Abin da ya sa Gwamnatin Bauchi ke biyan wadanda aka yi filin jirgi kudinsu bayan shekara 38 – Baba Suleiman

Aminiya ta zanta da Darakta Janar na Hukumar Filaye da Safayo na Jihar Bauchi Alhaji Baba Abubakar Suleiman, inda ya bayyana yadda Gwamnatin jihar take biyan basussukan tsawon shekara 38: Me ya sa sai yanzu gwamnati ke biyan mutane basussuka bayan shekara 38? Wadannan mutane ne da gwamnatin Jihar Bauchi tun 1981 zuwa 1983 ta […]

Abin da ya sa Gwamnatin Bauchi ke biyan wadanda aka yi filin jirgi kudinsu bayan shekara 38 – Baba Suleiman

Alhaji Baba Abubakar Suleiman

Aminiya ta zanta da Darakta Janar na Hukumar Filaye da Safayo na Jihar Bauchi Alhaji Baba Abubakar Suleiman, inda ya bayyana yadda Gwamnatin jihar take biyan basussukan tsawon shekara 38:

Me ya sa sai yanzu gwamnati ke biyan mutane basussuka bayan shekara 38?

Wadannan mutane ne da gwamnatin Jihar Bauchi tun 1981 zuwa 1983 ta karbi filayensu domin a samar da babban filin jirgin sama na kasa da kasa a Bauchi. Tun lokacin da aka karbi filayen an samu gwamnatoci da dama da suka gabata amma Allah bai ba su ikon biyan wadannan kudade ba. Kuma bayan wancan fili da aka karba, a shekarar 2011 an sake karban wasu filayen domin fadada filin jirgin. Duk dai Allah bai nufa an biya su ba sai yanzu. A yanzu Mai girma Gwamna Muhammadu Abdullahi Abubakar ya ba da umarnin a biya su bisa yarjejeniyar za a kasa kudin kashi biyar. Yanzu Allah Ya yi an samu kashi na farko wanda ya kai kimanin Naira miliyan 55. Ana tantancewa kafin a biya su. Akwai  mutum 625 wadanda za su karbi hakkokinsu.

Kun ce za ku raba kudin kashi biyar anya masu filin za su samu wani abu mai auki kuwa?

Maimakon a raba wadannan kudade kowa a ba shi kashi biyar, sai muka lura cewa wasu kudinsu ba su da yawa, saboda mai dubu 25 ko dubu 20 ko dubu 30 in aka raba sai ka ga kudin da zai samu bai taka kara ya karya ba, saboda haka sai muka yi tunani tare da lauyansu saboda sun kai karar Gwamnatin Jihar shekara da shekaru suna shari’a a kotu, kafin muka nemi a sasanta, kuma ko ba su kai kara ba, wannan gwamnati tana da zimmar biyansu, don haka ne mu da sarakunan wadannan wurare da wakilan al’umma da lauyansu muka ce yanzu daga mai Naira dubu daya zuwa dubu 150 a yi amfani da kudin a sallame su gaba daya. Lokacin ya dade wadansu daga cikin masu filin sun rasu, shi ya sa ake biyan magadansu idan aka tantance su, kuma masu sarautu da wakilan al’umma suka tabbatar cewa wadannan magada ne in sha Allahu za a biya su.

Da yake wannan kudi ya dade ga shi ana biyan mutane kudi cikin cokali ba ku gani darajar filin ta daga a yau?

A wancan lokacin da aka karbi filin kudin da ka gani shi ne kudin da ake sayar da fili a wancan lokacin. A wancan lokacin ana sayen filin ma a Naira 30 a farashin da gwamnati take saya, wanda in ka dauka tun daga wancan lokaci a yanzu abin da ake sayen fili kowane eka shi ne Naira dubu 500. A wasu kananan hukumomi kuma za ka samu Naira dubu 300, a kwanan nan wannan gwamnati ta kara darajar fili amma a da abin da ake saya a gwamnati kowane fili kowace eka Naira dubu 60, wadanda kake gani sun samu kudi kadan din nan su ne wadanda aka karba lokacin mulkin Shagari, wato a lokacin mulkin marigayi Gwamna Tatari Ali.

Da yake kun kasa kudin gida biyar zuwa wani lokaci ke nan za ku gama biyansu?

Wannan kasa wa da aka yi,  mai girma Gwamna ya so ne a biya su kudinsu baki daya, amma saboda rashin kudi da gwamnati ke fama da shi hakan bai samu ba. Lokacin da gwamnatin nan ta karbi mulki sai da aka shekara kusan biyu da rabi kashi 26 na abin da gwamnatin baya take samu shi take samu, sannan ga ayyuka na ci gaban al’umma na hanyoyi da ake kan yi a jihar. Ka je kowace karamar hukuma a jihar nan a yanzu haka ba inda ba za ka ga kamfanonin aikin hanya ba da sauran ayyukan raya kasa. Kullum bukatar kudi ke karuwa, amma samun kudin kuma raguwa yake yi. Amma da ikon Allah ina tabbatar muku kamar yadda muka shirya, gwamnati za ta biya wadannan kudade ba tare da bata lokaci ba kamar yadda Mai girma Gwamna ya yi alkawari. Ba sonsa ba ne a biya wannan kudi sau biyar ba, yanayi da aka samu kai a ciki ne ya sanya haka. In ka duba masu filayen nan yawancinsu mutane ne masu karamin karfi, in ka biya su wani zai kara jari, wani zai ciyar da iyalansa wani kudin kuma na magada ne.

Nawa ne jimillan kudin baki daya?

Jimillar kudin ya kai sama da Naira miliyan 269.