Abin da ya sa gwamnonin Amurka suka fasa karbar ’yan Siriya

A farkon makon nan ne wasu gwamnoni 26 a kasar Amurka suka ce ba za su amince a tsugunar da wasu ’yan gudun hijira daga kasar Siriya a jihohinsu ba.Matakin yana zuwa ne kwana biyu bayan wani mummunan harin kunar bakin wake a birnin Paris na kasar Faransa. Hakan ya sa wasu masana suke tunanin […]

Abin da ya sa gwamnonin Amurka suka fasa karbar ’yan Siriya
Abin da ya sa gwamnonin Amurka suka fasa karbar ’yan Siriya

A farkon makon nan ne wasu gwamnoni 26 a kasar Amurka suka ce ba za su amince a tsugunar da wasu ’yan gudun hijira daga kasar Siriya a jihohinsu ba.
Matakin yana zuwa ne kwana biyu bayan wani mummunan harin kunar bakin wake a birnin Paris na kasar Faransa. Hakan ya sa wasu masana suke tunanin cewa gwamnonin sun yi hakan ne saboda tsoron duk wani Musulmi dan gudun hijira. Musamman idan aka yi la’akari da wani rahoto da ya ce an tsinci fasfo din wani dan Siriya a kusa da gawar daya daga cikin maharan, wanda ya rasa ransa lokacin harin da ya yi  sanadiyyar mutuwar mutum 131 ranar Juma’ar makon jiya.
A dokokin kasar gwamnoni ba su ikon hana tsugunar da ’yan gudun hijira a jihohinsu. Kodayake, za su iya umartar jami’an da ke kula da aikace-aikace  ’yan gudun hijira a jihohi kan kada su ba gwamnatin tarayyar kasar hadin kan da ya dace.
Wasu daga cikin jihohin da gwamnoninsu suka ki amincewa su ne: Florida da Tedas da Georgia da Ohio da Massachusetts da Alabama da Michigan da Louisiana da Indiana da Mississippi da  Arizona da Illinois da North Carolina da Wisconsin da Arkansas da sauransu. Har ila yau, gwamnonin wadanda duka ’yan Jam’iyyar Republican ne adadinsu ya dara na rabin gwamnonin kasar gaba daya.