Abin da ya sa Gwamnatin Zamfara ta samar da miloniyoyi ta hanyar Hukumar SUBEB – Jangebe

Alhaji Murtala Adamu Jangebe shi ne Shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya (SUBEB) ta Jihar Zamfara, kuma Shugaban kungiyar Shugabannin Hukumomin SUBEB na Najeriya, kuma ya taba zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara. A kwanakin baya gwamnatin jihar ta hannun hukumarsa ta bayar da kwangilar Naira biliyan 3 da miliyan 600 ga ’yan kwangila ’yan asalin […]

Abin da ya sa Gwamnatin Zamfara ta samar da miloniyoyi ta hanyar Hukumar SUBEB – Jangebe

Alhaji Murtala Adamu Jangebe shi ne Shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya (SUBEB) ta Jihar Zamfara, kuma Shugaban kungiyar Shugabannin Hukumomin SUBEB na Najeriya, kuma ya taba zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara. A kwanakin baya gwamnatin jihar ta hannun hukumarsa ta bayar da kwangilar Naira biliyan 3 da miliyan 600 ga ’yan kwangila ’yan asalin jihar su 326 domin karfafa su. A wannan tattaunawa, Jangebe ya yi bayani kan shirin kyautata wa jama’a da kokarin hukumarsa na canja fasalin ilimi domin samu ci gaba mai amfani da dorewa a jihar:

 

Ko za ka yi mana bayani kan dalilin bayar da kwangilar sama da Naira biliyan uku da rabi ga ’yan kwangilar cikin gida na Jihar Zamfara?

Gaskiya ce Gwamnatin Jihar Zamfara ta hannun Hukumar SUBEB ta samu karbar kudi daga Hukumar Ilimi Bai daya ta kasa (UBEC) don gudanar da ayyukan shekarar 2014/2015 a bara. Don haka muka fara shirye-shiryen bayar da kwangilolin aikin agaji a makarantunmu na furamare da kananan sakandare. Kudin kimanin Naira biliyan 3 da miliyan 600 ne kamar yadda ka fadi. Mun yi nazari don gano yanayin da makarantun firamare da kananan sakandare suke ciki, wadanda ke bukatar gyara ko sabuntawa a jihar baki daya. Kuma mun yi niyyar fadada makarantun ta hanyar gina ajujuwa domin rage cinkoson dalibai. Mun dauki matakan da suka kamata domin mu samu nasara a wannan shiri da muka daura niyya. 

Kimanin makarantu 114 ne za su ci gajiyar wannan shirin na agaji. Kuma za mu sayi kujeru da tebura dubu 11 da 887 don zaman yara. Kuma za mu samar da kujeru da teburan zaman malamai guda 1,456 domin kara samar da yanayin koyarwa mai kyau.

Wani muhimmin abu a wannan shiri shi ne a karo na farko a Najeriya muna duba yadda za mu kyautata sashen mulki na sakatarorin ilimi domin ya zama ingantacce. Da farko akalla za mu gina ofisoshi 10 a kananan hukumomi 10 kuma za a inganta su da na’urorin kimiyyar sadarwar (ICT), haka ma za a sanya Internet ya rika aiki na awa 24 domin sakatarorin su samu damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

’Yan kwangilarmu na gida 326 da suke zaune a yankunan da makarantun suke aka dauka domin gudanar da wannan aiki.

 

Me ya ja hankalin gwamnatin ta bayar da wannan aiki ga ’yan kwangilar gida kuma wane buri ake son a cimma a karshe?

A karshen wannan shiri muna fatan cimma abubuwa uku: Na daya samar da yanayin koyar da karatu mai kyau a makarantu, na biyu domin rage cinkoso a ajujuwa, domin a wasu lokuta akan samu yara 150 zuwa 200 a aji daya, don haka wannan shiri zai magance cinkoson. Na uku, muna son yin amfani da shirin domin mu karfafa wa ’yan kwangilarmu na gida ta yadda za a rage fatara a jihar, saboda ’yan kwangilar ’yan asalin jihar ne, da aka zabo daga ainihin wuraren da za a gudanar da gyare- gyaren.

Manufarmu ita ce mu karfafa wa mutanen domin za su samu kudaden da za su kara inganta rayuwarsu. Idan aka ce an zuba Naira biliyan uku a cikin jama’a ka san ba karamin abu ba ne, aikin zai samar da aiki ga kafintoci da masu walda da magina da sauransu, don haka muna sa ran sake dawowar Naira biliyan 15 ta wanan hanya. Domin shirin zai kunshi ma’aikatan da suke zaune a yankunan da za a yi ayyukan. ’Yan kwangila za su sayi siminti da katako da fenti da sauransu daga jama’ar yankunan, don haka shirin zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar, wannan shi ne burinmu.

Baya ga yanayin koyarwa mai kyau, me hukumarka ke yi domin inganta jin dadi da walwalar malamai?

Gwamnatin Zamfara ta bayar da fifiko ga kyautata jin dadi da walwalar malaman makarantun firamare, babu shakka a kan wannan. A wannan hukuma muna kula da walwalarsu ta fuskoki biyu. Na farko Zamfara tana daya daga cikin jihohin kasar nan da ba su taba rike albashin malamai ba ko da na wata daya ba. Akwai jihohi da dama da ake kasa biyan albashin malamai a tsayin watanni shida zuwa sama. A Zamfara muna bayar da albashi a kan kari da sauran hakkokin malamai. Sannan wata hanya ta kyautata musu ita ce ta inganta aikin malanta. Mun fahimci cewa kyautata jin dadin malamai ya wuce daukar albashi zuwa gida kawai. Gwamnati tana yin abubuwa da dama ta fuskar horar da malamai a Najeriya da wajenta a cibiyoyi masu inganci. Yanzu haka mun kulla dangantaka da shirin bunkasa rayuwar yara na Hukumar DFID, kuma mun kulla da UNICEF wadda ta samu goyon baya daga DFID.

Bugu da kari mun kulla dangantaka da Jolly Phoenid da wasu cibiyoyin bayar da horo da suka hada da JAKA wadda ke samun tallafi daga Cibiyar Malamai ta kasa (NTI), domin bunkasa yanayin koyarwa a makarantunmu.

 Baya ga wannan Zamfara ce kadai a jihohin Najeriya ke daukar nauyin malamai zuwa rangadin ilimantarwa. Kwanan nan mun dauki nauyin malamai 10 zuwa kasar Birtaniya domin halartar wani shiri na ilimantarwa daga Jolly Phoenid. Malaman da aka horar yanzu haka suna horar da wadansu malamai kan abubuwan da aka koyar da su a Ingila. A takaice malamanmu ne ke bayar da horo ga wadansu malamai a jihohin Kwara da Kaduna da Jigawa da Gombe, Taraba da sauransu a karkashin shirin ilimantarwa na Jolly Phoenid.

Kuma wannan jiha ita kadai ce jihar da malamanta na firamare suke samun kudin hutu, domin tun daga shekarar 2011 muna biyan su kudin hutu a kan lokaci. Wadannan ne hanyoyin da muke bayar da fifiko don jin dadin malaman firamare, duk da dai har yanzu ba mu samar musu da abin da muke fata ba, wato tabbatar da karin mafi karancin albashi. Abin da ya faru shi ne mun buga lissafi idan za mu kaddamar da karin albashi mafi karanci, dole mu tabbatar mun like duk wata kafa ta rashin biyan albashi. Idan muka kaddamar da tsarin kuma aka wayi gari ba mu iya biyan albashin ka ga akwai matsala don haka muka zabar musu abu mafi dacewa ba tare da rike musu albashi a karshen wata ba. Amma kuma muna kokarin tabbatar da tsarin da zarar tattalin arziki ya inganta.

 

Me gwamnati ke yi don karfafa kara sanya yara a makaranta?

Idan za ku iya tunawa a shekarar 2011 lokacin da wannan gwamnatin ta shiga ofis, mun gudanar da bita kan ilimin firamare a Zamfara, mun gudanar da bita kan sha’anin gudanar da makarantun firamare a jihar ciki har da yanayin da malamai suke ciki da dakunan karatu da koyarwa da kayan karatu da gine-gine da tsabtar makarantu da samar da ruwan sha da sauransu. Mun gudanar da wannan aiki ne don mu gano abin da ya kamata ya zama ingantacce a sha’anin bayar da ilimi a makarantun firamaren jihar. Mun fara a shekarar 2011 muka kammala a 2012, bayan kammala aikin mun gano muna da yara dubu 283,  a firamare maimakon dubu 500 zuwa dubu 600 da suka kamata a ce suna firamare. A lokacin da muka gano wannan matsalar, gwamnati ta kara kaimi a kamfe din sanya yara makaranta a Satumban 2012, inda aka umarci sarakunan gargajiya da manyan jami’an gwamnati da shugabannin siyasa su koma wajen al’ummarsu domin su himmatu sosai wajen kamfen din sanya yara makaranta domin dawo da yaran da suka kaurace wa makaranta domin su sake komawa wanda hakan ya sanya adadin lambar yaran ya karu daga dubu 283 zuwa dubu 447, a cikin wata daya kadai, bisa wannan ne adadin yara ’yan makaranta ke karuwa har zuwa yau.

Kuma a kowace shekara muna gudanar da abin da muka kira kidayar Shekara da manufar gano hakikanin adadin yaran da ke shiga makaranta. Wata hanya kuma ita ce ta kawance da muka yi a cikin shekarar 2011. Ba mu da abokan kawancen ci gaba ko guda daya a cikin jiha, amma bisa ga kokarinmu mun samu nasarar kawo UNICEF da DFID da MC Arthur Foundation. Muna da shirin da muke gabatarwa mai suna RANA wanda yake kokarin ilimantar da jama’a a cikin harshen Hausa. A yau muna da abokan hulda biyar a wannan jihar. Bankin Duniya ma zai zo domin duba matsalar yaran da suka kaurace wa makaranta. Zuwa wannan wata na Satumba za mu fara shirin bayar da kudade ga iyaye ’yan asalin jiha wadanda suke kasa daukar nauyin sanya yaransu a makaranta. Mun kira shirin da sunan shirin tallafa wa iyaye. Kuma wadanda suka amfana za su yi amfani da kudin ne wajen saya wa ’ya’yansu yunifom da kayan makaranta da litaffan karatu. Muna da tabbacin wannan shirin zai taimaka wajen kara yawan yaran da suke shiga makaranta. Kusan Naira milyan 200 za a kashe a wannan shirin tare da hadin gwiwa da Hukumar UNICEF.

 

Mu koma baya kadan, kwangilar da za a bai wa ’yan asalin jihar. Wane shiri aka yi na tabbatar da ingancin aiki bayan kammalawa?

Duk wanda yake biye da al’amura a Jihar Zamfara daga shekarar 2011 zuwa yau ya san cewa makarantunmu suna da kyakkyawan fasali da tsari idan ana maganar inganci da kyan gini. Da zarar ka shigo jihar, ba ka bukatar a gaya maka wadannan su ne makarantun gwamnati. Ginin mai kyau ne kuma mai inganci tare da fenti da rufin kwano mai kyau, mun samu wannan nasarar ce bai domin damar da aka ba mu kawai ba, a’a har da tsari mai ma’ana. Lokacin da muka shiga ofis a shekarar 2011, makarantunmu sun yi kama da na jihar da aka kammala yaki. Sun tabarbare tare da daukar hanyar lalacewa, don haka muka dauki matakin gaggawa na sake gina makarantun da lamarin ya shafa. Domin cimma wannan burin, mun zabi inganci a matsayin ma’aunin auna kwazonmu. Misali idan muka karbi Naira biliyan biyu daga Hukumar UBEC, kashi biyu daga ciki za su tafi ne ga fannin sanya idanu da duba makarantu. Hakan ba ta samu ba a gwamnatin da ta gabata inda aka rika barnatar da kudaden ba tare da amfani da su yadda ya kamata ba.

Daga cikin kaso biyu, mukan gayyato jami’an tuntuba masu zaman kansu domin su rika duba ayyukanmu. Ba wannan kadai ba, muna amfani da ma’aikatanmu domin shiga cikin aikin dubawa da sanya idanu. Ma’aikatan da ke ayyukan hannu ba biyan su muke yi ba amma saboda manbobinsu ne ke gudanar da ayyukan, a kashin kansu sukan yi aikin sanya idanu ga manbobinsu da aka bai wa aikin. Muna tuntubarsu domin tabbatar da ingancin ayyukanmu. Idan aka yi kokarin duba tsarin makarantunmu, za a ga cewa an yi musu aikin da za su kai har su shekara 30 masu zuwa. Baya ga wannan mafi yawan ’yan kwangilarmu a kan sanya su su yi rantsuwar cewa za su yi aiki mai inganci kamar yadda takardun kwangila suka nuna. Akan yi wannan ne baya ga yarjejeniyar takardun da aka sanya wa hannu tun farko. Wadannan wasu ne daga cikin hanyoyin da muke tabbatar da inganci a ayyukanmu. 

 

Yaya za ku tabbatar  ayyuka da kayan aiki da kuke samarwa an rika kula da su sosai musamman daga shugabannin makarantu da malamai da ’yan makaranta?

A bayyane yake cewa mun bayar da horo da sake bayar da horo ga shugabannin makarantu domin shugabanci abu ne mai matukar muhimmanci, tamkar abin da ake kira ‘Nuna mini makaranta mai kyau ni kuma in nuna maka shugaban makaranta.’ Za mu bayar da horo kan yadda ya kamata a kula da gini da kayan aiki da aka zuba a ciki.

Za mu ba su horo mai kyau kan yadda ya kamata su kula da wadannan ayyuka musamman a lokacin da makarantu suke lokacin hutu. Har yanzu a kan inganci, ’yan kwangilarmu za su rika amfani da kayan aiki na zamani a wadannan ayyukan musamman domin tabbatar da ingantaccen tsaro a kofofi da tagogi.

 

Yaya kake son a rika ba da labarin aikin da ka gudanar a karshen wa’adin mulkinka?

Muna da kudirori da manufofi a yayin da muka fara wannan aiki, kuma wannan bai canja ba, domin kashi 80 cikin 100 na yaran mu suna makarantun Gwamnati a halin yanzu. Don haka sai mun tabbatar da ingancin koyarwa a makarantun na gwamnatin sannan za mu iya iya cewa mun kai kaso mafi yawa na yaranmu a matakin samun ilimi tare da kauce wa matsalolin ilimi a cikin al’umma. Abin da muke yi shi ne mu samar da komai mafi kyau ga wadannan yaran. Abin da nake nufi da mafi kyau shi ne ta hanyar kara inganta sha’anin koyarwa a makarantu ta hanyar bayar da horo da sake bayar da horo. Daga bisani wadannan kwararrun malaman za su bayar da ilimi ga yaranmu. Muna son bayar da ilimi ingantacce ga yaranmu domin su yi gogayya da yara masu hazaka na duniya.

A takaice Zamfara kadai a fadin Najeriya da ta sadaukar da Cibiyar Bayar da Horo Da Ci-gaba inda malamai ke zuwa karbar horo na wata uku kan sha’anin koyarwa. Mafarkina shi ne a wayi gari makarantun kudi wato masu zaman kansu ba su da wani tasiri ga iyaye a matsayin makarantu mafiya kyau da bayar da ilimi. Daga lokacin na tabbatar na samu nasarar canja batun yadda ake ba da labarin makarantun gwamnati a Jihar Zamfara.