Abin da ya sa muka bude gidan talabijin na Afirka Tb – Dokta Huzaifa
Babban Daraktan Gidan Talabijin na Africa Tb da ke kasar Sudan, Dokta Huzaifa Abdulkareem ya ce sun bude gidan talabijin din ne saboda kishin addinin Musulunci. Dokta Huzaifa ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya […]
Babban Daraktan Gidan Talabijin na Africa Tb da ke kasar Sudan, Dokta Huzaifa Abdulkareem ya ce sun bude gidan talabijin din ne saboda kishin addinin Musulunci. Dokta Huzaifa ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ziyara a gidansa da ke garin Jos.
Ya ce dukkan wadanda suka kafa gidan talabijin din babu mai jin harshen Hausa, amma ganin yadda miliyoyin mutane suke amfani da harshen, ya sanya gidan talabijin din yake watsa shirye shiryensa da harshen Hausa. Ya ce miliyoyin jama’a suna amfana da abubuwan da ake watsawa a gidan talabijin din.
Dokta Huzaifa ya ce sun kai wa Sheikh Sani Yahya Jingir ziyara ce, domin su mika godiyarsu kan irin gudunmawar da ya bai wa gidan talabijin din, ta hanyar wa’azuzzukan da yake gabatarwa a
gidan talabijin din.
“Babu shakka shigowar da Sheikh Sani Yahya ya yi a gidan talabijin din ya kara karfafa mana gwiwa. Muna fatar Malam
zai tsaya wajen ganin an tallafawa gidan talabijin din ta kowane bangare.”
A jawabin Sheikh Sani Yahya Jingir ya yaba wa gidan talabijin na Africa Tb, kan irin shirye-shiryen da yake watsawa.
Ya ce, “A gaskiya wannan gidan talabijin yana faranta mana rai kwarai da gaske, musamman ganin yadda kuke tsare Sunnah da kyawawan dabi’u da al’adun Musulunci, a shirye-shiryen da kuke watsawa.”
Ya yi kira ga gidan talabijin din kan su yi amfani da shi wajen wayar da kan al’umma kan tausayi da iya zaman tare na addinin Musulunci.