Abin da ya sa Jonathan ya kori Ministan Matasa

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaba Goodluck Jonathan ya kori Ministan Bunkasa Harkokin Matasa Malam Inuwa Abdulkadir. Wata gajeriyar sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim, dauke da sanya hannun kakakinsa Sam Nwaobasi, ta ce Shugaba Jonathan “Ya sallami Lauya Inuwa Abdulkadir daga mukaminsa na Ministan Bunkasa Harkokin Matasa ne daga […]

Abin da ya sa Jonathan ya kori Ministan Matasa

Alhaji Inuwa Abdulkadir tsohon Ministan Bunkasa Harkokin MatasaA ranar Litinin da ta gabata ce Shugaba Goodluck Jonathan ya kori Ministan Bunkasa Harkokin Matasa Malam Inuwa Abdulkadir. Wata gajeriyar sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim, dauke da sanya hannun kakakinsa Sam Nwaobasi, ta ce Shugaba Jonathan “Ya sallami Lauya Inuwa Abdulkadir daga mukaminsa na Ministan Bunkasa Harkokin Matasa ne daga ranar 26 ga Agusta, 2013.”
 Sanarwar ta ce Jonathan ya nuna “godiya ga tsohon ministan kan lokacin da ya kashe wajen bauta wa kasar nan” kuma ya yi masa fatan alheri kan abin da zai sanya a gaba. Sai ta bukaci Abdulkadir ya mika ragamar harkokin ma’aikatar ga Babban Sakataren Ma’aikatar.
Aminiya ta gano sauke Abdulkadir ya zo masa a ba-zata, domin sanarwar sallamarsa ta zo ne a lokacin da yake halartar taron shekara-shekara na kungiyar Lauyoyi ta kasa karo na 53 a Kalaba Jihar Kuros Riba.
Wakilinmu ya ruwaito cewa Abdulkadir ne ya jagoranci daya daga cikin zaman taron a ranar Litinin din kafin ya bar wurin lokacin da ga alama ya samu labarin sallamarsa.
Jim kadan da bude taron ya gabatar da batutuwan da za a tattauna, sannan ya gayyaci toshon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya gabatar da wata takarda mai taken: “Giwa a shekara 100.” Daga baya ya gayyaci Gwamnan Jihar Kuros Riba Liyel Imoke don karin haske kan takardar.
Wasu majiyoyi sun ce mai yiwuwa takaddamar siyasa a tsakanin Shugaba Jonathan da Gwamna Aliyu Wamakko na Jihar Sakkwato inda Abdulkadir ya fito ne ta ci ministan.
Wamakko yana cikin gwamnonin da suke goyon bayan Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi a rikicin siyasarsa da Shugaba Jonathan da shugabannin PDP bisa jagorancin Bamanga Tukur.
Wata majiya ta ce fadar Shugaban kasa ta sa rai Abdulkadir ya rika fada da Wamakko a madadinta kamar yadda takwaransa Minista a Ma’aikatar Ilimi Nyesom Wike ke yi da na Ribas. Amma sai Abdulkadir, wanda kwararren lauya ne kuma tsohon kwamishinan shari’a a jiharsa ya zabi kauce wa wannan rigima.
Shi ne minista na biyu daga jihar da ya bar gwamnatin Jonathan a bayan Alhaji Yusuf Suleiman ya sauka daga Ministan Wasanni don takarar Gwamna a bara.