Abin da ya sa Gwamna Lalong zai binciki Jang – Nanle

A makon jiya ne Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya kafa kwamitin mutum 6 a karkashin jagorancin Mai shari’a Stephen Adah, domin gudanar da bincike kan tsohuwar gwamnatin jihar ta Jonah Jang. Wakilinmu ya tattauna da Daraktan Watsa Labarai da Sadarwa na Gwamnan Filato, Mista Samuel  Emmanuel Nanle, inda ya yi bayanin kan manufar […]

Abin da ya sa Gwamna Lalong zai binciki Jang – Nanle
Abin da ya sa Gwamna Lalong zai binciki Jang – Nanle

A makon jiya ne Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya kafa kwamitin mutum 6 a karkashin jagorancin Mai shari’a Stephen Adah, domin gudanar da bincike kan tsohuwar gwamnatin jihar ta Jonah Jang. Wakilinmu ya tattauna da Daraktan Watsa Labarai da Sadarwa na Gwamnan Filato, Mista Samuel  Emmanuel Nanle, inda ya yi bayanin kan manufar Gwamnan ta kafa wannan kwamiti:

Aminiya: A makon jiya Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya kafa kwamitin bincikar gwamnatin Jonah Jang me ya sa Gwamnan ya kafa kwamitin?
Nanle: Shi dai wannan kwamitin bincike da gwamna Lalong ya kafa, ya kafa ne saboda koke-koken jama’ar Jihar Filato, kan yadda gwamnatin tsohon Gwamna Jonah Jang  ta barnatar da kudaden jihar, a cikin shekara takwas da ta yi tana mulkin jihar. Domin bayan da Gwamna Lalong ya kafa kwamitin karbar mulki daga Jonah Jang  kuma kwamitin ya fitar da rahotonsa, sai aka gano cewa abubuwan da kwamitin ya gano sun sha bamban da abubuwan da abin da tsohuwar gwamnatin ta rubuta a takardun mika mulki. Misali kamar maganar kwagiloli da kayayyakin da aka sayo da basussukan da aka karbo a zamanin tsohuwar gwamnati, sun bambanta da abubuwan da suka rubuta a takardar mika mana mulki. Don haka Gwamna Lalong ya kafa kwamitin binciken ne domin gano yadda aka shigar da kudade a ma’aikatu da hukumomin jihar da yadda aka kashe kudaden a cikin shekara takwas na gwamnatin Jonah Jang.

Aminiya: Gwamnatin ta rubuta wa Hukumar EFCC ta binciki gwamnatin Jang, kuma tuni EFCC ta fara binciken, ba ku gamsu da bincikenta ba ne ya sa kuka kafa wannan kwamiti?
Nanle: Binciken EFCC kan gwamnatin Jang daban, aikin wannan kwamitin bincike da Gwamna Lalong ya kafa daban. Abubuwan da EFCC za su bincika su ne kamar maganar kudaden da Gwamnatin Tarayya ta bai wa tsohuwar gwamnatin. Idan aka ce Gwamnatin Tarayya ta bai wa Jihar Filato wasu kudade, sai aka zo aka gane cewa kudaden ba su shiga asusun gwamnatin Jihar Filato ba, sai Hukumar EFCC ta tambaya shin ina aka kai kudaden? Irin wadannan abubuwa ne hukumar EFCC za ta bincika. Shi  kuma wannan kwamiti abubuwan da ba a tura wa EFCC ba ne aka ba shi aiki, don ya yi  aikin bincike a kansu.

Aminiya: Idan kwamitin ya binciki abubuwan da ake zargi ya gano cewa gaskiya ne, wane mataki za ku dauka?
Nanle: Ka san wannan gwamnati ba ta wasa da maganar yaki da cin hanci da rashawa. Kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya riga ya fadi cewa duk wanda ya debi kudin jama’a ya dawo da su. Haka shi ma Gwamna Lalong, tun lokacin da aka zabe shi, ya ba da tabbacin cewa zai bi duk kudin da aka ce an bai wa jihar nan, don a yi mata ayyukan raya kasa amma ba a yi ba, ya tabbatar an dawo da kudin don a yi wa al’ummar Filato ayyuka, saboda wannan amana ce  aka damka masa.

Aminiya: Wadansu jami’an tsohuwar gwamnatin na cewa ana yi musu haka ne domin a rufe bakinsu, su daina yi wa gwamnatin adawa, me za ka ce kan wannan zargi?
Nanle: Wanda yake siyasa idan babu adawa, tafiyarsa  ba ta yiwuwa yadda ya kamata. Domin kai dan siyasa, dan adawa kullum kara maka kaimi yake yi kan harkokinka. Kuma duk abin da za ka yi, idan babu mai hassada ba ya ci gaba. Don haka babu ruwanmu da hana su yin adawa, abin da muka sanya a gaba shi ne kwato wa al’ummar Filato dukiyarsu da aka yi rub-da-ciki a kai.

Aminiya: Har ila yau suna  cewa tun da kuka karbi mulkin jihar har yanzu ba ku yi komai ba?
Nanle: Wannan zancen banza ne, domin yanzu mun samu zaman lafiya a jihar nan. Ko da a kwanakin baya, wadansu ’yan tada-zaune-tsaye sun so su tayar da rikici a jihar nan, lokacin da aka kashe babban basaraken karamar Hukumar Bokkos. Idan aka lura duk wanda yake Jihar Filato, ya san an yi  sama da shekara daya, ba a samu kai hare-hare ko kashe-kashe ko tashin hankali ba. Idan ka dubi maganar biyan ma’aikatan jihar albashi, gwamnatin Lalong ta yi kokari. Domin bashin albashin ma’aikata da muka gada na wata bakwai mun gama biya. Bayan haka manyan makarantun jihar nan da aka rufe a zamanin gwamnatin baya, yanzu duk an bude su saboda mun biya musu bukatunsu. Kuma idan ka je Jami’ar Jihar da ke garin Bokkos, yanzu ana ta yin ayyuka a ciki don ganin dalibai sun ji dadin karatu. Sannan mun ci gaba da ayyukan hanyoyin da gwamnatin baya da ta faro, kamar hanyar da ta tashi daga nan Jos zuwa Marabar Jama’a. Bayan haka mun bayar da aikin sake gina Babbar Kasuwar Jos da ta kone da aikin kwangilar sake bude kamfanin kwalabe. Mun biya kudaden tallafin karatu ga daliban da ke manyan makarantu a nan gida Najeriya da kasashen waje. Idan ba dan adawa ba babu mutumin da zai ce gwamnatin Lalong ba ta yi komai ba, don haka al’ummar Filato suke yaba wa wannan gwamnati.

Aminiya: Mista Jonah Jang ya yi zargin cewa Gwamna Lalong na son amfani da sake gina Babbar Kasuwar da ka yi bayani ne, domin ya kwashe kudin Filato, ganin ya bayar da aikin tuntuba don bayar da shawara kan kamfanin da za a bai wa aikin gina kasuwar a kan Naira miliyan 250 me za ka ce?
Nanle: Ai idan da kura tana maganin zawo da ta yi wa kanta. Shi Jang da ya yi shekara 8 yana mulkin jihar, idan da aikin sake gina kasuwar hanyar kwashe kudi ne da ya yi. Mu dai kukan jama’a muke sauraro don haka jama’a ne suka ce suna son a sake gina kasuwar, kuma sake gina kasuwar na daya daga cikin alkawuran da Gwamna Lalong  ya yi lokacin da yake yakin neman zabe. Bayar da aikin sake gina kasuwar ya nuna cewa Gwamna Lalong shi mai cika alkawari ne kuma mai sauraron bukatun jama’a ne. Idan ka ga lokacin da aka sanya hannu kan wannan aiki na sake gina kasuwar Jos mutane sun yaba wa Gwamna Lalong sosai. Haka ranar da muka je zagaya kasuwar idan ka ga dubban ’yan kasuwar da suka tarbi Gwamna Lalong, ya nuna cewa jama’a sun ji dadin wannan mataki da ya dauka.