Abin da ya sa Gwamna dankwmabo ya cire ni daga hakimi – Sale Tinka
Tsohon Hakimin Bodor da ke masarautar Funakaye a Jihar Gombe Alhaji Sale Tinka ya zargi Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo da yi masa danniya da kin biyansa bashin da yake binsa, tare da cire shi daga hakimci ba bisa ka’ida ba: Me ya hada ku da Gwamnan Gombe da kake zargi da cire […]
Tsohon Hakimin Bodor da ke masarautar Funakaye a Jihar Gombe Alhaji Sale Tinka ya zargi Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo da yi masa danniya da kin biyansa bashin da yake binsa, tare da cire shi daga hakimci ba bisa ka’ida ba:
Me ya hada ku da Gwamnan Gombe da kake zargi da cire ka daga sarauta?
Sunana Alhaji Sale Tinka, shekarata 70, kuma ni ne tsohon hakimin Bodor da ke masarautar Funakaye a Jihar Gombe wanda Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo ya cire daga sarauta.
Yaushe ka zama hakimi?
Da muna karkashin masarautar Gombe ne inda nake dagaci, amma bayan an ba mu jiha sai aka maida ni Hakimi a karkashin masarautar Funakaye a zamanin Gwamna Abubakar Hashidu. Kuma shekurata 20 ina sarautar Dagaci zuwa Hakimi, na gada ne kaka da kakanni.
Me ya sa aka cire ka?
Gwamnan Gombe kuma Talban Gombe Alhaji Ibrahim dankwambo ne ya cire ne bisa zargina da bin Jam’iyyar APC ta Shugaba Buhari maimakon tasa PDP. Abin da ya faru shi ne bayan an yi zaben Shugaban kasa an gama lafiya, PDP ta sha kaye, sai ranar zaben Gwamna aka kira ni aka ce in zo don in kashe wata rigima don kada a yi tashin hankali, sai na je na ce kada a yi tashin hankali, billahillazi abin da na fada ke nan. Sai abokan hammayyata a sarauta suka kira Shugaban karamar Hukuma na riko Alhaji Usman Ribadu da tsohon dan Majalisar Tarayya Alhaji Abubakar Abubakar (BD) suka zo da matasa dauke da makamai wadanda suka ce wa Gwamna Dankwambo sai sun kawo masa kuri’ar karamar Hukumar Funakaye ko ta halin kaka. Da zuwansu sai suka ce na zage su, suka shake min wuyan riga, suka yaga min riga a gaban fadata a gaban wani saje na ’yan sanda. Ban rama zagin ba don ban son a yi rigima a akwatin zaben kofar fada. Ina hanyar tafiya sai aka tsayar da ni a garin Jauro Chindo suka ce ana son a yi tashin hankali, nan ma na ce kada ku yi tashin hankali. Sai na tambayi jama’a na ce, don Allah jama’a akwai wanda na buga suka ce a’a, akwai wanda na ce a yi siyasar wani a bar ta wani, suka ce a’a.
Ka kai kara ga Sarkin Funkaye ko shugaban ’yan sanda?
Ban kai kararsu ba don na bar wa Allah abin da ya faru. Bayan an kwana biyu sai aka kira ni fadar Sarkin Funakaye, da na je sai aka ban takarda a gaban fadawa Sarki ya ce Gwamna ya kore ni daga sarauta.
An taba cire wani hakimi irin haka a Gombe?
An taba cire ni, wannan shi ne cire ni na biyu da aka yi. Na farko ya faru ne lokacin mulkin Gwamna Abubakar Hashidu. Dalilin shi ne ne ya ba ni aikin kwangila da fasalin irin ginin da zan yi ba tare da ya ban ko kwabo ba, kuma ba mu rubuta ba don in gina masa katanga a filinsa da ke gefen gidansa. Na yi nisa da aiki bai ba ni ko kwabo ba sai ya ce in sayar masa da gidana da ke Sabon Layi zai gina wa banki su yi haya. Domin ina kamfanin bulo da kayan aikin gine-gine na kwangila. Ina kammala katanga sai ya ce na raina shi, zai dauki mataki a kaina. Da aka zo yin aikin gyarar hanya sai na ce a taba gefen hagu, sai ya ce ya cire ni daga sarauta. Shi ma wasika aka ba ni amma ba a nada wani ba a zamanin Sarkin Funakaye marigayi ya nada wakili.
Yaya aka yi aka maida ka sarauta?
Bayan da Alhaji danjuma Goje ya ci zabe sai ya aiko Alhaji Usman Faruk ya ce in zo. Da na zo sai ya ce me ya hada ni da Hashidu ya cire ni daga sarauta. Na ce ya ba ni gini bai ban kudi ba, ya ce in sayar masa da filina na ki bayan kullum daga gonata ana kai masa madara lita 20 zuwa gidan gwamnati da zuma farar saka da ragunar layya roka guda. Ko kwabo bai taba biyana ba daga kudin gini har zuwa na kayan gonata. Da jin haka sai Alhaji danjuma Goje ya mayar da ni sarauta. In ba don ina da sarauta ba, ba wanda zai karbi kayana ya ki biya in bar shi.
Yaya alakarka da Gwamna dankwambo kafin ya cire ka daga sarauta?
Baba yake ce min, kuma ya taba ba ni takardar lambar girma ta nuna ni mutumin kirki ne. Amma abin da ya hada ni da Gwamna dankwmabo shi ne ya karbi hayar gidajena lokacin da ya zo neman zabe karo na farko, duk da wasu kabilu sun zo suna so da kudinsu a hannu daga Yola amma na hannun damansa suka roki alfarma, suka shiga gidajen don suna fuskar jama’a. Na farko a BCJ, na biyu a Herwagana Sabuwar Kwalta da na uku a Gadan Malele kwanar Gwamna Goje, haka Gwamna Ibrahim dankwambo ya shiga suka yi kamfe suka fita ba su ba ni ko sisi ba. Bayan nan mutanen Jeka-da-Fari suka nemi alfarmar in sayar musu da filina domin a gina makaranta a ciki don su daina zuwa karatun safe da yamma sai dai na safe kawai, na yarda don ci gaban jama’a ne. Sai Gwamna dankwambo wanda shi ne Talban Gombe ya buga min waya muka yi ciniki da shi Naira miliyan 20, ya ce Ali zai zo min da kudin da karfe 1:30 na dare sai ya kawo min Naira miliyan biyar ya ce da an yi zabe da mako daya zai biya ni sauran Naira 15. Da gari ya waye sai na kira lauyana da shaidu na gaya musu. Na tura wanda ya kawo kudin don ya karbo min sauran sai dai ya dawo ya ce Gwamna dankwambo ya ce na dame shi kuma zai ci mutuncina. Bayan nan sai aka turo ’yan sanda da jami’an SSS wurina, na gaya musu ba kudin kamfe ba ne, ciniki muka yi kuma lauyana ya san maganar, sai suka ce na fi shi gaskiya.
Me ya faru bayan haka?
Da na matsa a biya ni kudina sai Gwamna ya cire ni daga sarauta. Sarkin Funakaye ya aika in zo a gaban ’yan majalisa ya ce Gwamna ya cire ni daga sarauta. Ba a kira ni wani kwamiti don bincike ba kamar yadda doka ta tsara.
Me kake so Gwamna Dankwombo ya yi don ku warware cikin ruwan sanyi?
Ya biya ni cikon kudin fili Naira miliyan 15 da kudin hayan gidajena uku da aka yi kamfe da su na wata uku Naira miliyan uku, jamilla Naira miliyan 18 ke nan. Kuma ba na son sarauta a zamaninsa.
Ina kira da a cire wa masu mulki rigar kariya wadda za ta ba da dama a kai kararsu a kotu ko suna mulki ba sai sun sauka ba, kamar yadda ake yi a kasar Amurka. Gwamna Ibrahim Hassan dankwmabo in bai biya ni kudina ba da ya sauka daga mulki zan kai shi kotu.
Jaridar Aminiya ta nemi jin ta bakin Gwamnan amma an ce ba ya da jami’in yada labarai.
Ibraheem Hamza Muhammad