Abin da ya sa muka ƙara farashin man fetur — Tinubu

Idan ba mu ɗauki waɗannan matakan ba, ta yaya kuke tsammanin za mu samu ci gaba a Nijeriya?

Abin da ya sa muka ƙara farashin man fetur — Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya magantu kan dalilin da gwamnatinsa ta ƙara farashin man fetur da ake ta faman cece-kuce a kai a ƙasar.

A sabbin tsare-tsaren da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya NNPCL ya bijiro da su a kwanakin nan har da ƙara farashin litar man fetur zuwa kusan Naira 897.

Wannan lamari ya sanya dillalai masu zaman kansu suka ɗaga farashin man fetur ɗin zuwa tsakanin N930 da N1200 duk lita ɗaya.

Alƙaluma sun tabbatar da cewa tun bayan cire tallafin man fetur ɗin da Shugaba Tinubu ya yi a watan Mayun 2023, farashinsa ya ci gaba ninkuwa kusan sau uku.

Sai dai da yake kare wannan mataki yayin ganawa da ’yan Nijeriya mazauna ƙasar Sin a birnin Beijing, Shugaba Tinubu ya ce ƙara farashin man fetur ɗin mataki ne mai tsauri da babu makawa sai ya ɗauka domin ci gaban ƙasar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a, ta ambato Shugaban yana cewa ƙara farashin man fetur da sauran sauye-sauye da gwamnatinsa ke aiwatarwa na daga cikin tsare-tsaren da za su farfaɗo da kuma ɗora ƙasar a kan turba ta bunkasar tattalin arziki.

Shugaban ya ɗiga ayar tambaya kan ko Najeriya za ta iya cimma gaci kuwa a fannin ci gaba kamar China muddin ba a ɗauki tsauraran matakai ba?.

Ya ba da misali da kayayyakin more rayuwa da China ke da su da suka haɗa da kyawawan hanyoyi da wadatacciyar wutar lantarki mara yankewa da tsaftataccen ruwan sha da makarantu masu inganci.

“A halin yanzu ana gudanar da sauye-sauye a Nijeriya a dalilin matakan da muka ɗauka duk da cewa suna da tsauri.

“Na san a kwanakin nan kun ji ana ta magana cewa an samu ƙarin farashin man fetur a gida Nijeriya.

“Idan ba mu ɗauki waɗannan matakan ba, ta yaya kuke tsammanin za mu samu ingatattun hanyoyin sufuri kamar yadda kuke da su a nan [China]?

“A nan kuna da wadatacciyar wutar lantarki kuma matabbaciya. Kuna samun tsaftataccen ruwan sha da ke gudana a kodayaushe. Ga nagartattun makarantu.”

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, burinsu a matsayinsu na shugabannin Najeriya, shi ne su gadar wa yaran da ke tasowa a ƙasar yanayi mafi kyawu da za su yi tinkaho da shi.

Shugaban ƙasar ya ce ba a samun kowane irin ci gaba cikin sauƙi ko kuma a ɓagas.

“Idan kana son ka samu komai a kyauta, to zai zame maka mai wahalar samu ko ka jima ba ka same shi ba.

“Dole idan har muna son ’ya’yanmu su samu kyakkyawar makoma sai mun yi sadaukarwa,” inji Tinubu.