Abin da ya sa mitocin lantarki suke karanci – Jamilu Gwamna
Za mu so jin nasarorin da kamfaninku ya samu tun lokacin da kuka kafa shi?Alhamdulillahi mun samu nasarori masu yawa, to amma fa akwai kalubale da yawa da muka fuskanta. Misali lokacin da muka zo, wutar lantarkin da ake ba mu ta yi karanci kwarai da gaske saboda mafi yawan jama’a ba su samun wutar […]
Za mu so jin nasarorin da kamfaninku ya samu tun lokacin da kuka kafa shi?
Alhamdulillahi mun samu nasarori masu yawa, to amma fa akwai kalubale da yawa da muka fuskanta. Misali lokacin da muka zo, wutar lantarkin da ake ba mu ta yi karanci kwarai da gaske saboda mafi yawan jama’a ba su samun wutar da ta wuce ta awa biyu ko uku, ta kai mutuka shi ne a samu awa biyar. Amma a yanzu da yake wutar lantarkin ta samu muna iya raba ta har fiye da awa goma sha biyu. Saboda haka mun gode Allah.
To wadanne kalubale kuke fuskanta?
Akwai kalubale da yawa musamman rashin biyan kudin wutar lantarki daga jama’a da kuma ta mutanen da suke kan layukanmu wadanda ba mu sansu ba, wato wadanda suke shan wutar lantarki ta barauniyar hanya. Saboda haka shi ya sa muka bullo da hanyoyi da dabaru da yawa don yi maganin wadannan matsaloli.
Kwanan nan Hukumar Wutar Lantarki ta kasa (NERC) ta ba da umarnin cewa kada kamfanonin irin naku su bai wa jama’a wutar lantarki ba tare da sun samar musu da mita ba, me za ka iya cewa kan haka?
Ita wannan hukuma ba wai kawai masu rarrabawa take lura da su ba, tana lura da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki. In da a ce akwai isassun mitoci a wurinmu, to da babu shakka za mu ce wannan ba wata matsala ba ce. Mu kanmu za mu so a ce duk wanda za mu bai wa wutar lantarki mun ba shi mita. Saboda yawancin mutane wadanda ba su da mita a gaskiya kintace kawai ake yi na yadda suke shan wutar amma mafi a’ala shi ne a samu mita a bai wa jama’a. Wannan doka babu shakka za ta ba mu kalubale da yawa, amma dai ina mai tabbatar maka cewa mu dama muna da tsarin da muka yi na ganin cewa daga nan zuwa shekara biyar za mu bai wa dukkan abokan huldarmu mita. Kuma wannan shi ne dalilin da ya sa muka sayi wannan kamfani. Kuma da ma tun kafin a yi wannan doka mun dauki alkawarin bai wa jama’a mita. To amma dokar za ta kara mana kaimi, sai dai kuma ka san abu ne wanda ya shafi jari, abu ne wanda ya shafi sanya kudi. Dole za mu zauna mu yi nazari mu ga yadda za mu bullo wa lamarin.
Me kake ganin ya janyo karancin mita a yanzu?
Na gaya maka batun mita abu ne na kudi. Yanzu inda za a ce za bai wa kowa mita ba karamin kudi zai ci ba. Misali yanzu kowace shekara dole mu kashe Naira biliyan hudu idan ake ce sai an ba kowa mita. Mitar nan kashi daya ne daga cikin abubuwa da yawa da muke yi. Akwai batun taransifoma da wayoyin wuta da kuma turakun wutar lantarki, abubuwan suna da yawa da ake amfani da su wajen raba wutar lantarki. Amma saboda mitar ita tafi damun mutane, shi ya sa ake matsawa a kanta. Batun rashin mitar nan shi ne akwai kamfanoni masu samar da mitocin nan, to, amma su kansu ba su da mitocin da za su iya wadatar da jama’a kuma bayan mitocin nan ba kyauta ba ne dole za a saya. kalubalen shi ne kudin da za a samu a sayi mitocin.
Yaya kake ganin sabon farashin wutar lantarki da Hukumar NERC ta bayyana a kwanakin baya?
To za a iya cewa ya fi babu daga inda muka taso zuwa yanzu da kuma inda yanzu muka dosa. Da ma abin da muke ta kokarin yi shi ne mu tabbatar cewa kudin da ake biya ya zama kudi ne da ya dace a biya. A yanzu farashin ya tashi amma da yake abu ne wanda aka sanya shi daga yanzu zuwa shekara goma wannan farashi zai yi amfani. Abu ne wanda zai dauki lokaci sosai kafin a cimma burin da ka sanya gaba. Amma dai sabon farashin zai taimaka.
Kawanakin baya ma’aikatan da akasarin kamfanonin wutar lantarki suka dauka aiki sun yi zanga-zanga kan rashin biyan su albashi na watanni, me za ka iya cewa kan wannan?
Na farko, kafin mu karbi wadannan kamfanoni duk wani ma’aikaci da yake aiki ya kamata a ce Hukumar Sayar da Hannun Jari (BPE), ita ce take da hakkin biyansu ba mu ba. Sannan ma’aikatan da muka samu na wucin-gadi da ma ba ma’aikata ne na dindindin ba. Idan ana bukata a dauke su, idan kuma ba a bukatar su a sallame su. Ni ban ga wata matsala a cikin wannan ba.
Wane buri kuke son ku cimma a jihohin da kuke raba wa wutar lantarki?
Kamar yadda ka sani burinmu shi ne mu tabbatar cewa duk masu shan wutar lantarki mun inganta yadda suke samun wutar ba tare da wata matsala ba. Sannan ina kira ga jama’a cewa duk wanda ya sha wutar lantarki hakki ne a kansa ya biya kudin wutar, kuma mutane su taimaka mana su rika sanar da mu duk wanda yake shan wutar ba bisa ka’ida ba. Saboda idan ka bar mutum ya sha wutar lantarki kuma ka san ta sata ce, amma ba ka fada ba to babu shakka kai ne kake biya masa kudin wutar da yake sha ta barauniyar hanya.