Abin da ya sa Jamus ke karbar ’yan ci-rani

A karshen makon jiya ne kasar Jamus ta karbi dubban ’yan gudun hijira, wadanda galibinsu Musulmi ne wadanda suka fito daga kasashen Siriya da kuma Iraki.kasar ta yi maraba da masu neman mafakan  ne bayan wasu kasashen nahiyar sun rufe iyakokinsu don hana su shiga cikin kasashensu.Kodayake, a shekaranjiya Laraba ne gwamnatin kasar ta sanar […]

Abin da ya sa Jamus ke karbar ’yan ci-rani
Abin da ya sa Jamus ke karbar ’yan ci-rani

A karshen makon jiya ne kasar Jamus ta karbi dubban ’yan gudun hijira, wadanda galibinsu Musulmi ne wadanda suka fito daga kasashen Siriya da kuma Iraki.
kasar ta yi maraba da masu neman mafakan  ne bayan wasu kasashen nahiyar sun rufe iyakokinsu don hana su shiga cikin kasashensu.
Kodayake, a shekaranjiya Laraba ne gwamnatin kasar ta sanar da wasu jerin matakai na taimaka wa kasar yin dawainiyarsu. Matakan sun hada da samar da karin kudi kimanin Dala biliyan uku domin taimakawa jihohi da kuma gundumomi.
Sauran matakan sun hada da saukaka hanyoyin samun izinin mafaka ga ‘yan gudun hijiran, da samar musu matsugunnai da kuma samar da kudin dawainiya da sabbin ‘yan hijirar da za su shiga kasar.
Gwamnatin ta sanar da matakan ne bayan wata ganawa ta sa’o’i biyar tsakanin Shugabar Gwamnatin kasar Angela Merkel da kuma wasu shugabannin kasashen nahiyar Turai masu ra’ayi irin nata.
Akalla ‘yan gudun hijira dubu 18 ne aka yi kiyasin sun shiga kasar a ranakun karshen mako jiya bayan wata yarjejeniya da aka cimma da kasashen Austria da Hungary game da sassauta ka’idojin neman izinin mafaka.
Masana dai suna ganin cewa babban dalilin da ya  tilasta wa gwamnatin kasar karbar masu neman mafakar, wadanda galibinsu Musulmi shi ne yadda yawan al’ummar kasar yake kara raguwa cikin sauri.Yawan tsofaffi a kasar ya fi yawan matasan da ke kasar. Wannan ya sa kasar take bukatar matasa majiya karfi don bunkasa tattalin arzikinta.
Har ila yau, a bangare guda kuma kasar Birtaniya ta ki amincewa ta ba su mafaka ne saboda yadda al’ummarta ke kara karuwa cikin hanzari.