‘Abin da ya sa kunkuru ya rasa gashi’
Barkanmu da warhaka Manyan gobe, tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne mai taken: ‘Abin da ya sa kunkuru ya rasa gashi’. Labarin ya kunshi yadda kwadayi ke zama mabudin wahala. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi Akwai wani kunkuru mai matukar kwadayi. Rannan sai ya ziyarci […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe, tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne mai taken: ‘Abin da ya sa kunkuru ya rasa gashi’. Labarin ya kunshi yadda kwadayi ke zama mabudin wahala. A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi
Akwai wani kunkuru mai matukar kwadayi. Rannan sai ya ziyarci gidan kadangare. Isar sa ke da wuya sai ya rika jin kamshin abinci tun kafin ya shiga gidan na kadangare.
Ya ria maka sallama amma ya ji shiru. Bai san cewa kadangare ya shiga bandaki don yin wanka ba ne. Sai ya ga tukunya akan wuta. Ya waiga bai ga kowa ba sai ya bude tukunya ya ga fate a ciki. Sai ya debi fate ya zuba akansa sannan ya rufe da hularsa. Yin hakan ke da wuya sai kadangare ya fito. Ya dauke shi da hira mai tsawo. Kunkuru ya shiga cikin mawuyacin hali saboda faten da ya zuba ya rufe da hula yana da zafi kuma yana kona shi.
Da ya ga ba Sarki sai Allah sai ya yi wuf ya tube hular ya shiga kwarma ihu yana neman gafarar kadangare inda ya nuna kwadayi ne ya sa ya yi haka kuma ba zai sake yin haka a nan gaba ba.
Daga nan kadangare ya yafe masa kuma ya ja masa kunne da kada ya sake aikata irin haka ko a wani gida ne ma.
To Manyan gobe, kun ga abin da kwadayi ke janyo wa mutum. Da fatan za a rage yin kwadayi musamman idan an je anguwa.