Abin da ya sa jam’iyyarmu za ta yi nasara a 2019 – Shugaban LP
Tsohon dan takarar kujerar Gwamna daga Jihar Kwara sannan shugaban Jam’’iyyar Labour (LP) na kasa, Dakta Mike Omotosho, a tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana cewa a shirye jam’iyyarasu take ta kwace mulki daga APC a 2019. Haka kuma ya tabo batutuwa da dama da suka hada da rigingimun cikin gida na jam’iyyar, wadda har kawo […]
Tsohon dan takarar kujerar Gwamna daga Jihar Kwara sannan shugaban Jam’’iyyar Labour (LP) na kasa, Dakta Mike Omotosho, a tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana cewa a shirye jam’iyyarasu take ta kwace mulki daga APC a 2019. Haka kuma ya tabo batutuwa da dama da suka hada da rigingimun cikin gida na jam’iyyar, wadda har kawo yanzu tsohon shugaban jam’iyyar na ci gaba da ikirarin cewa shi ne shugabanta, da kuma irin matakan da suke dauke a kansa. Ga yadda tattaunawar ta gudana kamar haka:
Ranka ya dade ka fara da gabatar mana kanka a takaice.
Sunana Dakta Mike Omotosho, Shugaban Jam’iyyar Labour Party na kasa.
Wannan jam’iyyar ta samu kanta cikin rigingimun cikin gida kamar yadda PDP ta samu kanta. Yanzu wane hali ake ciki?
To a halin gaskiya dai babu wata rigima a wannan jam’iyya da har za a tada hankalia kansa. Muna da tsari kuma muna bin tsarin, kwamitin gudanarwa ya zauna da dukan mambobinsa ya tsara taron zaben shugabanni, kuma jama’armu sun zo daga dukkan jihohi 36 na kasar nan, aka gudanar da zaben cikin gida, mutane suka ce sun gaji da wancan shugabanci, sannan aka zabe ni a matsayin sabon shugaban jam’iyya na kasa. Ka ga wannan a sarari yake cewa wancan shugaban ya zama tsoho, don haka muke cewa babu wata rigima. Amma dai a dukkan matakin shugabanci ba lallai ne ace kowa ya gamsu ba, amma dai ina tabbatar maka cewa babu wata fitina, kanmu hade yake.
Kasancewar har yanzu tsohon shugaban yana ayyana kansa a matsayin shugaban wannan jam’iyya. Wane mataki ke nan za ku dauka?
Ba mu dauki wannan ikrarin nasa da muhimmanci ba, domin wannan zabe an yi shi a gaban kowa, hatta ita kanta Hukumar Zabe INEC mun gayyace ta kuma ta tura wakilanta, a kan idonsu aka yi komai. Mun bi dukan ka’idojin da ya kamata mu bi, har jami’an tsaro suna nan sannan da kuma ‘yan jarida. Don haka sakamakon a fili yake kuma duniya ta dauka. Amma na yarda da kai cewa tsohon shugaban yana ikrarin har yanzu shine shugaba, amma abinda ya kawo haka shine rashin cire sunansa da INEC ba ta yi ba a shafinta Intanet, kuma mun yi mu su magana akan haka sun ce za su dauki mataki, amma har yanzu basu cire ba, kuma wannan dalilin ne ke sa shi yana surutu. Sannan kana maganar mataki, to wannan shi ne na farko, sannan kuma mun sanar da ‘yan sanda halin da ake ciki, cewa ga wani nan yana amsa sunan da ba nasa ba, wannan kuma sabawa dokar kasa ce, kuma muna da tabbacin cewa za su dauki mataki akansa, musamman ma idan ya yi gigin cewa zai shirya wani taro da sunan LP.
A halin yanzu ma dai ba ta shi muke ba tukun, mun maida hankali ne akan yadda zamu samu cigaba a wannan jam’iyya tamu, akwai gyare-gyare da muke son yi wadda wancan shugabancin ya lalata. Haka kuma ita kanta jam’iyya mai mulki ta APC akwai abubuwa da yawa ta take yi wadanda mutane basu jin dadinsu. Don haka muke son kawo babban sauyi ta yadda zamu tafi da dukkan al’umma, wannan jam’iyya ce ta kowa hatta matar dake saida tumatur ko kosai a kasuwa da sauransu. Don haka muke son bayyana wa mutane asalin yadda jam’iyyar LP ta ke da kuma kara fito da manufofinta kyawawa, sannan so mu sanya mutanen da ke da tsoron Allah a zuciyarsu a dukkan kujerun takara, domin da haka ne kawai al’umma za ta samu shugabanci nagari.
Baya ga wannan matsala ta shugabanci akwai kuma wani kalubale da za a iya cewa LP na fuskanta?
Ai wannan ba kalubale ba ne, domin zai wuce yanzu, wannan ba damuwarmu ba ce damuwarsa ce shi da ya sa kansa.Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne yadda al’umma za su fahimce mu, su gane cewa LP ce ta fi dacewa da su saboda kyawawan manufinta masu cike da gaskiya, adalci da tausayi, kuma jam’iyyar kowa ce. Sannan wani abu da yake damunmu shi ne yadda ‘yan siyasa ke shigowa su yi amfani da jam’iyyarmu idan suka rasa takara a inda suke, sannan bayan sun ci zabe su gudu su koma inda suka fito. To ba za mu sake yarda da wannan yaudara ba. Za mu tsaida ‘ya’yan jam’iyyarmu ne masu kyawawan manufofi a dukkan kujerun takara.
Amma wasu na zargin cewa jam’iyyar LP ba ta tafiya da ‘yan Arewa. Me zaka ce?
A’a wannan ba gaskiya ba ne!babu lokacin da ba mu tafiya da mutanen Arewa, kuma ai ni kaina daga Arewa ta Tsakiya nake wato Jihar Kwara, ko ni ba dan Arewa ba ne? Ni cikakken dan Arewa ne kuma haifaffen Zariya sannan a can na yi karatuna, kuma akwai ire-irena da yawa cikin wannan jam’iyya, saboda haka jam’iyyarmu ta kowa ce babu bangaranci babu kabilanci.
Wane kira zaka yi don al’umma su kara gane cewa wannan jam’iyya ta dukan jama’a ce?
To sai dai in kara, amma ita LP ai ta kowa ce, kuma muna da tasiri a siyasar Najeriya, duk da cewa bamu da gwamna, amma muna da ‘yan majalisa. Amma abin da zan ce anan shi ne, a yanzu kasar ta zama cewa muddin baka da kudi to ba zaka iya shiga siyasa ba, to mu LP muna so mu fito da hanyoyin da hatta wadanda ba su da kudi za su iya tsayawa takara. Misali, zamu baiwa matasa da mata tikitin takara kyauta, ka ga yin hakan zai janyo mana karin mutanen da ke da kishin kasa a zukatansu amma rashin kudi ya hana su taka rawa ko gwada baiwar da Allah Ya masu.
Haka kuma muna da tsarin samar da kudi ba ta hanyar attajirai ko iyayen gida ba, wadanda idan aka ci zabe ka biya su da kudin al’umma, a’a, zamu fito da dabarun tara kudi a tsakaninmu, misali a cikin mutum sama da miliyan 200 da muke da su a kasar nan, idan muka samu mutum miliyan daya kowa ya bada naira budu daya kacal, mun samu biliyan daya kenan. Kuma zamu iya tara fiye da haka, ka ga yin haka zai sa mu kaucewa siyasar ubangida, wanda ake hada kai da su ana lalata kasa. Sannan muna da tsarin nuna cewa dukkan iyali suna da muhimmanci, domin idan ka inganta iyali kamar ka inganta dukkan kasa ce,sannan nagarta da lafiyar iyali, lafiyar kasa ce,haka kuma iyalan dake dogaro da kansu su ne tattalin arzikin kasa. Don haka dai idan ka dubi manufofinmu baki daya game da walwalar jama’a ne, domin su ne kasar.
A matsayinka na sabon shugaban wannan jam’iyya, me kake shirin yi don ganin an samu nasarar da ba a samu ba a lokacin tsohon shugaban?
To babban burina shine LP ta samu nasara a babban zabe na shugaban kasa. Kuma da yardar Allah zamu samu nasarar. Domin mutane sun fara gajiya da wannan jam’iyya ta APC. Sannan yunwa ta yi wa al’umma yawa, amma ba wai muna adawa ba ne, a’a, mu a al’adarmu duk shugaban da ya yi abin kirki muna yaba masa, kuma lallai akwai inda Shugaba Buhari ya yi kokari kuma mun fadi, amma kuma dole ne mu fadi abinda kuma ba a yi ba, wannan shine adalci.
Kamar menene kuke yabawa cikin ayyukan Shugaba Buhari?
Ka ga ya fitar da Najeriya daga rugujewar tattalin arziki, wannan abin yabo ne, amma dai har yanzu mun zuba ido mu ga abubuwan da za a yi da dukiyar da aka ce mana an samu din wadda al’ummar kasar nan zasu ji dadi, amma dai yunwar ta yi yawa.
Ka ce za ku kwace mulki a 2019. Wa zak u tsayar takarar shugaban kasa ken an?
Gaskiya ba mu sani ba tukun… Wannan ita ce gaskiyar magana, amma dai muna da tabbacin za mu tsayar da mutumin kirki wanda ba zai ci amanar al’umma ba.
Daga Arewa ko Kudu?
Idan lokacin ya yi za mu bayyana. Yanzu da sauran lokaci tukun.