Abin da ya sa mata za su taka muhimmiyyar rawa a 2019 – Sa’adatu Mahmud
Hajiya Sa’adatu Mahmud gogaggiyar ’yar siyasa ce, kuma ita ce Shugabar Mata ta Jami’yyar APC a Jihar Bauchi ta kuma taba yin takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu. A wannan mako ta zanta da manema labarai inda ta ce takan fadakar da mata da wayar musu da kai gida-gida don su mallaki katin zabe: Me […]
Hajiya Sa’adatu Mahmud gogaggiyar ’yar siyasa ce, kuma ita ce Shugabar Mata ta Jami’yyar APC a Jihar Bauchi ta kuma taba yin takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu. A wannan mako ta zanta da manema labarai inda ta ce takan fadakar da mata da wayar musu da kai gida-gida don su mallaki katin zabe:
Me ya sa kika fara wannan zagaye gida-gida kina bin mata don ki wayar musu da kai a kan katin zabe?
Dalilin da ya sa na fara wannan aiki na bin mutane gida-gida shi ne domin mu fadakar da al’umma musamman mata ’yan uwanmu, ka san wadansu sun yi aure daga wasu garuruwa sun dawo nan Bauchi, wadansu kuma daga wasu unguwanni suka koma wasu, wadansu kuwa yanzu ne suka cika shekara 18 a duniya. Saboda haka ne muka ga ya kamata mu wayar wa matan da ke sauraronmu kai kan su mallaki katin zabe, wanda ma ta mallaka ya zama akwai gyara a jiki za ta iya zuwa a gyara mata, ta wannan hanya ka ga kowa zai iya kare mutuncinsa ya kuma nuna kishin kasarsa ta hanyar zaben shugabanni na kirki.
Ana gani mata da yawa na da sha’awar siyasa a bana amma ba sa iya takara ko me ya sa haka?
Wannan kafin zuwan APC ne, amma tun zuwan APC akwai mata da yawa a mukamai daban-daban tun daga matakin gunduma da karamar hukuma da jiha da tarayya, maimakon da sai shugabar mata da mataimakiyarta kawai. Ka ga a nan Jihar Bauchi a lokacin gwamnatocin baya Kwamishinan Ma’aikatar Mata ma namiji ake nadawa, amma yanzu abin ya sauya mace ce Kwamishinar, kuma don a ba ta damar jawo mata kusa da masu mulki aka sanya Kwamishiniyar aiki tare da matan gwamnoni. Haka akwai Ministar Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhassan ga Ministar Kudi Misis Kemi Adeosun ga Minista a Ma’aikatar Harkokin kasashen Waje Hajiya Hadiza Bukar Abba Ibrahim da sauransu. Wannan gwamnati saboda karfafa wa mata ya sa Ministar Muhalli Hajiya Amina Muhammaed yau ita ce Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya. A nan Bauchi yanzu kwamishinoni uku dukansu mata ne kuma suna kan mukamai masu daraja kamar na lafiya da muhalli da harkokin mata. Sannan dubi irin kokarin da Uwargidan Shugaban kasa take yi na tallafa wa mata da yara da marayu da marasa galihu. A nan irin kokarin hadakan mata, ba Jihar Bauchi kawai ba har ma na Arewacin kasar nan da Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi Shugaban Matan Gwamnonin Arewa, Hajiya Hadiza Abubakar ke yi, dukansu sun yi tsare- tsaren kyautata rayuwar mata da bunkasa tattalin arzikinsu.
Amma wadannan mukamai ai duk alfarma aka yi musu ba takara suka tsaya suka yi ba?
Haka ne amma a baya ba a samu hakan ba ko? Ka ga yanzu tunda sun shigo suna kara ilimi da karatun siyasa. Mata ba gasa muke yi da maza ba, maza iyayenmu ne, su jagororinmu ne. A yanzu a Kudu akwai sanatoci mata da yawa amma a Arewa muna da Sanata Binta Garba Masi ce kawai, a 2019 za ka ga mata da yawa sun yi takara.
Kuma alhamdulillahi da irin damar da suke ba mu na alfarmar muka kai matsayin da muke kai a yau, kuma da haka za su karfafe mu mu ci gaba a zabe mai zuwa. Za ka yi mamakin yawan matan da za su fito takara bana, ko yanzu ka zagaya cikin gari za ka ga hotunan mata suna son tsayawa takara a mukamai daban-daban.
Jamiyyarku ta APC na fama da rikice rikice a kowace jiha, shi wannan baraka ba za ta hana ku nasara a 2019 ba?
Ku ’yan jarida, ai ba bakin siyasa ba ne, wannan duk dambarwar da kake gani na sabanin ra’ayoyin siyasa ne, don kokarin da kowane dan jam’iyya ke yi a samu ci gaba a yankinsa, amma in sha Allahu za ka yi mamakin yadda Jam’iyyar APC za ta dunkule ta kara karfi. Kuma za ta dinke dukan barakar ta tsayar da ’yan takara karbabbu da jama’a ke so. Wannan sabani haka siyasa ta gada kuma ba abin da zai faru sai alheri. Kuma ai an kafa Kwamitin Ngige ya zaga ya duba ya ba da bayani ga kuma kwamitin Bola Tinubu wanda zai yi wa kowa adalci mu daidaita mu kara hada kai mu samu nasara.