‘Abin da ya sa kunkuru ya rasa gashin kansa’
Akwai wani kunkuru mai matukar kwadayi. Rannan sai ya ziyarci gidan kadangare, isowarsa ke da wuya sai ya fara jin wani kamshin abinci tun kan ya shiga gidan. Ya rinka masa sallama amma ya ji shiru. Bai san cewa kadangare ya shiga bandaki wanka ba. Sai ya ga tukunya akan wuta. Ya waiga ya ga […]
Akwai wani kunkuru mai matukar kwadayi. Rannan sai ya ziyarci gidan kadangare, isowarsa ke da wuya sai ya fara jin wani kamshin abinci tun kan ya shiga gidan.
Ya rinka masa sallama amma ya ji shiru. Bai san cewa kadangare ya shiga bandaki wanka ba. Sai ya ga tukunya akan wuta. Ya waiga ya ga ba kowa sai ya bude tukuyar ya ga fate a ciki. Sai ya dibi fate ya zuba a kansa sannan ya rufe da hularsa. Yin hakan ke da wuya sai ga kadangare ya fito ya kwashe shi da hira. Ga kuma kunan faten a kansa. A hakan ya cire hular a gaban kadangaren.
Ya shiga ihu yana cewa kadangare ya yafe shi kwadayi ne ya sanya shi shiga wannan halin. kadangare yace da shi ai shi ke da matsalar don gashi yanzu ya dandana kudarsa.
Toh! Manyan gobe, kun ga abinda kwadayi ke janyo wa mutum. Da fatan za’a rage yin kwadayi musamman ma idan anje anguwa.
Taku anti Amina