Abin da ya sa kabilar Ibo suke boren raba kasa – Sanata Hanga
Sanata Ruda’i Sani Hanga, Shi ne Shugaban Jam’iyyar CPC na darko kuma ditaccen dan siyasa a Najeriya, wanda ya taba zama sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa. A wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya, Sanata Hanga, ya bayyana boren neman kasar Biyadara da Ibo ke yi shakiyanci ne kawai da shagwaba. […]

Sanata Ruda’i Sani Hanga, Shi ne Shugaban Jam’iyyar CPC na darko kuma ditaccen dan siyasa a Najeriya, wanda ya taba zama sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa. A wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya, Sanata Hanga, ya bayyana boren neman kasar Biyadara da Ibo ke yi shakiyanci ne kawai da shagwaba. Sannan ya tabo batutuwan da suka shadi sake dasalin kasa, yawaitar jam’iyyu da kuma takarar matasa a dagen siyasar Najeriya. Ga yadda zantawar ta kasance kamar haka:
Aminiya: Ranka ya dade mu dara duba batun boren raba kasar nan da al’ummar Ibo suke yi bayan shekaru 50 da Ojukwu ya taka rawarsa. A matsayinka na gogaggen dan siyasa kuma mai dashin baki kan al’amuran yau da kullum, me ka ke ganin ya sake dawo da wannan bore kuma wace hanya za a bi wajen magance ta?
To ni a ganina za a kalli wannan abu ta bangarori guda biyu, yawanci ana bore ace ana so a rabu idan ba a gamsu da irin zaman da ake yi ba. Idan mutane ba sa jin dadin zaman kuma ba sa darin ciki da abinda yake daruwa. Ko kuma suna cikin wani halin kunci wanda sauran bangarorin kasar ba sa ciki. Amma su a halin da nake gani yanzu ba su kan wannan dalilin sam, saboda dukkan halin da ake ciki a Najeriya zan iya cewa gara ma su da wasu! Ka ga kenan ba matsuwa ba ce ko tashin hankali ko rashin jin dadi. Sai nake ganin shakiyanci ne kawai da shagwaba da kuma ganin cewa wasu sun tsaga sun ga jini. Kamar yadda ‘yan Kudu maso Kadu suka zo suka yi ta barazana cewa sai an ba su kason su na mallakar dukiyar kasa tun da su ke da mai, da aka tsorata aka yi rashin tunani da rashin hange da rashin kishi aka zo aka sa hannu aka ba su kashi 13 bisa 100 na abinda ake samu.
To ganin wannan su ma suka taso da wannan barazanar. Amma ga dukkan mai hankalinsu ya san cewa wannan shirme ne rashin hankali ne rashin hange ne. Domin idan aka rabun su za su di kowa shan wahala da tashin hankali! Mu a nan Arewa ba ruwanmu. Na darko dai idan ka dubi wannan yanki na Kudu maso Gabas da kyau, babu abinda za su iya dogara da shi, inda ke da arzikin mai yankin Kudu maso Kudu ne, su kuma ba zasu yarda a bangare a tadi tare da su ba. Idan kuma haka ta daru to za a maimaita irin rikicin Kudancin Sudan ne. Don haka ni ina ganin wannan shagwaba ce da latsi kawai, saboda sun raina gwamnatin, sun raina mutane. Amma ba ni ban ga wani dalili da ya wuce wannan ba.
Aminiya: Akwai wata shakka ce da gwamnatin ke yi game da su kenan musamman ganin yadda kotu ta saki jagoran nasu bisa wasu sharuda amma ya yi datali da su kuma babu wani mataki da aka dauka kan hakan?
Babu wata shakka da nake ganin gwamnati ta na yi, illa dai kawai ka san kowa yana da lokacinsa na yin wani abu, sannan kuma kowa da irin yanayinsa da yanayin yadda yake yin abubuwansa. Amma ni a ganina shi kadai bai isa ya yi wa gwamnati barazana ba, saboda duk yawancin manyan jiga-jigan yankin sun barranata daga gare shi suna dadin ba ruwansu da shi. Kuma kamar yadda mu muka yi ittidaki akai shi ne ma su sa shi yin wannan bore suna can kasashen waje, ko kuma wasu kasashen ne da ba su so a zauna ladiya suke tunkudo shi don idan aka samu matsala a kasar su shiga su yi rabo, wannan kawai shi ne, amma babu wata barazana da gwamnati ke shakka daga gare shi.
Aminiya: Kiraye-kirayen sake dasalin kundin tsarin mulki ya dauki sabon salo, inda mutane rin su Janar Babangida da Atiku Abubakar suka shiga sahu. Shin ya ya kalli wannan dambarwa?
Wato ina ganin matsalar Najeriya ba tsarin mulki ba ce, mu ’yan Najariya mu ne matsalar kasar nan! Duk ma abinda ka tsara din sai an zo an ma shi hawar kawara, saboda kowa ta kansa yake, kuma duk yadda zaka sa ko su waye ma a gaba, zaka zo ka ji kunya ne kawai. Domin abubuwan ga su nan sun sha daruwa muna gani, saboda kawo yanzu duk wadannan kiraye-kirayen da ake yi kowa yana dadar ra’ayinsa ne kawai, har yanzu babu wanda ya zo da kwakkwaran dalili na sake dasalin. Kowa na dassara ne daidai da son ransa, wani so yake a sake tsari a kara musu jiha, wani a sake tsari a kara musu kudi, wani so yake a sake tsari a ba su shugabanci, kowa da son zuciyarsa, babu wanda ya zo da abu guda daya tak wanda ya shadi kowa da kowa. Sai dai kawai akwai bukatar tantancewa, domin kamar Babangida ko Atiku ba zasu yi kira da ka ba, akwai dai inda aka samu matsala, don haka dole sai an ji kai tsaye daga gare su, ta yadda suke son a sake dasalin tukun. Domin ko ni ka nemi shawarata zan ce ka raba kasar nan gida biyar kowa ya kama gabansa.
Aminiya: Ta ina da ina kenan?
Ka ga dai yankin Kudu maso Yamma na Yarbawa ya kama gabansa, duk da dai cewa arziki ne jibge a yankin musamman Jihar Legas kawai wanda ya dauki kaso daya cikin hudu na arzikin Adirka baki daya, sannan ga Jihohin Ogun da Oyo wadanda kusan dukkan kamdanonin kasar nan acan suke, saboda ko ka hada Arewa da wannan yankin ba dorewa zai yi ba, kowa da tsarinsa da al’adarsa da kuma manudarsa, sai dai su je ruwa ya sha mun yarda! Illa dai kawai tunda ayi wani tsari tunda Legas da dukiyar kowa aka gina, sai ayi wata ka’ida da za a rika baiwa kowane bangare kasonsa a shekara ko a sanya wakilai da za sus a ido, idan an raba su aika da kason su gida. Sai yankin Kudu maso Kudu ya tadi da mansa ba ruwanmu, su kuma Ibo su je can su san yadda za su yi da kwakwar manjar dake wurin, sannan mu Arewa mu haki ma’adinanmu da man detir ga kuma kasar noma wacce ta ishe mu noma dukkan bukatunmu har mu dita da ragowa kasashen ketare. Sai mu rude kododinmu ba shiga ba dita, mu yi irinta Chana, tare da yawansu amma suka ga yunwu na son kashe su, har ta kai mutum na cin naman dan’uwansa don yunwa, sai su kaka rude kododinsu, su ka himmatu har sai da suka mallaki komai, an wayi gari abincin da Chana ta ke ditarwa ya ninka wanda ta ke ci a gida, sannan ta di kowace kasa ci gaba a duniya. Don haka idan za a rabu gwamma a rabun kawai, saboda mu Arewa muna da komai, ga man ga ma’adinai ga kuma kasar noma, amma mun yi sakaci saboda shagwabar cewa muna da mai, to yanzu ga shi yadda abubuwan suka zama.
Aminiya: Akwai kuma batun yawaitar jam’iyyu a kasar nan, kusan duk bayan wani lokaci sai hukumar zabe ta yi rajistar sabuwar jam’iyya, a yanku haka muna da jam’iyyu 45. Shin wannan ci gaba ne a siyasance ko kuwa?
Gaskiya wannan ba ci gaba ba ne, abinda wannan yake nunawa shi ne mutane ba su gamsu ba, dimokuradiyyar nan suna ce ba da gaske ake ba, saboda ga shi nan kana ganin mutum tamkar waliyyi, amma da ka ba shi dama sai yadda ya ga dama zai yi, ba zai ji ba, ba zai bi doka ba, kawai sai dai zalunci da danniya. Duk wanda ya karbi mulki ba ya son ya motsa, ba ya son a taba shi, zai danne kowa don mulkinsa ya tabbata, sannan kuma shugabannin jam’iyya wani lokacin ba su baiwa wadanda suka cancanta damar tsayawa takara, komai jama’arka komai kwarjininka muddin ba ka da kardi a jam’iyya to ba a baka dama. To wannan yasa kake ganin kullun mutane suke dito da sababbin jam’iyyu saboda an gaza yi mu su adalci. Amma da za a cimma wannan doka ta dan takarar kai da-halinka, muddin ya tabbata a kundin tsarin mulkinmu, to za a rage samun ambaliyyar jam’iyyu a kasar nan. Idan za a yi wannan to za a samu sauki, domin da zarar wadanda suka sanya jam’iyya a aljihunsu sun hana ka takara sai ka je ka tsaya a karan kanka jama’a su zabe ka.
Aminiya: A kwanan nan ne Majalisar Dattawa ta gabatar da wani kuduri wanda zai baiwa matasa damar tsayawa takarar shugabancin kasa da kuma majalisun tarayya. Ya ya ka kalli wannan yunkuri?
Gaskiya wannan doka ta yi ma’ana kwarai, domin ina cikin wadanda muka yarda da cewa ya kamata a baiwa samari damar shiga a dama da su a siyasar kasar nan. Idan ka duba duniya a yau zaka ga tuni wannan sauyi ya dara, manyan kasashe da dama a yau matasa ne ke jagorancinsu. To lallai ya kamata mu ma a Najeriya mu yi wannan, can ma da tsodaddinsu suke da ladiya da dahimta da kardi, ballantana mu nan ladiya ba ta ishe mu ba, kuma kullum idan baka da ladiya basirarka kara daburcewa ta ke! Amma sanya yara a gaba wadanda suke da jini a jika zai yi tasiri. disabilillahi ni na ji dadin wannan abu da aka yi, domin ko kwanakin baya akwai wadanda suka ce in zo in yi takarar gwamnan Jihar Kano, na ce a’a takarar gwamna yanzu ba tawa ba ce, domin shekaru sun dara ja yanzu,, ba zan nemi gwamna ba amma zan nemi sanata. Amma gwamna kamata ya yi matasa su yi, domin wadannan kujeru na shugaban kasa da gwamna su na da dawainiya da yawa, sannan da wuyan sha’ani ga dattijo, amma matashi ladiya lau zai tadiyar da ayyukan muddin yana samun shawarwari daga dattawansa. Da wannan nake datan majalisun jihohi za su karbi wannan doka da muhimmanci ta yadda za a gaggauta tabbatar da shi domin har yanzu ba ta tabbata tukun.