwata:
An haife ni a garin Minna da ke Jihar Neja. Bayan na kammala makarantar firamare ta Umar Farouk Bahago, na wuce Kwalejin Gobernment Day domin ci gaba da karatun sakandare. Har ila yau, na wuce Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Bidda, inda na kammala a shekarar 2009 da shaidar Difloma a bangaren aikin jarida.
Dalilin da ya sa na shiga harkar fim:
Kusan duk wata sana’a da ka ga mutum ya shiga, hakan ba ya rasa nasaba da sha’awarsa ga sana’ar. Harkar fim sana’a ce da nake kauna kuma nake alfahari da ita. Na fara harkar ne a shekarar 2010 da fim din ‘Macijiya’ wanda kuma da shi jama’a suke mini lakabi.
kalubalen da na fuskanta:
Alhamdulillahi, ba ka zama gwani sai ka fuskance kalubale, amma ba wasu manyan kalubale da zan ce na fuskanta tun fara wannan sana’a.
Fina-finan da na fito:
Suna da dama kwarai, amma akwai ‘Macijiya’ da ‘Mace Sai Allah’ da ‘Kishiyar Gida’ da ‘Butulu’ da ‘Hanyar Abuja’ da ‘Masu Zaman Kansu’ da ‘Ciwon Sata’ da ’Yar Mama’ da sauransu. Amma a gaskiya na fi kaunar fim din ‘Maciya’ domin shi ya fito da ni fili duniya ta san ni.
Burina:
Ko a haka Ubangiji Ya dakatar da ni, ina alfahari domin wasu na neman irin wannan damar ba su samu ba. Masu iya magana na cewa tun ran gini tun ran zane. Allah ne ke tsara maka rayuwarka amma duk halin da ka tsinci kanka, kasance mai gode wa Allah. Ina alfahari da Shi da kuma masoyana saboda su ne silar duk wata nasara da na samu ko zan samu a gaba.
Albishir ga masoyana a sabuwar shekarar 2015:
Muna da kyakkyawar fatan cewa mun shige ta a sa’a. Allah Ya yi mana jagora, Ya ba mu zaman lafiya. Ina wa masoyana albishir da cewa sabbin fina-finaina za su ci gaba da kayatar da su fiye da wadanda suka gabata. Su kasance masu hakuri da ni. Idan suka ga na fito a fim din mugunta hakan ba ya nufin cewa halina ne ba. Wannan umarni ne daga darakta, amma ba halina ba ne.
Ta’aziyata ga marigayi Rabilu Musa (dan Ibro):
A gaskiya ba zan taba mantawa da marigayin ba, mun yi aiki tare a fina-finai da dama. Mutum ne shi mai kaunar jama’a da aiki tukuru. Allah Ya jikansa da gafara.
Dalilin da ya sa kwana biyu ba a ji ni ba:
Wannan ba ya rasa nasaba da hutun da na bai wa kaina domin bai wa sabbin jarumai dama. Har ila yau, ka san jiki da jini kuma masu iya magana na cewa rai dangin goro. Amma a yanzu haka ina da sabbin fina-finai akalla guda 15 da ke gab da shiga kasuwa. Kodayake, zan dawo gadan-gadan ne a cikin watan gobe wato watan Fabrairu.
’Yan fim da na fi jin dadin aiki da su:
Ba ni da zabi. Ina jin dadin aiki da kowa da kowa. Ko sabon dan wasa ko tsoho.
kasashen da na taba ziyarta:
Na taba ziyartar kasar China, inda na je na yi aikin dora muryar Hausa ga wani fim mai suna ‘Beijing Lobe Story’ da aka fassara zuwa harshen Hausa, wanda kuma a yanzu ake sanyawa a tashar NTA Hausa. Ni ce na hau muryar Lin da a wasan. Lokacin da na je kasar sai da aka fara koya mini harshen Sinanci kuma ni ce ’yar fim daya tilo daga Najeriya da ta yi aikin hawan muryar, sauran wadanda suka yi ba jarumai ba ne.
Bambancin masana’antar fina-finan China da ta mu ta Hausa:
A gaskiya akwai saboda su suna samun goyon bayan gwamnatin kasar dari bisa dari saboda lokacin da muke aikin saka muryar sai da Mataimakin Shugaban kasar Li Yuanchao ya kawo mana ziyara. Abu na biyu shi ne masu shirya fina-finansu sun fi namu kashe kudi wajen aikin shirya fim. Har ila yau, sun fi mu ci gaba ta fuskar na’urorin zamani kamar na dauka da sarrafa hoto da sauransu.
Sana’ar da nake bayan harkar fim:
A gaskiya ina kasuwanci, ina sayar da tufafi ne.
Batun aure:
A gaskiya har yanzu a kasuwa nake, da zarar Ubangiji Ya kawo miji nagari zan yi aure domin ina da buri.