Abin da ya sa Gidauniyar Mai Goje ta ba ‘yan Jihar Yobe tallafin karatu
Ka fada mana cikakken sunanka da kuma dalilin kafa wannan gidauniyar? Sunana Dokta Mohammad Goje, ni dan asalin karamar Hukumar Gujuba ne a Buni Yadi. Na yi karatuna na digirin farko a jami’ar Maiduguri kana daga bisani gwamnati ta tura ni kasar Malaysia na yi digiri na biyu. Mene ne makasudin kafa wannan gidauniya ta […]
Ka fada mana cikakken sunanka da kuma dalilin kafa wannan gidauniyar?
Sunana Dokta Mohammad Goje, ni dan asalin karamar Hukumar Gujuba ne a Buni Yadi. Na yi karatuna na digirin farko a jami’ar Maiduguri kana daga bisani gwamnati ta tura ni kasar Malaysia na yi digiri na biyu.
Mene ne makasudin kafa wannan gidauniya ta Mai Goje foundation?
Gidauniyar mai Goje, gidauniya ce ta hadin gwiwar abokai da suka ci gajiyar karatu a kasar waje na Gwamnatin Jihar Yobe da suke da manufa daya ta mara wa kudurin gwamnati baya kan ayyukan alheri da take yi wa al’umma.
A ina da ina gidauniyar ta bayar da tallafin?
Na fara ne da garin Gujuba inda nan ne ta’addanci Boko haram ya fi kamari domin nan ne Boko Haram suka kama kuma zauna fiye da shekara biyu daga bisani suka kona garin gaba daya, bayan da zaman lafiya ya dawo mutane suka koma gidajensu duk wanda ya ga yadda garin yake a lokacin sai ya yi kuka. A lokacin iyaye ba su san ta inda za su fara ba wajen gyaran gidajensu ga batun mayar da yara makaranta. Mu kuma ganin Gwamna Ibrahim Gaidam, ya gina sabuwar hanyar shiga garin sai muka yi tunanin ragewa iyayen dawainiya ta hanyar mayar da wasu makaranta hakan ya sa muka zabo wasu yara muka fara da su.
Yaushe aka kafa wannan gidauniyar kuma ta ina take samun kudin shiga?
Mun kafa gidauniyar ce a shekarar 2015 kuma karo-karo muke yi daga duk wani membanmu sannan duk wanda yake ganin zai sa nasa gudumawar don mara wa aniyar gwamnati baya kofa a bude take.
bangaren ilimi ne kawai kuke bayar da tallafi?
Kafin mu fara bada tallafin karo karatu a jami’oi sai da muka fara kula da bangaren kiwon lafiya don a lokacin da jama’a suka koma gidajensu wannan gidauniya ta Mai Goje ce ta hada kai da ma’aikatar kiwon lafiya aka bata likitoci suka je garin Gujuba suka yi aikin jinya a bangarori dabam-daban kyauta.
Ya ya kuka nemo yaran da kuka tallafawa kuma dukansu ‘yan Gujuba ne?
Mun zakulo su ta hannun jama’a ne kuma muna nemo yara masu kwazo ne da za mu ba wa wannan tallafi na gurbin karo karatu kuma mata da matasa 20 muka fara da su. Kuma ba ‘yan Gujuba kadai ba ne har da ‘yan Gulani da Tarmuwa, kuma kafin mu ba su tallafin sai da muka biya musu kudin jarabawar shiga jami’a na Jamb, kuma muka koyar das u yadda za su yi jabawarar ba, sannan kuma bayan sun rubuta jarabawar, fiye da rabi sun samu nasara. Sai muka tura su jami’a muka dauki nauyinsu na shekara 4 har su gama.
Shin kun kafa wannan gidauniya ce don siyasa?
Mun kafa wannan gidauniyar ce don bayar da tallafi na marawa aniyar gwamnati da kuma Gwamna Gaidam na yadda take tura ‘ya’yan talakawa kasashen waje suke karatu kamar yadda a ka mana mu ma.
Ya zuwa yanzu yara nawa kuka tallafa wa?
Yara 24 ne daga garuruwan Gujuba da Gulani da Tarmuwa, amma burinmu shi ne nan gaba za mu fadada zuwa fadin Jihar Yobe baki daya.
Mene ne kiranka ga wadanda kuke tallafa wa?
Muna ja musu kunne da su tsaya su yi karatu, idan ba su yi kokari ba, ba za mu ci gaba da biya musu kudin ba domin ba a dunkule muke biyan kudin ba: shekara-shekara ne, idan muka ga kokarin mutum sai mu biya masa na shekarar gaba idan mutum ya tsaya wasa sai mu rabu da shi.
Wana kuke kashe wa?
A shekara hudun da za su yi, za mu kashe kudi fiye da naira miliyan hudu domin duk shekara kudin ya kai miliyan daya.
Baya ga bangaren kiwon lafiya da ilimi, kuna da shirin koya wa mata da marasa gata sana’oin hannu?
Muna da shirin hakan musammam matan da mazajensu suka mutu a hare-haren nan na Boko Haram. Yanzu haka akwai wata kungiyar da ta ce idan mun tashi za ta bamu goyon baya wajen yin hakan, idan kuma aka koya musu sana’a kuma a ba su kayan sana’ar da dan jari da za su fara.
A karshe mene ne sakon ka ga Gwamnatin Yobe?
Sakona bai wuce godiya domin Gwamna Ibrahim Gaidam ya mana komai, sai dai fatan ya ci gaba saboda wannan aiki da muke yi shi muke kwaikwaiya saboda abin da ya mana ne muke koya. Allah Ya biya shi, Allah kuma Ya sa duk wanda zai gaje shi ya dora kan irin wannan ayyukan alheri da yake yi.